logo

HAUSA

Likitocin kasar Sin suna taimakawa Saliyo don gano ko akwai wani nau’in COVID-19

2021-01-12 20:33:25 CRI

Mai magana da yawun cibiyar kai daukin gaggawa kan COVID-19 ta kasar Saliyo (NaCOVERC), Solomon Jamiru ya bayyana cewa, yanzu haka wata tawagar ma’aikatan lafiya daga kasar Sin yana kasar, inda suke aiki da cibiyar, don gano ko akwai wani nau’i na COVID-19 a kasar.

A cewarsa, tawagar ma’aikatan lafiyar ta kasar Sin, tana taimaka musu, musamman a sassan da suka hada da warkar da marasa lafiya, da binciken lafiya, da sauran fannonin aikin kiwon lafiya dake da nasaba da yaki da annobar.

Jamiru ya kara da cewa, “muna aiki ba dare ba rana da tawagar, wajen gudanar da cikakken bincike kan mutanen da ake zargin suna dauke da nau’in cutar. Sai dai har zuwa yanzu, ba mu kai ga gano wani da yake dauke da nau’in cutar ba.(Ibrahim)