logo

HAUSA

Zhao Xinzhu: Basiniya 'yar kasuwa da ta yi kokarin samun tambari da suna mai kyau bisa kirkire-kirkire, kulawa da kauna

2021-01-11 15:39:12 CRI

Zhao Xinzhu: Basiniya 'yar kasuwa da ta yi kokarin samun tambari da suna mai kyau bisa kirkire-kirkire, kulawa da kauna_fororder_1

An karrama Zhao Xinzhu, ‘yar kasuwa daga Shenzhen, wani birni dake lardin Guangdong na kudancin kasar Sin a matsayin ‘yar kasuwa mai basira kuma abar koyi, yayin bukukuwan cikar yankin musammam na raya tattalin arziki na Shenzhen shekaru 40 da kafuwa. Ta ce, “ ta hanyar kara bada gudunmuwa ga wannan birni ne za ta iya saka masa da kuma gano darajar rayuwarta a wannan muhimmin zamani!”

Zhao Xinzhu tana rike da imani a shekarar 1989. Kamar galibin matasa na wancan lokaci, ta barin garinsu dake arewa maso gabashin Sin zuwa Shenzhen, mafarin manufar bude kofa da gyare-gyare a gida ta kasar Sin ba tare da komai ba. “hango lokacin, lallai ina da karfin hali”, cewar Zhao.

Bayan kasancewarsa yankin musammam na raya tattalin arziki na farko a kasar Sin shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya sauya zuwa birnin irin na zamani, inda yake da al’umma sama da miliyan 13, ana masa lakabi mai “al’ajabi”.

Birnin shi ne mafi dacewa ga Zhao ta cika burinta. Ta fara da dinka tufafi, kuma ta yi nasarar raya sana’arta ta hanyar ci gaba da koyon dabaru a fannin.

Zartar da sabbin manufofi a shekarar 2001, ta haifar da bunkasar kasuwar samar da gidaje ta kasar Sin. “Akwai bukatar samar da dakin girki mai kyau da tsari ga wadanda ba su da shi. Idan za a cimma wannan, za a iya samun sabuwar sana’a a kasar Sin”, cewar Zhao.

A shekarar 2001, Zhao ta jagoranci wata tawaga shiga kasuwancin tsarawa da samar da kantar dakin girki. Ta sauya sunan kamfaninta zuwa “Zhongyi” wanda ke bayyana sha’awarta na ba kwastomomi muhimmanci da kuma kudurinta na samar da kayayyakin da mutane za su so.

A lokacin da ta kafa kamfanin Zhongyi, tana da karamin ofis mai fadin murabba’in mita 47 da masana’anta mai murabba’in mita 500 kawai. Abun da ya kwantar mata da hankali shi ne, sauyawar tunanin Sinawa game da dakin girki ya zo daidai da habakar sana’ar, da kuma abun da ta yi tsammani.

Cikin shekaru 20 da suka biyo baya, kamfanin ya habaka zuwa na zamani, sannan ya hada bincike da dabarun samun ci gaba cikin ayyukan samar da kayayyaki da na cinikayya. Kamfanin mai hedkwata a yankin Qianhai na Shenzhen, ya kulla kyakkyawar dangantakar kasuwanci da masu samar da gidaje da kuma kayayyaki daga ciki da wajen kasar.

Zhao ta hango damar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta kasar Sin ta samar, inda ta kafa cibiyar baje kolin kayayyakin gida na zamani a Nanning, babban birnin jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai. Ta kuma bude rassa a yankin HongKong da biranen Beijing da Shanghai da Chongqing da kuma lardunan Guangdong da Hubei.

Zhao Xinzhu: Basiniya 'yar kasuwa da ta yi kokarin samun tambari da suna mai kyau bisa kirkire-kirkire, kulawa da kauna_fororder_2

Kamfaninta ya samar da wani tsarin samar da kayayyakin gida na zamani mai zaman kansa, wanda aka yi wa lakabi “Intelligently Manufactured in China” wato wanda aka samar a kasar Sin bisa fasahar zamani, maimakon “Made in China” wato wanda aka samar a kasar Sin kadai.

Da ta waiwayi yadda harkokin kasuwancinta suka gudana, Zhao ba ta yi nadamar jajircewa. Ta ce, “fara harka a bangaren da ba ka da ilminsa, na bukatar kwarin gwiwa da tsayawa tsayin daka da kuma amincewa gazawa ko asara. Na kan ce ba zan yi kasa a gwiwa ba, zan jajirce”.

Falsafar Zhongyi ita ce “rayuwa bisa inganci, ci gaba bisa nagarta” cewar Zhao, “alfahari da ingancin kayayyakin ne ke sa ni kara bin hanyar kirkirar sabbin abubuwa”.

A lokacin da aka shiga matsalar kudi a shekarar 2008, kamfanoni da dama sun zaku su rayu, amma sai suka kauce hanya. Zhao ta nace kan tabbatar da ingancin kayayyaki da kuma ingiza ci gaban tattalin arzikin kamfanin ta hanyar hadin gwiwa da yankunan raya masana’antu. 

Ta mayar da hankali ne kan sauyawar harkokin masana’antu da kirkire-kirkiren fasaha da samun ci gaba, sannan ta kan nazarci matsaloli ta lalubo mafita mafi dacewa, lamarin da ya saukakawa shawo kan matsaloli da amfani da sabbin damarmaki.

Zhao ta yi ammana cewa, ci gaba da kirkirar sabbin abubuwa shi ne zai kawo ci gaban kamfani. Ta kara da cewa, “zuwa yanzu, muna da sama da ‘yancin mallakar fasaha 100. A nan gaba, za mu yi kokarin kirkire-kirkiren a fanni fasaha.”

A zamanin amfani da sabbin fasahohin, bangaren samar da kayayyakin gida da ake amfani da shi ya fara fuskantar kalubale. A shekarar 2015, kamfanin Zhongyi ya fara hada hannu da jami’o’i da kamfanonin fasahohin zamani domin samar da tsarin samar da kayayyakin gida na zamani ta hanyar amfani da tsarin Cloud da intanet na wayar salula da sauran fasahohi. Wannan tsarin zai taimakawa masu amfani da shi samun kayayyaki cikin sauki.

A yankin masana’antun kamfanin masu amfani da fasahohin zamani, ana iya samar da kayayyaki kai tsaye da na’urori, lamarin da ke rage kurakuran da bil adama ke tafkawa.

Zhongyi ya samu tambari da suna mai kyau duk da takara mai tsanani da yake fuskanta a kasuwa. An karrama shi a matsayin “Tambarin kasuwanci mafi fice a Guangdong” da kuma “Tambari mafi fice a Shenzhen”.

Zhao na da yakinin cewa, kamfanin zai ci gaba da samun nasara. “Kirkire- kirkire shi ne tubalin kamfanin, kuma jajircewa shi ne ginshikin tamburan kasa. wannan na nufin, mun yi imanin Zhongyi zai zama katafaren tambari a kasar Sin,” cewar Zhao.

“Sanya mutane farin ciki abu ne mai muhimmanci, ko da kuwa kana fafutukar cimma burinka,” cewar Zhao. Fitacciyar ‘yar kasuwar ta taka rawa da dama a harkokin da suka shafi al’umma, ta kasance mai sauke nauyin dake wuyanta na taimakawa al’umma.

Mata na taka rawa sosai a fannin raya al’umma, cewar Zhao. Ta kara da cewa, yara su ne manyan gobe. A cewarta, “ni mace ce, don haka na shirya mayar da hankali kan taimakawa mata da yara, muddin ana bukatata. Har yanzu akwai aiki mai yawa a gabanmu ta fuskar taimakawa mata da yara masu rauni shawo kan wahalhalunsu.”

Yayin da annobar COVID-19 ta fara yaduwa a lokacin bikin bazara a bara, daukacin al’ummar kasar ne suka hadu domin yaki da ita. Zhao ta jagoranci shugabannin kamfanoni wajen kafa wata tawagar aikin kandagarki da dakile cutar

Zhao Xinzhu: Basiniya 'yar kasuwa da ta yi kokarin samun tambari da suna mai kyau bisa kirkire-kirkire, kulawa da kauna_fororder_3

A ranar 29 ga watan Janairun bara, kamfaninta ya bada gudunmuwar kudi ga kungiyar agaji ta Red Cross ta lardin Guandong domin taimakawa ayyukan kandagarki da dakile cutar. Ya kuma bada gudunmuwa ga kungiyar mata ta Guangdong domin tallafawa iyalan jami’an lafiya na lardin, wadanda suka gaggauta tafiya lardin Hubei, da ya fi fama da cutar, domin bada taimako.

Har ila yau, kamfanin Zhongyi ya bada gudunmuwar marufin baki da hanci ga Jixi, wani birni a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Ya kuma bada sinadaran kashe kwayoyin cuta ga asusun kula da mata da yara na Shenzhen, a lokacin da kayayyakin yaki da annobar suka yi karanci a kasar Sin. Ban da haka, Zhao ta jagoranci komawa bakin aiki da fara samar da kayayyaki.

Zhao ta yi imanin cewa, ya kamata ‘yan kasuwa su rika yin kyawawan ayyuka. “JKS da gwamnatin kasar ne suka rene mu, ya kamata mu saka musu ta hanyar taimakawa al’umma.”

“Baya ga haka, zan ji dadi idan na sanya mutane farin ciki. A bara, yaran da suka ci gajiyar shirin lafiya na Liangshan, na asusun China Red Ribbon, sun zo Shenzhen. Ban yi zaton galibinsu za su tuna ni ba. Amma sun aiko min da wasu rubutattun kalaman da suka taba min zuciya.”

A matsayin babbar jami’ar kungiyar mata ta kasar Sin, kuma shugabar cibiyar cinikayya ta mata ta kungiyar raya masana’antu da cinikayya ta kasar, Zhao na karfafawa mata ‘yan kasuwa gwiwar zage damtse da kuma kula da ma’aikatansu domin kara karfi da hadin kai a kamfanoninsu.

Ta kara da cewa, ya zama wajibi a yi amfani da fifikon da mata ke da shi a cikin iyali, domin samun yara da dabi’u na kwarai.

“A matsayin mambar kungiyar mata ta kasar Sin, dole ne kungiyarmu ta zama gadar da ta hada gwamnati da dukkan mata, kuma dole ne mu so ayyukanmu, mu kuma yi aiki tukuru domin kyautata duniya a sabon zamani”, cewar Zhao.

Kande