logo

HAUSA

Gasar Olympic ta ci karo da babban sauyi na rashin tabbas irin sa na farko a tarihi

2021-01-07 12:49:09 CRI

A ranar 24 ga watan Maris na shekara 2020 da ta shude ne, gasar Olympic ta zamanin yau da aka shafe shekaru 124 ana gudanarwa, ta fuskanci wani irin sauyi irin sa na farko a tarihin ta.

Domin kuwa a wannan rana ne, kwamitin kasa da kasa mai shirya gasar ko IOC, da kuma mashiryan gasar na birnin Tokyo, suka amince su dage lokacin gudanar da gasar da aka tsara birnin na Tokyo zai karbi bakuncin ta da shekara guda, saboda bullar cutar numfashi ta COVID-19, wadda kawo yanzu ke ci gaba da addabar sassan duniya. A karon farko, ba a samu zarafin gudanar da gasar ba, sakamakon dalilin da ba na yaki ba.

Cikin wata wasika da shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya rubuta a karshen watan Afirilun barar, wanda ya yiwa lakabi da "Yanayin Olympic da cutar COVID-19", ya ce yayin da duniya ke fama da wannan cuta ta COVID-19, dukkanin mu mun shiga wani hali na rashin tabbas. A wannan gaba a tarihi, ba alamun rashin tabbas din nan zai sassauta. A yanzu ne muka fara gane mummunan tasirin da wannan annoba ke haddasawa a duniya.

Mr. Bach ya ce, babbar kalma a nan ita ce "Rashin tabbas." Idan muka waiwayi wannan shekara mai cike da rudani, yanayin "Rashin tabbas" da annobar nan ta haifar a fannin kiwon lafiya, ya kasance daya daga manyan kalubale ga harkar wasannin Olympic, da ma harkar wasanni a matakin kasa da kasa, wanda kuma za a jima ana fama da shi a nan gaba.

Yanayi mai wuyar hasashe game da wannan annoba

Cutar COVID-19 ta sauya daukacin sassan zamantakewar al’umma da aka saba da su, ciki har da fannin wasanni. Yanzu haka a lokuta da dama, ragamar harkokin wasanni ba ta hannun masu ruwa da tsakinta, maimakon hakan ta na hannun masu lura da tsaftar muhalli ne.

Al’amaru kamar dage gasar “French Open” a watan Satumbar da ya shude, da batun dage adadin ‘yan kallo a kullum, daga mutane 20,000 da aka tsara tun da fari, zuwa mutane 11,500, daga nan kuma zuwa mutane 5,000, kai har ma zuwa mutane 1,000, kwanaki 3 gabanin gudanar da raba rukunin gasar, daidai da matakan gwamnati na dakile yaduwar wannan cuta ta COVID-19, sun isa kyakkyawan misali na hakan.

A matsayin sa na shugaban hukumar shirya gasar Olympic ta duniya, tambayar da aka sha yiwa Mr Bach ita ce, mece ce makomar gasar Olympic ta birnin Tokyo ? shin za a gudanar da ita kuwa? Idan za ta gudana, yaya za a tsara ta?

Game da bangaren tambayar na farko, akwai amsa: "Eh", amma bangare na biyu, ba bu tabbas game da yadda al’amura za su wakana, har yanzu ba bu cikakkun bayanai game da yanayin da cutar za ta kasance cikin watanni masu zuwa.

Yuhei Inoue dan asalin kasar Japan, malami ne a jami’ar “Manchester Metropolitan”, yana kuma kallon gasar ta birnin Tokyo ta fannin tasirin ta ga kasar Japan, da ma duniya baki daya; musamman don gane da alakar ta da cutar COVID-19.

Ya ce "Idan har aka kai ga cimma nasarar gudanar da wannan gasa lami lafiya, cikin tsari mai nagarta, duk kuwa da kalubalen da cutar a haifar, hakan zai shaidawa duniya ikon da Japan, da shi kan sa birnin Tokyo ke da shi, na kasancewa kasa, da birni masu karfin gaske, kuma hakan zai daga martabar su a idanun sauran sassan duniya.

Masanin ya ce "Nasarar farfadowa daga wannan annoba, ya wuce batun manufofin tattalin arziki, kamar shigar da karin kudade na zaburar da fannin. Mr. Yuhei ya ce, karsashi da alamar gasar Olympic, za su kasance wani jigo da zai taimakawa mutane, da al’ummu, ta yadda za su iya samun zarafin yin aiki tare, wajen cimma buri daya, na farfadowa daga wannan annoba, kuma tabbatar hakan zai kara sanya al’ummun duniya kara gamsuwa da tasirin da wasanni gasar Olympic ke da su, a tsakanin al’ummar duniya,".

Lokaci mai wahala ga kowa

Ga mutane irin su Mr. Alfons Hormann, shugaban hukumar harkokin wasanni ta kasar Jamus ko DOSB a takaice, aiki mafi girma da yake fama da shi, tun daga watan Maris na shekarar bara, shi ne nemo tallafin gwamnati, duba da yadda wasu rahotanni daga hukumar ta DOSB suka nuna cewa, burin Jamus na karbar bakuncin gasar Olympic na iya gamuwa da cikas, da ma hasarar da za ta iya kaiwa har euro biliyan daya.

Haka kuma wannan lamari yake a sassan duniya daban daban. Tun daga hukumomin shirya wasanni na kasa da kasa ko “Ifs”, zuwa kwamitocin shirya gasar Olympic a matakin kasashe ko “NOCs”, zuwa ga daidaikun mutane, kowa yana fama da matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu.

Ga mafi yawan hukumomin shirya wasanni na kasa da kasa, cutar COVID-19 ta riga ta haddasa musu dunbin hasara ta dukiya, tun daga batun kudin shiga da suke samu daga shiga kallon wasanni, zuwa masu daukar nauyin harkar wasanni da ake baiwa lasisin nuna tallace tallace a talabijin, da dai sauran su, dukkanin su sun tafka asara.

Dage lokacin gudanar da gasar birnin Tokyo ta 2020, kusan yana nufin da yawa daga hukumomin shirya wasanni na kasa da kasa, ba za su samu kudaden shiga na Olympic daga hukumar IOC ba, sabanin yadda abun yake a da, wanda hakan ya dada ta’azzara yanayin da suke ciki.

Kan dai wannan batu, wani sakon Tiwita daga shafin kungiyar wasan Rugby sevens ta Ingila ta ce, "Yanzu lokaci ne mai wahalar sha’ani. A lokacin bazarar bara, lokacin da kungiyoyin mu na maza da mata suka samu gurbin buga gasar Olympic ta birnin Tokyo muna cikin farin ciki. Amma a watan da ya gabata, an katse kwangilar da muka kulla saboda karancin kudade, wanda hakan ke nuni ga kawo karshen shirin mu na Ingila “7s” da muka sani a baya.

Karancin kudade, da kuma matakan kulle a wasu kasashen duniya da yankuna, ya sanya ‘yan wasa da dama ba sa iya samun damar yin horo yadda ya kamata.

Ka canza ko a canza ka: Sauyin gaggawa na IOC

Yanayin da ake ciki a halin yanzu, na nufin dole ne IOC ta taka rawar gani a fannin shugabanci game da batun gudanar gasar Olympic, kuma wannan aiki ne da ya rataya a wuyan Mr. Bach da abokan aikin sa.

A watan Nuwambar da ya shude, IOC ta sanar da cewa, za ta kara yawan kudin tallafawa gasar Olympic tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024 da kaso 16 bisa dari, wanda a yanzu ya kai dalar Amurka miliyan 590, domin karfafa taimakon da ‘yan wasan motsa jiki ke samu, da kwamitocin shirya gasar Olympic na kasashe, da kuma takwarorin su na nahiyoyi ko NOCs.

A daya bangaren kuma, akwai kusan dalar Amurka miliyan 100 da aka ware, don tallafawa hukumomin wasannin kasashe, da NOCs, nan zuwa karshen watan Yulin bana, baya ga wasu kudin dala miliyan 150 da za a iya baiwa NOCs karkashin shirin TOP, nan da karshen shekarar nan ta 2021.

Baya ga batun tallafin kudade, IOC na kuma gaggauta gudanar da sauye sauye a manufofin ta, bayan fara hakan a shekarar 2014, lokacin da aka amince da ajandar gasar Olympic ta 2020. Wani rahoto da IOC ta fitar a watan Disambar da ya shude, ya nuna cewa, an cimma nasarar aiwatar da kaso 85 bisa dari na ajandar gasar Olympic ta 2020, cikin shekaru 6 da suka gabata.

Game da hakan, Mr. Bach ya ce "Taken, a lokacin da muka kaddamar da ajandar gasar Olympic ta 2020, wanda kuma aka rabuta a bangon zauren Olympic: shi ne, ka canza ko a canza ka,' wannan take ya yi matukar dacewa da yanayi matsananci da ake ciki a yanzu".

Kwamitin OIC na aiki karkashin manufofi 3, wato aiki kan ka’ida, da wanzar da manufofi, da aiki da matasa. IOC na ci gaba da kokarin aiwatar da wadannan manufofi wajen daga martabar wasannin gasar Olympic. Har ila yau, mun ga yadda Paris ta rage adadin gadajen kwana da za a samar a yayin gasar 2024, a kauyen gasar Olympic, daga 17,000 zuwa 14,000, a wani mataki na rage kudaden kashewa. Kana an fitar da tsarin shigar da wasannin skateboarding, da na hawa duwatsu, da wasan zamiya na ruwa cikin gasar, domin jawo hankulan karin matasa su shiga gasar.

A daya bangaren kuma, an aiwatar da wasu matakai na daidaita gasar Olympic ta birnin Beijing dake tafe a shekarar 2022, ta yadda za ta dace yanayin da ake ciki, kuma daidai da yadda aka alkawarta shekaru 5 da suka shude, lokacin da aka mika izinin karbar bakuncin gasar ga birnin. Ana sa ran cimma nasarar shirya dukkanin wuraren da gasar za ta gudana nan da shekarar nan ta 2021, duk kuwa da kalubale daban daban da ake fuskanta.

Duk da cewa halin rashin tabbas bai wuce ba, wani abu da ake da tabbas a kan sa shi ne "Ba wanda ya yi zaton fuskantar wadannan matsaloli da ake ciki yanzu, gabanin barkewar wannan annoba."

Kamar dai yadda Mr. Bach ya rubuta, a cikin wasikar sa game da ayyukan shirya gasar ta Olympic: "Wannan annoba ta shafi kowa, za ta kuma taba dukkanin sassan zamantakewar al’umma, ciki har da dukkanin mu dake taka rawa a fannin wasanni. Amma idan mun koyi darussa daga halin da ake ciki a yanzu, muna iya kyautata yanayin gaba, har ma mu iya kaiwa ga karfafa ayyukan shirya gasannin Olympic na duniya a nan gaba."