logo

HAUSA

Gidauniyar ECW ta sanar da samar da kyautar dala miliyan 33.3 ga kasashen dake yankin Sahel

2021-01-05 11:26:42 CRI

Shirin nan na Education Cannot Wait (ECW) dake gwagwarmayar samar da ilimi, ya sanar da samar da tallafin dala miliyan 33.3, don magance matsalar kiwon lafiya da jin kai da ake fama da su a kasashen Burkina Faso, da Mali da Nijar dake tsakiyar yankin Sahel.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, asusun na ECW ya bayyana cewa, sabbin shirye-shiryen da za a gudanar a kasashen uku, za su hallara duk kan masu ruwa da tsaki a harkokin jin kan bil-Adama da raya kasa, inda za su samar da ilimi mai inganci ga yara da matasan da aka bar su a baya a yankin.

Za dai a kwashe tsawon shekaru uku ne ana gudanar da shirye-shiryen, inda ake fatan kashe karin dala miliyan 117.8, da za a samar tsakanin abokan hulda na kasa da na duniya, da sassa masu zaman kansu da manyan masu bayar da gudummawa.

Yara mata dai na daga cikin wadannan matsaloli suka fi shafa. A don haka, asusun na ECW ya fi mayar da hankali kan ba da ilimi ga yara mata, tun daga matakin makarantun reno har zuwa sakandare, ta hanyar tabbatar da cewa, kaso 60 cikin 100 na wadanda za su ci gajiyar shirin a dukkan kasashen, mata ne.

Haka kuma, asusun ECW ya dora muhimmanci wajen ganin ya kai ga wadanda aka bar su a baya, wajen samun kariya daga matsaloli na rikice-rikice. Abin da ke nuna cewa, yara da baligai masu nakasa, sun kunshi kaso 10 cikin 100 na wadanda za su ci gajiyar shirin na shekaru uku.

Za a raba tallafin ne daidai wa daida tsakanin kasashen uku, inda kowa ce kasa, za ta samu dala miliyan 11.1. (Ibrahim)

Ibrahim Yaya