logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yi Allah wadai da kisan ma’aikatan wanzar da zaman lafiya uku a CAR

2020-12-26 16:37:50 CRI

Babban sakataren MDD ya yi Allah wadai da kisan ma’aikatan wanzar da zaman lafiya uku a CARBabban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da babbar murya, kan hare-haren da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, suka kaddamar kan ma’aikatan wanzar da lafiya na MDD a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR).

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar ta bayyana cewa, hare-haren na ranar Jumma’a kan dakarun tsaron kasar CAR da ma dakarun MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, sun kai ga halaka masu aikin wanzar da zaman lafiya uku ‘yan kasar Burundi tare da jikkata wasu guda biyu.

Dujarric ya ce, babban sakataren ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan ma’aikatan wanzar da zaman lafiyar da suka halaka, gami da gwamnati da al’ummar Burundi, tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.

Guturres ya sake sanar da cewa, hare-hare kan ma’akatan wanzar da zaman lafiya, na iya zama laifukan yaki. A don haka ya yi kira ga mahukuntan Jamhuriyar Afirka ta tsakiya(CAR), da su gudanar da bincike kan wadannan munanan hare-hare kana su gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya, kamar yadda sanarwar ta bayyana. (Ibrahim)