logo

HAUSA

AU ta yi kashedi kan daukar doka kan wadanda suka yi kokarin wargaza zabukan CAR

2020-12-26 16:23:50 CRI

Hukumar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar Tarayyar Afirka(AU), ta yi kira ga dukkan kungiyoyi masu dauke da makamai da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR), da su guji aikata duk wani abin da ka iya hana gudanar da shirye-shiryen zabukan kasar da aka tsara.

Hukumar ta bayyana damuwa matuka, kan karuwar tashin hankali a kasar, da yadda fito na fito tsakanin wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da shugabannin ‘yan siyasa, ya haifar da karin kisan jama’a da bai kamata ba, da haifar da zullumi, da rashin sanin inda aka dosa ga al’umma.

Gobe Lahadi 27 ga watan Disamba ne dai, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya (CAR) za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Fabrairun shekarar 2019, tsakanin gwamnati wadda ke rike da kaso daya daga cikin biyar na yankunan kasar, da kungiyoyi masu dauke da makamai 14.(Ibrahim)