logo

HAUSA

Ministan tsaron Turkiyya: Takunkumin Amurka kan Turkiyya zai lahanta alakar kasashen biyu

2020-12-16 11:32:44 CRI

Ministan tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar, ya ce takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa Turkiyya, saboda sayo kayayyakin tsaro samfurin S-400 daga kasar Rasha, ya saba wa ka’idojin kawancen sassan biyu, wanda ke cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu, ya rawaiton ministan na Allah wadai da matakin Amurka, yana mai cewa, yanayin bukatun ayyukan soji, da na siyasa da ake ciki, bai dace da matakin da Amurka ta dauka kan Turkiyyar ba.

Sai dai duk da haka, a cewar Mr. Akar, Turkiyya za ta ci gaba da aiwatar da matakan tsaron yankunan ta, tare da kare dukkanin moriyar ta yadda ya kamata.

A nasa bangaren, shugaban sashen masana’antun tsaron Turkiyya Ismail Demir, ya ce gwamnatin kasar mai ci, a shirye take da ta kara inganta fannin masana’antun tsaron ta na gida, duba da yadda takunkumin Amurka kan kasar ke zama wani hannun ka mai sanda, game da bukatar dogaro da kai a wannan fanni.   (Saminu)

Saminu Alhasan