logo

HAUSA

Wang Yi ya yi jawabi yayin taron musamman kan COVID-19 na MDD

2020-12-04 14:21:52 CRI

Manzon musamman na shugaban kasar Sin, wanda kuma shi ne mamban majalisar gudanarwa kana ministan harkokin waje na kasar Sin, Mr. Wang Yi, ya halarci taron musamman dangane da yaki da cutar COVID-19 da MDD ta gudanar a jiya Alhamis, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Wang Yi ya ce, Sin na goyon bayan taron da majalisar ta gudanar, yana mai fatan kasashen duniya su kara hada kai da fahimtar juna don yakar wannan mumunar cuta tare.

Ya ce, ya kamata a yi iyakacin kokari hana yaduwar cutar ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma kara hadin kan kasa da kasa da kuma tabbatar da samar da allurar rigakafi ga dukkanin kasashen duniya musamman ma ga kasashe masu tasowa.

Ban da wannan kuma, ya ce kamata ya yi a kara karfin taimakawa kasashe masu tasowa, tare da baiwa masu karamin karfi tallafin jin kai. (Amina Xu)