logo

HAUSA

An kashe mayakan BH 5 yayin wani samamen soji

2020-11-30 10:40:26 CRI

Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta sun kashe mayakan BH 5, sannan wasu da dama sun jikkata, yayin wani samame da suka kai maboyar kungiyar dake jihar Borno, a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin, Benard Onyeuko, ya ce an kai samamen ne a ranar 27 ga watan Nuwamba, kuma sojojin na ci gaba da aikin fatattakar mayakan kungiyar daga maboyarsu a yankin.

Kakakin ya shaidawa kamfanin dallancin labarai na Xinhua cewa, yayin samamen da aka kai kauyukan Garal da Bulankesa da Pulka na jihar Borno, an kashe mayakan kungiyar 5.

Ya kara da cewa, da dama daga cikin mayakan sun tsere cikin dazuka da munanan raunukan harbi, yana mai cewa, manufar samamen ita ce, fatattakar ragowar mayakan kungiyar BH daga maboyarsu dake yankin arewa maso gabashin kasar. (Fa’iza Mustapha)