logo

HAUSA

OIC na fatan inganta hada kai da kasar Sin

2020-11-30 20:50:51 CRI

Kwanan baya, kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta kira taron ministocin harkokin waje a birnin Niamey, hedkwatar kasar Nijer, inda aka tsai da kudurin inganta hadin kai da kasar Sin.

Dangane da lamarin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying ta bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin ta yaba da kudurin OIC sosai dangane da inganta hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan