logo

HAUSA

An kaddamar da taro na 4 na rukunin kwamitin tsarin mulkin kasar Syria

2020-11-30 11:23:13 CRI

Ana shirya gudanar da taro na 4 na rukunin kwamitin tsarin mulkin kasar Syria a birnin Geneva, daga yau 30 ga watan Nuwanba zuwa ranar 4 ga watan Disamba. A jiya Lahadi, manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Syria, Geir Pedersen, ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, yana fatan bangarori daban daban za su yi imani da juna don sa kaimi ga warware batun Syria ta hanyar siyasa.

Geir Pedersen ya yi nuni da cewa, mai yiwuwa ta hanyar taron, a samar da wata dama ta neman warware yakin kasar Syria da ya shafe kimanin shekaru 10, ta hanyar siyasa kuma cikin lumana. Yana fatan shawarwari a sabon zagayen zai sa kaimi ga samun ci gaba kan kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhun MDD, wato tsagaita bude wuta da warware batun Syria ta hanyar siyasa, inda ya ce ta hakan, ‘yan Syria dake cikin mawuyacin hali, za su ga haske. (Zainab)