Sin tana da tasoshin amfani da fasahar 5G fiye da 700,000
2020-11-27 10:27:17 CRI
Rahotanni na cewa, ya zuwa karshen watan Octomba, Sin ta kafa tasoshin amfani da fasahar 5G fiye da dubu 700, inda bangarorin waje da aka hade da wadannan tasoshi suka kai fiye da miliyan 180.
Mataimakin ministan masana’atu da sadarwa Liu Liehong, ya gabatar da wadannan alkaluman ne a gun bikin bude taron fasahar 5G na kasa da kasa na shekarar 2020, wanda aka yi a kwanan baya a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin.
Liu ya nuna cewa, Sin na ingiza hada fasahar 5G da kamfanoni, kuma ana habaka fannoni dake amfani da ita. Alal misali, samar da kayayyaki ta amfani da na’urori na zamani, da kiwo lafiya, da makamashi, da aikin noma da sauransu.
Kungiyar kamfanoni masu samar da kayayyakin salula ta kasa da kasa ta ba da labarin cewa, ya zuwa tsakar watan Nuwamba, kamfanonin sakon wayar salula 122 daga kasashe ko yankuna 49 sun samar da fasahar 5G. An yi kiyasin cewa, ya zuwa karshen bana, yawan tsarin sadarwa na 5G da za a yi amfani da shi a duk fadin duniya game da kasuwanci zai kai fiye da 180. (Amina Xu)