Ikon mallakar fasaha ya taimaka wajen yaki da fatara a Sin
2020-11-27 11:10:51 CRI
Kasar Sin ta dora muhimmancin gaske, game da batun ikon mallakar fasaha, a matsayin jigon cimma nasarar rage talauci.
Da yaka bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, mataimakin shugaban hukumar NIPA, mai lura da ayyukan kare ikon mallakar fasaha na kasar Sin Mr. Gan Shaoning, ya ce Sin na lura da dabarun hade ikon mallakar fasahohi, da tamburan sana’oi, da alamun ci gaba masu nasaba da yankuna ko (GIs).
Gan Shaoning ya ce bisa hadin gwiwar hukumar kasa da kasa mai lura da ikon mallakar fasaha ko WIPO, hukumar NIPA ta kafa cibiyoyin tallafawa raya fasahohi da kirkire kirkire 51, a sassan kasar ta Sin daban daban, cibiyoyin da ke samar da hidimomi na kariyar fasaha, da samar da bayanai, ciki hadda shawo kan kalubalen binciken fasaha a fannin shuka, da sarrafa albarkatun gona, a yankuna mafiya fama da fatara.
Ya zuwa karshen watan Oktoba, an samar da yankunan gwaji 24 na alamun ci gaba masu nasaba da yankuna, don samar da kariya ga hajojin da ake samarwa, karkashin shirin kasar na rage fatara da samar da ci gaba. (Saminu)