Tanzania: Adadin masu harbuwa da HIV ya ragu da kusan rabi cikin shekaru 19
2020-11-25 12:50:05 CRI
Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV ko SIDA a kasar Tanzania wato (TACAIDS), ta ce adadin masu dauke da cutar a kasar ya yi kasa da kusan rabi cikin shekaru 19 da suka gabata.
Babban daraktan hukumar ta TACAIDS Leonard Maboko ne ya bayyana hakan a jiya Talata, yana mai cewa, sabbin masu harbuwa da HIV sun ragu, daga mutum 130,000 a shekarar 2001, zuwa mutum 68,400 a shekarar 2019.
Mr. Maboko wanda ya shaidawa taron manema labarai hakan a birnin Moshi, gabanin ranar cutar HIV ta duniya dake tafe ran 1 ga watan Disamba, ya ce muhimmiyar nasara da aka samu, ta rage adadin masu harbuwa da cutar a Tanzania, ya biyo bayan kara wayar da kan al’umma ne game da cutar, da kuma kara azama wajen amfani da magungunan kashe kafin ta.
Jami’in ya kara da cewa, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, mace mace sakamakon cututtuka masu nasaba da cutar HIV ko SIDA sun ragu, daga mutum 85,000 a shekarar 2001, zuwa mutum 25,000 a shekarar 2019.
Daga nan sai Maboko ya alkawarta shigar TACAIDS hadin gwiwa tare da sauran abokan hulda, don ci gaba da kara wayar da kan jama’a game da wannan cuta, ciki hadda batun dagewa wajen amfani da magungunan kashe kafin ta tsakanin masu dauke da ita. (Saminu)