logo

HAUSA

Iran na shirin kai karar Amurka kotun ICJ

2020-11-24 10:35:21 CRI

Ma’aikatar lafiya da ilimin likitanci ta kasar Iran, ta ce tana shirin gabatar da koke ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ko ICJ, game da yadda takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran din ke haifar da matsi, a bangaren kiwon lafiyar al’ummar ta.

Kamfanin dllancin labarai na kasar IRNA, ya rawaito mataimakin ministan lafiya Taher Mouhebati, wanda kuma ke kula da shirin mika korafin na cewa, takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran suna cutar da Iraniyawa ta fuskoki da dama.

Taher Mouhebati, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta kafar bidiyo, ya kara da cewa, Iran na da burin shigo da kayayyakin gwaji, da rigakafi, da na’urorin kiwon lafiya, amma a duk lokacin da ta yi yunkurin hakan tana haduwa da cikas.

Jami’in ya ce in banda kasar na dogaro da abun da take samarwa a cikin gida, da ta shiga mawuyacin hali ta fuskar kiwon lafiya.

A watan Afirilun da ya gabata, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya ayyana takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar sa, game da shigar da kayan kiwon lafiya a matsayin ta’addanci a bangaren lafiya.  (Saminu)