logo

HAUSA

An karrama tsoffin sojoji Sinawa saboda taimakon da suka ba Koriya ta Arewa wajen turjewa zaluncin Amurka

2020-10-22 14:00:46 cri

An karrama tsoffin sojoji Sinawa, wadanda suka fafata tare da taimakawa Koriya ta Arewa, turjewa zaluncin Amurka daga shekarar 1950 zuwa 1953. An karrama su ne yayin da ake cika shekaru 70 da sojojin Sin suka shiga yakin Koriya ta Arewa.

An ba da lambobin karramawar ne ga tsoffin sojojin da suke raye da sauran wasu jami'ai, da sunan JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin da kuma kwamitin aikin sojin kasar.

Lambar mai dauke da hoton sojan sa kai da kuma wasu abubuwa da suka hada da tattabara da aninai 5, na alamta cewa, yakin da Koriya ta Arewa ta yi da Amurka, yaki ne da aka yi bisa gaskiya da nufin kiyaye zaman lafiya da turjewa zaluncin Amurka, sannan alama ce dake cewa irin halin da aka nuna a yakin zai ci gaba da kasancewa abu mai daraja a wajen Sinawa.

Haka zalika, yana alamta kudurin kasar Sin da yakininta na kin ba da kai ga makiyanta da kiyaye zaman lafiya a duniya da kuma gina al'umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama. (Fa'iza Mustapha)