logo

HAUSA

Chadi: An dakile Boko Haram a kasar baki daya

2020-04-10 11:07:39 cri

Jiya Alhamis, sojojin kasar Chadi sun sanar da cewa, sun riga sun dakile dukkan dakarun Boko Haram baki daya dake cikin kasar.

Mai magana da yawun sojojin Azem Bermendoa Agouna ya bayyana a wannan rana cewa, sojojin sun kawo karshen aikin kai samame kan Boko Haram a ranar 8 ga wata, a cikin wannan mataki, sojoji 52 sun halaka, kuma an harbi 'yan Boko Haram 1000. A cewarsa, ana fatan kasashen Niger da Najeriya da dai sauransu su ci gaba da dakile 'yan Boko Haram da suka gudu.

An ce, a ranar 23 ga watan Maris, Boko Haram ta kai hari lardin teku dake kan iyakar yammacin Chadi. Alkaluman da sojojin kasar suka bayar na nuna cewa, harin ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 98, asara mafi tsanani da sojoji suka fuskanta wajen dakile Boko Haram. A Ranar 24 ga watan Maris, shugaban kasar Idriss Deby ya yi rangadi a wurin da aka kai hari, daga baya ya kafa wata cibiyar ba da jagoranci a fegen daga don ya ba da jagoganci kai tsaye wajen yakar Bokon Haram. (Amina Xu)