logo

HAUSA

An cafke sama da mutane 1,000 saboda karya dokar hana fita a Tunisia

2020-03-31 11:30:54 cri

Ma'aikatar cikin gida a Tunisia, ta ce jami'an tsaro sun cafke mutane 1,031 a jiya Litinin, sakamakon karya dokar hana fita da aka ayyana, a wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19 a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na TAP ya tabbatar da hakan. Ya kuma rawaito kakakin ma'aikatar Khaled Hayouni na cewa, an kame karin wasu mutanen su 197 sakamakon karya dokar gama-gari ta zama a gida da suka karya.

Gwamnatin Tunisia ta sanar da fara aiwatar da dokar zama a gida ta mako 2, wadda ta fara aiki tun daga ranar 22 ga watan nan, zuwa ranar 4 ga watan Afrilu mai zuwa. (Saminu)