Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-01 16:10:42    
Gasar kacici-kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin

cri

Tambayoyin da za mu yi muku su ne, na farko shi ne, daga wace shekara, an farfado da halalliyar kujerar jamhuriyar jama'ar Sin a M.D.D, na biyu kuwa shi ne, kasashe nawa ne da suka kafa huldar diplomasiyya da Sin. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji wannan shiri.


"Mu,'yan jam'iyyar kwaminis ta Sin, ba za yi maganganun karya ba, mun yi imani cewa, tsarin kwaminisanci na da kyau sosai, kuma mun amince cewa tsarin gurguza shi ma na da kyau, amma, a gun taron, ba za a yi furofaganda kan ra'ayin mutane ko kuma tsarin siyasa na wasu kasashe ba. Kungiyar wakilai ta Sin ta zo nan domin cimma matsaya guda da ku, ba wai don samun sabani ba ne."


Firaminista na gwamnatin Sin na wancan lokaci, kuma ministan harkokin waje na farko na sabuwar Sin Zhou Enlai ya fadi haka, a gun taron Bandung na shekarar 1955. A watan Afrilu na shekarar 1955, an yi babban taron duniya na bangarori daban daban a birnin Bandung,kana wannan karo na farko ne da sabuwar Sin ta halarci babban taron, a gun taron, kasashe da dama sun kara sanin manufofin da Sin ta gabatar, watau girmama wa juna kan mallakar kasa da cikakken yankin kasar da rashin kai wa juna hari, da rashin kutsa kai cikin harkokin siyasa na sauran kasashe, da yin zaman daidaici da samun moriyar juna, watau aiwatar da ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana. Ya zuwa yanzu, ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana sun riga sun zama tamkar tushen ka'idoji da kowa ya amince da su ne wajen kyautata dangantakar kasashen duniya.


A karkashin dambarawar siyasa da ake ciki, Sin ta tsaya tsayin daka kan ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana, haka kuma Sin ta kara samun abokai da yawa, musamman ma kasashe masu tasowa. A farkon lokacin da aka kafa sabuwar kasar Sin, sabo da manyan kasashen yamancin duniya sun mayar da kasar Sin saniyar ware, kasashe fiye da goma ne kawai, suka kulla huldar diplomasiyya da Sin, yanzu yawan kasashen da suka kulla dangantakar diplomasiyya da Sin ya kai 171.Tsohuwar tarayyar Soviet ta kasance babbar kasa ta farko da ta kulla dangantakar diplomasiyya da Sin, watau a ranar 2 ga watan Disamba na shekarar 1949, watau a lokacin rana ta biyu bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin. A watan Disamba na shekarar 1991, bayan da tsohuwar tarayyar Soviet ta wargaje, Rasha ta ci gaba da kiyaye dangantakar diplomasiyya da Sin.


A kwanakin baya da suka gabata, a birnin London shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya gana da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev, bangarorin biyu sun cimma matsaya guda a kan dangantakar abokantaka ta taimakawa juna bisa manyan tsare-tsare da ke tsakaninsu da mangance rikicin kudi na duniya da hadin gwiwa kan batutuwan duniya.
Tikhvinsky, wani tsoho mai shekaru 90 da haihuwa dan kasar Rasha, ya taba zama karamin jakadan tsohuwar tarayar Soviet da ke birnin Beijing, kuma ya gane wa idanunsa nasarorin da aka samu a kan dangantakar da ke tsakanin Soviet da Sin. A watan Oktoba na shekarar 2008, yayin da firaministan Sin Wen Jiabao ya kai ziyara a birnin Moscow, ya yi magana da Tikhvinsky.


Tikhbinsky ya ce: "Sin za ta shirya bikin murnar shekarar harshen Rashanci kuma Rasha za ta shirya bikin murnar shekarar harshen Sinanci, dukkansu za su kara kawo sharadi wajen bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Rasha a fannin al'adun 'yan adam, kuma muna iya karfafa hadin gwiwa tsakaninmu wajen ilmi da al'adu, don kara jawo hankulan matasa don su shiga cikin wannan aiki."


Wen Jiabao ya ce, A cikin shekarun 60 da suka wuce, Mr. Tikhvinsky ya taba zama karamin jakadan Soviet da ke birnin Beijing, kana ya halarci bikin kafa sabuwar kasar Sin, kasashen Sin da Rasha na da dauwamammen dankon zumunci tsakaninsu, kuma dangantakar tsakaninsu za ta ci gaba da samun bunkasuwa ba tare da fasawa ba. In Allah ya yarda, yayin da aka shirya shekarun don murnar harsuna na kasashen biyu, zan gayyace ka da ka yi ziyarar bude ido a birnin Beijing."


Bayan da aka shiga shekarun 60 da 70 na karnin da ya wuce, dangantakar tsakanin Sin da kasashen yammacin duniya ta sami kyautuwa. A wannan lokaci, Sin ta kafa dangantakar diplomasiyya da Amurka.


Daga karshen shekarun 60 ko 70 na karnin da ya wuce, Amurka da sauran kasashen yamancin duniya sun kyautata manufofinsu ga kasar Sin bisa moriyarsu, shahararrun bikin diplomasiyya na wasannin kwallon tebur ya bude hanyoyin mu'amala da aka katse tsakanin Sin da Amurka cikin shekarun 20 da suka gabata. A shekarar 1971, Kisinger ya kai ziyara a kasar Sin cikin sirri, har zuwa ga Nixon ya ziyarci Sin da ba da hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da Amurka, dangantakar kasashen biyu ta sami babban ci gaba. A watan Janairu na shekarar 1979, Sin da Amurka sun kafa huldar diplomasiyya tsakaninsu.


Yayin da aka kafa huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, cinikin kasashe biyu bai kai dalar Amurka biliyan 2.5 ba, amma yanzu wannan adadi ya zarce dalar Amurka biliyan 300. a watan Afrilu na bana, yayin da shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Amurka Barack Obama, bangarori biyu sun cimma daidaito a kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni ta karni na 21, kuma sun zayyana shirin bunkasa dangantakar kasashen biyu.


Dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha, da ta Sin da Amurka ta bayyana mana sauye-sauyen harkokin diplomasiyya da sabuwar Sin ta samu ko ba ta samu ba a cikin shekarun 60 da suka wuce, watau ba ta kafa kawace da sauran manyan kasashe ba, kuma ba ta kusanta ko kuma nisanta kanta da sauran kasashe ba bisa tsarin zamantakewar al'umma ko tsarin siyasa na kasar, kana ta kafa dangantakar sada zumunci da dukkan kasashen duniya a karkashin ka'idoji biyar na yin zaman tare cikin lumana, da kyautata dangantaka tsakaninta da sauran kasashe makwabta da kasashe masu tasowa? wannan ya sa karfin Sin ya inganta, kuma Sin ta gaggauta bunkasuwa, kuma ta kara samun hakkin yin magana a duniya.


Babban daki mai launin zinariya da ke ginin M.D.D wuri ne da ake yin taron M.D.D, a ko wace shekara, za a kara samun sabbin mambobin da suka shiga cikin kungiyar M.D.D. A watan Oktoba na shekarar 1971, a gun taron M.D.D a karo na 26, an zartas da kuduri mai lamba 2758 da gagarumin rinjaye, an farfado da halaccin hakki na kasar Sin a M.D.D.


Tsohon wakilin Sin da ke M.D.D Ling Qing ya taba yin aiki farfado da halaccin kujerar Sin a M.D.D. ya waiwayi baya da cewa:"Wannan ita ce babbar nasara da Sin ta samu, watau an farfado da halaccin kujerarta a kungiyar M.D.D, haka M.D.D ta sami ci gaba sosai.


Aikin farfado da kujerar Sin a M.D.D ya bude wani sabon babi na hadin gwiwa tsakanin Sin da M.D.D, haka kuma Sin ta kara kaddamar da harkokin diplomasiyya da kasashe daban daban, a cikin shekarun 30 da suka wuce kafin shekarar 1978, shugabannin Sin sun halarci bikin harkokin diplomasiyya sau 6 ne kawai, amma yanzu, Sin ta tsinci kanta kungiyoyin duniya fiye da 100 kuma ta kulla yarjejeniyoyin duniya sama da 300, kana ta gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D 22, haka kuma ta tura dubun dubatan ma'aikata masu aikin kiyaye zaman lafiya ga kasashen waje.
Bayan da aka shiga sabon karnin da ake ciki, Sin ta gabatar da ra'ayin gina daidaitaciyar duniya mai jituwa.


Ministan harkokin waje na Sin Yang Jiechi ya ce: A halin da duniya ke ciki, harkokin diplomasiyya da ake bukatar su ne samun moriya tare, harkokin diplomasiyya na Sin sun bi ra'ayin daidai wa daida da hadin gwiwa da cimma nasara tare da samun moriyar juna tare.(Bako)