Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-01 09:28:23    
Bunkasuwar karfin kasar Sin a cikin shekaru 60 da suka gabata

cri
Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhiryar Jama'ar Kasar Sin. Kuma a cikin wadannan shekaru 60 da suka gabata, kasar Sin ta canja daga wata kasa da ke fama da talauci sosai zuwa wata kasa mai wadata. To a cikin shirinmu na yau, bari mu waiwayi hanyar bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, da kuma ganin kyautatuwar zaman rayuwar jama'ar Sin. Tambayoyin da za mu gabatar muku a cikin shirinmu na yau su ne: Yaya matsayin tattalin arzikin kasar Sin yake a duniya? Kuma a wane birni ne za a shirya taron baje-koli na duniya na shekara ta 2010?

A ran 8 ga watan Agusta na shekara ta 2008, an kaddanar da taron wasannin Olympics a karo na 29 a Beijing, babban birnin kasar Sin, wanda ya tattara 'yan wasa daga kasashe da yankuna 204 a ciki, da kuma faranta ran biliyoyin mutane na duniya a fannin jin dadin wasanni.

Bayan kwanaki 16, an kashe wutar wasannin Olympics a filin wasa na shekar tsuntsu, ta haka an dasa wata kyakkyawar aya ga wasannin Olympics na Beijing. A gun bikin rufe wasannin, Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya ya nuna yabo sosai ga wasannin, ta cewar

"Ta wasannin Olympics a wannan karo, duniya ta kara fahimtar kasar Sin, kuma Sin ta kara fahimtar duniya. Lalle wasannin na da kyau kwarai da gaske har ma ba a iya kwatanta shi da na baya ba."

Game da Sinawa biliyan 1.3, wadannan kwanaki 16 lokaci ne da za su yi ta tunawa da shi har abada. He Zhenliang, mai gabatar da wasannin Olympics na kasar Sin kuma shugaban sashen kula da al'adu da ilmin Olympics na kwamitin wasannin Olympics na duniya ya bayyana cewa, Sinawa sun cimma burinsu sosai a wadannan kwanaki 16. Ya ce,

"Shirya wasannin Olympics burin Sinawa ne na dogon lokaci, amma a lokacin da ba za a iya cimma burin ba. Dalilin da ya sa haka shi ne shirya wasannin Olympics na bukatar dimbin mutane da kudade. Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin, ba mu da karfin shirya wasannin, wanda ya kasance kamar wani mafarki ne kawai."

Kamar yadda He Zhenliang ya fada, shirya wasannin Olympics na bukatar wasu sharuda. Kasar Sin ta kebe kudi Yuan biliyan 310 a fannonin gina filaye da dakunan wasannin Olympics da kuma yin kwaskwarima ga muhimman ayyukan yau da kullum. A lokacin da, kebe wadannan kudade masu dimbin yawa wani abu ne maras yiyuwa.

Lokacin da ake kafa sabuwar kasar Sin a shekara ta 1949, matsakaicin yawan kudin GDP da ko wane mutum kan samu ba su fi dala 50 kawai ba sakamakon yake-yake na dogon lokaci da kuma tabarbarewar tattalin arziki. Madam Liu Guixian mai shekaru 77 da haihuwa ta bayyana cewa,

"A wancan lokaci, mun yi fama da talauci sosai. Ina da yara da yawa, amma kudin shiga dan kadan ne. Ko da yaushe ba mu da isasshen abinci. A lokacin hunturu kuma, mu bakwai muna da barguna biyu ne kawai."

A shekara ta 1978, kasar Sin ta kaddamar da aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, da kuma sanya muhimmanci kan raya tattalin arziki. Don haka kasar Sin ta samu babban ci gaba a kan aikin zamananci.

A ran 30 ga watan Satumba na shekara ta 1980, Madam Liu Guixian ta bude wani karamin dakin cin abinci a birnin Beijing. Kuma jim kadan bayan da aka yi wasan wuta don taya murnar bude dakin, nan da nan mutane suka yi jerin gwano a kofar dakin cin abinci, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da wannan shi ne dakin cin abinci mai zaman kai na farko a kasar Sin.

Zaman rayuwar Madam Liu ya samu kyautatuwa a bayyane sakamakon wannan karamin dakin cin abinci. Yanzu ita da mijinta sun sayi wani Siheyuan a bayan birnin Beijing, wanda shi ne wani tsarin gidajen kwana masu fasali hudu irin na da domin jin dadin zaman rayuwarsu.

Bayan da aka bude kofa ga waje da kuma yin kwaskwarima a gida, duk fadin kasar Sin ya samu canzawa kwarai, tsarin tattalin arziki kuma ya canja daga tsarin shiri zuwa tsarin kasuwanci sannu a hankali. Irin wannan sauyi ya karfafa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, kuma ana iya sayen kayayyakin da ake so. Yanzu yawancin gidajen Sinawa suna da talibijin da firiji da injin dauraya da kuma kwamfuta, har ma da motocin da a da mafarkinsu kawai suke yi. Ma Yunliang mai shekaru 27 da haihuwa, wani ma'aikaci ne na wani kamfani, ya sayi wata mota a watan jiya. Kuma ya gaya mana cewa,

"Yanzu sayen motoci ya zama ruwan dare, yawan kudaden shiga na shekara daya ko biyu na iya sayen wata mota. Bayan da na sayi mota, na ji dadin yawon shakatawa a bayan birnin Beijing, kuma ba zan shiga motar bus ba a kan hanyar zuwa aiki."

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, Jimillar kadaden da kasar Sin ta samu daga aikin samar da kayayyaki a cikin gida a shekara ta 2008 ta ninka sau fiye da 400 bisa ta shekara ta 1952, kuma matsayin tattalin arzikinta yake kai na hudu a duniya, matsakaicin yawan kudin GDP da ko wane mutum ya samu ya zarce dala 3000.

Sakamakon kyautatuwar zaman rayuwa, yanzu ba kawai Sinawa suna iya sayen dakunan kwana da motoci ba, hatta ma suna sha'awar yawon shakatawa. Bugu da kari kuma, sakamakon kara bude kofa ga waje, yanzu ana iya samun Sinawa masu yawon shakatawa a wurare daban daban na duniya. Mr. Hao Xin wani mutum ne da ke sha'awar yawon shakatawa a ketare sosai. Ya ce,

"Sau tari na kan yi yawon shakatawa a ketare a ko wace shekara guda ko shekaru biyu. Na taba zuwa kasashen Birtaniya da Singapore da Malaysia don shan iska. Amma ba a iya yin hasashe kan wannan batu ba yau da shekaru fiye da goma da suka gabata, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da a wancan lokaci, har ma ba a da kudin yawon shakatawa a sauran lardunan kasar Sin."

Amma a shekara mai zuwa, Mr. Hao ba shi da shirin yawon shakatawa a ketare, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da zai je birnin Shanghai don sheda halayen musamman na kasashe daban daban, wanda za a shirya bikin baje koli na duniya a watan Mayu a ciki.

Yu Zhengsheng, sakataren kwamitin Shanghai na JKS kuma shugaban zartaswa na kwamitin kula da ayyukan bikin baje koli na duniya na Shanghai ya bayyana cewa, yanzu birnin Shanghai ya riga ya kebe kusan Yuan biliyan 20 a fannonin shimfida hanyoyin jiragen kasa da ke karkashin kasa da hanyoyin mota da kuma raya kayayyakin jama'a na farfajiyar shirya bikin. Kuma ya kara da cewa,

"A watan Maris na shekara mai zuwa, tsayin hanyoyin jiragen kasa da ke karkashin kasa na Shanghai zai kai kilomita 400, wanda ba a iya zatonsa a lokacin da ba. Kyautatuwar zirga-zirga za ta ba da taimako sosai ga kyautatuwar zaman jama'a da kuma bunkasuwar tattalin arziki."(Kande Gao)