Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-01 09:28:23    
Nasarorin da aka samu ta fannin tsarin dokoki a cikin shekaru 60 da aka kafa jamhuriyar jama'ar Sin

cri

Yau za mu waiwayi hanyar da sabuwar kasar Sin ta bi wajen kafa tsarin dokokinta a cikin shekaru 60 da suka wuce, kuma tambayoyin da za mu yi muku su ne: ra'ayoyin jama'a nawa aka tattara domin tsara kundin mulki na farko a kasar Sin? Kuma dokoki nawa ne Sin take tafiyarwa yanzu?

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, marigayi Mao Zedong, tsohon shugaban kasar Sin, ya sanar da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, abin da ya bude wani sabon babi na tarihin al'ummar kasar Sin.

Wannan sabon mulkin da aka kafa ya sha bamban sosai da tsarin zaman al'umma na gargajiyar kasar Sin, wato a karkashin mulkin, ba ma kawai ya kasance jama'a su ne suke rike da ikon kasa a hannunsu ba, haka kuma ana neman cimma rashin kasancewar ci da gumin jama'a da rashin nuna bambanci da kuma samun wadatar jama'a baki daya. To, sai kuma a lokacin da aka shiga shekara ta biyar da kafuwar sabuwar kasar Sin, aka fito da "tsarin mulkin jamhuriyar jama'ar Sin", wanda kafin an fito da shi, an mika daftarinsa ga jama'a don su yi shawarwari, kuma gaba daya aka samu ra'ayoyin jama'a har miliyan 1 da dubu 380. Bisa ra'ayoyin, an yi wa tsarin mulkin gyare-gyare, sa'an nan aka fito da shi. Har zuwa yanzu, bangaren dokoki na nuna yabo ga wannan tsarin mulki sabo da irin tasirin da ya yi ta fannin raya tsarin dokokin kasar Sin. A yayin da yake hira da wakilinmu, Mr.Li Buyun, wani masanin ilmin doka na kasar Sin ya tabo wani batu musamman a kan ka'idoji biyu da aka tanada a cikin wannan tsarin mulkin kasar. Ya ce,"Muna da tsarin mulkin kasar da aka fito da shi a shekarar 1954, wanda ke da inganci. Akwai ka'idoji biyu da aka bi cikin tsarin mulki din, wato cin gashin kai a wajen gudanar da harkokin shari'a da kafa doka bisa dimokuradiyya."

Akwai kuma sauran dokoki biyu da aka fito da su a lokaci daya da tsarin mulkin kasar na farko, wato su ne "dokar taron wakilan jama'ar kasar Sin" da "dokar kotun jama'ar Sin", kuma a sakamakonsu, hukumomin ikon mulkin kasar Sin da na shari'a sun fara aiki bisa doka. Daga nan kuma, kasar Sin ta shiga wani lokaci mai kyau wajen raya tsarin dokokinta.

Shekarar 1978 ta kasance wata shekarar da da kyar za a manta da ita a tarihin sabuwar kasar Sin. Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da aka fara aiwatarwa a wannan shekara ta sanya kasar Sin a kan wata hanyar samun ingantuwar kasa. A fili ne kasar Sin ta gabatar da "raya dimokuradiyyar gurguzu da dokokin gurguzu". A yayin fitowar jerin dokoki, ciki har da dokar daukaka kara da dokar hukunta laifuffuka da dai sauransu, kasar Sin ta shiga wani kyakkyawan lokaci na raya tsarin dokoki.

A yanzu haka dai, wani tsarin dokokin da ke da sigar musamman na kasar Sin ya riga ya kafu a nan kasar bisa tsarin mulkinta, kuma an tanada jerin ka'idoji da ya kamata a bi cikin tsarin mulkin kasar, ciki har da "kowa na zaman daidai a idon doka", da "tafiyar da harkokin kasa bisa doka" da "girmama hakkin bil Adama da ba shi kariya" da "kiyaye hakkin jama'a na mallakar dukiyoyinsu".

A halin yanzu, tsarin mulkin kasar Sin da kuma dokar kafa dokoki sun kafa wani hadadden tsarin doka da ke da matakai daban daban yadda ya kamata, ciki har da tsarin mulkin kasar da dokokin da ke jibantar tsarin mulkin kasar da dokokin fararen hula da dokokin kasuwanci da dokokin tattalin arziki da dokokin hukunta manyan laifuffuka da dai sauransu, wadanda yawansu ya kai har 231. A sakamakon haka, an tabbatar da samun dokoki a dukkan fannonin tattalin arziki da siyasa da al'adu da zaman al'umma da dai sauransu, an inganta tsarin dokokin kasar Sin kwarai da gaske.

Ba za a iya lisafta nasarorin da aka samu ta fannin raya tsarin dokokin kasar Sin ba, misali, an samu babban ci gaba wajen ba da ilmin doka, kuma yanzu haka akwai jami'o'i fiye da 600 da ke koyar da ilmi a fannonin doka. Ban da wannan, an kuma sami babban ci gaba ta fannin nazarin dokoki, kuma dimbin littattafan ilmin doka da aka wallafa sun shaida mana wannan lamari. A sa'i daya kuma, an tabbatar da kafa doka bisa kimiyya da dimokuradiyya, yanzu haka, ya zama wajibi a nemi ra'ayoyin al'umma a kan daftarin dokoki. Ban da wannan, jama'ar kasar Sin sun kuma gane wa idanunsu yadda ake ta kara gudanar da harkokin mulki bisa doka da kuma tafiyar da harkokin shari'a bisa adalci, an kuma inganta rawar da dokoki ke takawa ta fannin kayyade iko da kuma sa ido a kan yadda ake amfani da iko.

Amma abin da ya fi faranta ran Mr.Li Buyun, masanin ilmin doka na kasar Sin ya wuce haka, kamar yadda ya fada,"ra'ayoyin gudanar da harkoki bisa doka da kuma hakkin bil Adam sun shiga zukatan jama'a, har sun zama tamkar makaminsu, wannan ya faranta mini rai sosai."

A ganin Mr.Li Buyun, a cikin shekaru 60 da aka kafa sabuwar kasar Sin, an samar wa Sinawa tabbacin kula da hakkin bil Adam ta fannin doka. Ba ma kawai furucin nan na "girmama da tabbatar da hakkin bil Adam da sa kaimi ga bunkasuwar harkokin bil Adam daga dukkan fannoni" ya sami farin jini daga al'umma ba, har ma an tanadi "girmama da tabbatar da hakkin bil Adama" cikin tsarin mulki. Idan mun yi la'akari da yawansu, za mu gane cewa, yawan dokokin da ke shafar hakkin bil Adama da yarjejeniyoyin duniya da kasar ta amince ya kai sama da 250, an kuma samu dokoki na takanas da ke tabbatar da wasu rukunonin jama'a na musamman, ciki har da mata da tsofaffi da matasa da nakasassu da 'yan kananan kabilu da sauransu.

Mr.Li Buyun, ya taba sa hannu cikin aikin raya tsarin dokokin kasar Sin, ya kuma gane wa idonsa a kan yadda tsarin dokokin kasar Sin ya yi ta ingantuwa. Bunkasuwar tsarin dokokin kasar Sin ba abu ne mai sauki ba, amma idan aka yi tunani a kansa, za a gane cewa, a cikin shekarun 60 da suka gabata, kasar Sin ta raya wannan tsari na dokokinta ne mataki bisa mataki, wato na farko, Sin ta fi mai da hankalinta a kan inganta sabon mulki, sa'an nan, ta karkata hankalinta zuwa ba da kariya ga ikon kasa da ya tafi yadda ya kamata. Daga bisani kuma, ta samar da yanayin doka mai kyau ga manufarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da kuma tafiyar da tsarin tattalin arzikinta na kasuwanci. A yanzu haka kuma, tana dora muhimmanci iri daya a kan ba da kariya ga ikon kasa da moriyar kasa da moriyar al'umma da kuma moriyar mutane masu zaman kansu. Kamar yadda firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya taba bayyana cewa,"gurguzu bai saba wa dimokuradiyya da dokoki ba. Dimokuradiyya da doka da 'yanci da hakkin bil Adam da zaman nuna daidaito da kaunar kowa ba abubuwan da kawai ake samu cikin tsarin jari-huja ba ne, amma wasu nasarori ne da aka samu daga wayewar kan dan Adam a cikin tsawon tarihin duniya, haka kuma buri ne na 'yan Adam baki daya."

A yayin da gudanar da kome da kome bisa doka ke kara zamowa Sinawa ruwan dare, ana kuma ci gaba da raya tsarin dokoki a kasar Sin. Masanan ilmin doka na kasar Sin, ciki har da Li Buyun suna ganin cewa, tsarin dokokin kasar Sin na bunkasa ne kan wata hanyar da ke da sigar musamman ta kasar Sin, amma kuma, a yayin da Sin ke kara yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje, za a kuma kara fadada hanyar bisa nasarorin da aka samu a duniya baki daya.

To, masu sauraro, gasar kacici-kacici dangane da cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin da muka gabatar muku ta fannin bunkasuwar tsarin dokokin kasar a cikin shekaru 60 da suka wuce ke nan, kuma tambayoyinmu su ne: ra'ayoyin jama'a nawa aka tattara wajen fito da tsarin mulki na farko a kasar Sin? Kuma dokoki nawa ne Sin take tafiyar yanzu? Da fatan za ku turo mana amsoshinku, kada kuma ku manta, kuna iya aiko mana amsoshi zuwa akwatinmu a gidan waya, wato Hausa Service, CRI-24, China Radio International, akwatin gidan waya, 4216, Beijing, Jamhuriyar jama'ar Sin. Ban da wannan, kuna kuma iya aiko mana sakonni na Email zuwa hausa@cri.com.cn, da fatan Allah ya karfafa dankon zumunci a tsakaninmu.(Lubabatu)