Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-01 09:28:23    
Bayani kan dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin aikin gona yau da shekaru 60 da suka gabata

cri
Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 60 da kafa sabuwar kasar Sin. Yau da shekaru 60 da suka gabata, gwamnatin kasar ta dade tana dukufa ka'in da na'in kan raya harkokin kauyuka, har ma zaman rayuwar manoma ya samu manyan sauye-sauye. To, tambayoyi biyu da za mu yi muku a yau su ne, tambaya ta farko, da filayen gonaki da fadinsu ya kai kashi nawa na fadin duniya ne kasar Sin ta ciyar da jama'arta da yawansu ya kai kashi 22 cikin dari na duniya? Tambaya ta biyu ita ce, menene yawan hatsin da kasar Sin ta samar a shekara ta 2008?

Karancin abinci ya taba kasancewa wata babbar matsala dake ciwa jama'ar kasar Sin tuwo a kwarya. Mista Long Yongtu, babban sakatare na dandalin tattaunawa na Bo'ao na hadin-gwiwar kasashen Asiya, wanda aka haife shi a shekara ta 1943 a birnin Changsha na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Long ya gayawa wakilinmu cewa, akasarin Sinawa wadanda shekarunsu suka yi daidai da nasa, sun taba fama da matsalar karancin abinci, inda ya ce:

"Akasarinmu mun taba fama da matsalar karancin abinci, da dai sauran wahalhalu. Duk lokacin da muka ji yunwa, sai mu dafa kabewa mu ci. Don haka ne a halin yanzu, ba na jin dadin kabewa ko kadan."

Kamar Nijeriya, kasar Sin babbar kasar noma ce, wadda galibin mutanenta manoma ne. A cikin shekarun 1940 na karnin da ya gabata ne, sakamakon tsoffin hanyoyin da aka bi wajen gudanar da harkokin gona, da mummunan tasirin da bala'un fari da ambaliyar ruwa suka haifar, ayyukan gona a kasar Sin a baya-baya suke, haka kuma akwai mutane da dama wadanda suka rasa abinci da sutura a kasar.

A shekara ta 1949 ne, aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Daga baya, kasar Sin ta shafe tsawon shekaru 3 tana yin gyare-gyare ga tsarin rarraba gonaki, da aiwatar da manufar rarraba amfanin gona, da kayayyakin gona, gami da dabbobi ga manoma, wadda ta samu cikakken goyon-baya daga manoma. Haka kuma, ayyukan gona a kasar Sin sun samu farfadowa kwarai da gaske, yawan hatsi da auduga da aka samar ya zarce na baya. Bayan shekara ta 1952, kasar Sin ta kara gudanar da manyan ayyukan ban ruwa, da yin gyare-gyare kan fasahohin aikin gona, a wani kokarin kyautata sharadin aikin gona, da kara samar da amfanin gona. Zuwa karshen shekarun 1970 na karnin da ya gabata ne, yawan hatsi da auduga da aka samar ya ninka har sau 1, idan an kwatanta da na shekara ta 1952.

Amma ko da yake yawan hatsi da aka samar ya karu sosai, sakamakon karuwar yawan mutane a kasar Sin, yawan amfanin gona da aka samar ya kasa biyan bukatun jama'a. Yang Jiliang, wani mazaunin kauyen Bisheng na birnin Chizhou na lardin Anhui ya ce, karancin abinci ya dade da kasancewa babbar matsala da ta yi katutu a kauyensa:

"A shekarun 1960 da 1970 na karnin da ya gabata ne, yawan hatsin da aka samar ya kasa biyan bukatun jama'a, don haka ne mutane suka yi ta cin ganyaye."

A karshen shekara ta 1978, kauyen Xiaogang na lardin Anhui ya tsaida kudurin rarraba gonaki zuwa ga manoma domin biyan bukatunsu, sakamakon haka, yawan hatsi da aka samar a waccan shekara ya ninka har sau 4 idan an kwatanta da na matsakaicin yawan hatsi da aka samar a shekaru 10 da suka gabata. A shekara ta 1980, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar yada abun da kauyen Xiaogang ya yi a duk kasar, wanda ake kiran shi "tsarin daukar nauyin aikin samar da albarkar noma ta hanyar yin kwangila da iyalan manomi tare da yin la'akari da yawan amfanin gona da ake samu".

Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, daga shekara ta 1978 zuwa 1984, matsakaicin yawan amfanin gona da kasar Sin ta kan samar a kowace shekara ya karu da kashi 8 bisa dari. Daga wancan lokaci ne, yawan hatsin da kasar ta samar yake ta karuwa ba kakkautawa. Ya zuwa shekara ta 2008, yawan hatsin da kasar Sin ta samar ya zarce ton miliyan 500, kuma da filayen gonaki da fadinsu ya kai kashi 7 bisa dari na fadin duniya ne, kasar Sin ta ciyar da jama'arta da yawansu ya kai kashi 22 bisa dari na duniya.

Madam Liu Dongzhu, jami'a mai kula da shirin ajiyar hatsi ta hukumar kula da harkokin hatsi ta kasar Sin ta ce, Sinawa sun warware matsalar karancin abinci sakamakon matukar kokarin da suka yi, lallai wannan abu ne mai ban al'ajabi. Madam Liu ta ce:

"Kasar Sin ta dade da tsayawa tsayin daka kan manufar biyan bukatun jama'a cikin gida a fannin abinci. A cikin 'yan shekarun nan, yawan hatsin da ake bukata ya yi daidai da yawan hatsin da ake samarwa cikin gida."

Domin kara baiwa manoma kwarin-gwiwar su shuka hatsi, a cikin 'yan shekarun da suka gabata ne, gwamnatin kasar Sin ta bayar da karin kudin tallafi ga manoma kai-tsaye don shuka hatsi, da sayen kayayyakin gona da dai sauransu, zuwa shekara ta 2007, yawan kudin tallafi da gwamnatin kasar ta bayar ga manoma ya zarce Yuan biliyan 60. Kazalika kuma, gwamnatin kasar ta kara samar da guraban aikin yi ga manoma 'yan ci rani, a wani kokarin bunkasa tattalin arziki a kauyukan kasar. Dadin dadawa, yau da shekaru 8 da suka wuce, Sin ta fara soke kudin haraji a fannin noma, har zuwa shekara ta 2006, gaba daya an soke kudin harajin daga dukkan fannoni.

Sakamakon wadannan matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka, zaman rayuwar manoma a kasar Sin ya samu kyautatuwa kwarai da gaske. A yayin da yake magana kan zaman rayuwar mazauna kauyen Bisheng, Yang Jiliang ya yi farin-ciki matuka. Ya ce, yanzu akwai mazauna kauyen da dama wadanda suke yin amfani da wayar tafi-da-gidanka, akwai kuma wadanda suka riga suka sayi motoci. Yang Jiliang ya ce:

"Lallai zaman rayuwarmu ya kyautata kwarai da gaske. Yanzu muna yin amfani da kayayyakin zaman rayuwa na yau da kullum iri-iri, ciki har da fitilun wutar lantarki, da wayar tarho."

A halin yanzu dai, matsakaicin kudin shiga da manoman kasar Sin suke samu ya ninka har sau 30 idan an kwatanta da na shekara ta 1978, kuma yawan mutanen da suke fama sosai da kangin talauci ya ragu daga miliyan 250 zuwa kasa da miliyan 15.

Yang Jiliang ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar ta zuba karin kudi a fannin raya muhimman ababen biyan bukatun jama'a a yankunan karkara, inda ya ce:

"Sakamakon kulawa da cikakken goyon-baya da gwamnatin kasar ta nuna, zaman rayuwar mutane a yankunan karkara ya samu kyautatuwa sosai daga fannoni daban-daban, ciki har da hanyoyin sufuri, da hidimomin aikin jiyya, gami da gidajen kwana a kauyuka."

Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, an ce, zuwa shekara ta 2020, matsakaicin kudin shiga da manoman kasar zasu samu zai ninka sau 1 idan an kwatanta da na shekara ta 2008, za'a kuma kawar da kangin talauci a duk kasar. Yanzu, gwamnatin kasar Sin tare da jama'arta suna kokari ba tare da yin kasala ba wajen neman cimma wannan buri.

Yanzu bari in maimaito muku tambayoyi biyu da muka gabatar muku. Tambaya ta farko ita ce, da filayen gonaki da fadinsu ya kai kashi nawa na fadin duniya ne kasar Sin ta ciyar da jama'arta da yawansu ya kai kashi 22 cikin dari na duniya? Tambaya ta biyu ita ce, menene yawan hatsin da kasar Sin ta samar a shekara ta 2008?

Ina fatan za ku cimma nasara da yardar Allah!(Murtala)