Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-05-27 21:21:18    
Bayani kan yin zirga-zirga a sararin samaniya

cri

Yau za mu soma daga wani bayani dangane da gasar kacici-kacici ta murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Babban taken bayanin shi ne, yin zirga-zirga a sararin samaniya, wato gasar da ake yi dangane da nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu ta fannin kimiyya da fasaha a cikin shekaru 60 da suka wuce.

Jama'a masu sauraro, shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin. A cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin ta yi ta samun ci gaba a fannin kimiyya da fasaha. Yau za mu bayyana muku wadannan nasarorin da kasar Sin ta samu bisa misalin da aka samu dangane da yadda mutanen kasar Sin suka yi tafiya a sararin samaniya a karo na farko. Yanzu ga tambayar farko da za mu gabatar da ita mai cewa, mene ne sunan mutumin kasar Sin da ya yi tafiya a sararin samaniya a karo na farko? Tambaya ta biyu ita ce, wace shekara ce kasar Sin ta soma harba tauraron dan adam a karo na farko? To, yanzu bari mu gabatar da cikakken bayani dangane da lamarin.

Na riga na fito daga kumbo mai lamba Shenzhou-- 7, ina lafiya sosai, ina yin gaisuwa ga jama'ar duk kasar Sin da na duk duniya.

A ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2008, a sararin samaniya dake nesa da yankin kasa da kilomita fiye da 300, dan sama jannati na kasar Sin mai suna Zhai Zhigang ya yi tafiya a sararin samaniya a karo na farko. Abin da kuka saurara dazun nan muryar Zhai Zhigang ce yayin da ya yi magana a sararin samaniya don nuna gaisuwa ga jama'ar duk kasar Sin da na duk duniya. Wannan ya bayyana cewa, Zhai Zhigang shi ne mutumin farko na kasar Sin da ya yi tafiya a sararin samaniya a karo na farko, daga nan sai kasar Sin ta zama ta uku a fasahar fitar mutane daga kumbon da ke sararin samaniya bayan kasar Rasha da Amurka.

Fasahar daukar mutane zuwa sararin samaniya fasaha ce da ta hada da kimiyya a fannoni da yawa gu daya, wadda ta wakilci hakikanin karfin kasar ta dukkan fannoni, tana da nasaba da tsare-tsare guda 7 na harba rokoki da kumbuna zuwa sararin samaniya da bincike kan sadarwa da sauransu, kuma aiki ne mafi girma da ke kasancewa cikin rikice-rikice mafi tsanani tare da hadari sosai, kuma aiki ne da ke yin amfani da fasahohi na zamani sosai da sosai. Mataimakin babban mai ba da jagoranci ga aikin zirga-zirgar kumbon daukar mutane zuwa sararin samaniya na kasar Sin malam Zhang Jianqi ya bayyana cewa, idan ba a sami fasahohin kimiyya na zamani sosai da karfin yin bincike kan kimiyya ba, to ba za a iya fitowa daga kumbon da ke sararin samaniya ba. Ya bayyana cewa, Kumbonmu na sararin samaniya dole ne ya yi amfani da wasu fashohin kimiyya, da kuma yin bincike kan yadda za a dinka rigunan da 'yan sama jannati za su sanya a sararin samaniya da kuma fasahar yin amfani da kwamufuta ta zamani sosai da fasahar yin wasu sabbin kayayyaki da sauransu.

Injiniyoyin kasar Sin da yawansu ya kai dubu 100 sun halaci aikin, wadanda suka fito ne daga hukumomin binciken kimiyya da masana'antu fiye da 100. Yanzu, kasar Sin ta sami masana harkokin kimiyya da fasaha da yawansu ya kai miliyan 35, kuma yawan kudaden da aka yi amfani da su ya kai kudin Sin Yuan biliyan 300.

A lokacin kafa sabuwar kasar Sin ba da dadewa ba, gwamnatin kasar Sin ta kuma mai da hankali sosai ga raya sha'anin bunkasuwar kimiyya da fasaha, ita kuma ta tsara shirin raya kimiyya da fasaha na dogon lokaci. A shekarar 1964, wani girgije mai sifar lema wato mai sifar halittar nan ta mushroom cikin turanci ya tashi a sararin samaniya na hamadar da ke arewa maso yammacin kasar Sin,wannan ya yi wa duk duniya al'ajabi sosai, wato kasar Sin ta yi nasarar fasar bom din nukiliya a karo na farko. Bayan shekaru uku da suka shige, kasar Sin ta kuma yi nasarar fasar bom da aka yi amfani da iskar hydrogen. A shekarar 1970, kasar Sin ta yi nasarar harba wani tauraron dan adam mai suna Dongfanghong a karo na farko. Wani jami'in sashen kimiyya da fasaha na kasar Sin mai suna Mei Yonghong ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta kai wani babban matsayi wajen raya kimiyya da fasahohi, mun riga mun sami cikakken tsarin ilmi da ba shi da yawa a duniya. Sa'anan kuma, mun riga mun sami wadatattun albarkatun mutane masu aikin kimiyya da fasahohi, ciki har da masu yin bincike kan kimiyya da fasaha, dukkansu suna jerin gaba a duniya.

A shekarar 1978, kasar Sin ta soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kasashen waje kofa, daga nan kasar Sin ta soma kasancewa cikin lokacin samun sakamakon kimiyya da fasaha mafi yawa. Direktan sashen yin bincike kan kimiyya da fasaha na kasar Sin mai suna Xu Heping ya bayyana cewa, hakikanin karfin da kasar Sin ta samu a fannin kimiyya da fasaha ya riga ya rage ratar da ke tsakaninta da kasashe masu ci gaba na duniya, kuma wasu fannoninta sun riga sun shiga jerin gaba a duniya, kuma ta kara tasirinta a duniya.

A lokacin da mutanen kasar Sin suke more sakamakon da aka samu wajen kimiyya da fasaha ga zaman rayuwarsu, sun yi alfahari sosai, sa'anna kuma suna kasancewa cikin irin hali mafi kyau a sakamakon samun nasarar harba kumbon da ke daukar mutane zuwa sararin samaniya. Wasu mutane sun bayyana cewa, Wata mai suna malama Wang ta bayyana cewa, na yi alfahari sosai da sosai, a ganina, wannan sakamako ya almanta bunkasuwar da kasar Sin ta samu sosai a fannin kimiyya da fasaha, kuma karfin kasar Sin na kara ingantawa, sa'anan kuma na da ma'ana mai muhimmanci sosai, ina son in gaya wa 'yan sama jannati cewa, su ne jaruman al'ummar kasar Sin.

Malami Liu ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar harba kumbo mai lambar Shenzhou-7, wannan ya zama babban ci gaba da kasar Sin ta samu a cikin tarihin kasar na yin zirga-zirga a sararin smaniya , duk duniya sun yi mamaki sosai, kuma mun yi alfahari sosai.

A watan Oktoba na shekarar 2003, dan sama jannati na kasar Sin mai suna Yang Liwei karo a farko ya shiga kumbo ya yi zirga-zirga a sararin smaniya cikin sa'o'I 21 ko fiye, a shekarar 2005, 'yan sama jannati na kasar Sin biyu su ma sun yi nasarar zirga-zirga a sararin samaniya cikin kwanaki 5. A watan Satumba na shekarar 2008, 'yan sama jannati uku na kasar Sin su ma sun yi nasarar zirga-zirga a sararin samaniya, a wannan karo, dan sama jannati mai suna Zhai Zhigang ya fito daga kumbu kuma ya yi tafiya a karo na farko a sararin samaniya.

A watan Oktoba na shekarar 2007 kuma, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraro mai lamba Chang E-1 don yin bincike kan wata, bayan shekara daya, tauraron ya kammala dawainiyoyinsa daban daban na yin bincike lami lafiya.(Halima)