logo

HAUSA

Babi20: Gidan kayayyaki

2020-10-30 10:07:44 CRI

>>[Zanen a Tarihi]

Qiu Ying da zanensa na wurin al'ajabi

Qiu Ying (1493-1560AD),wani sunansa Shi Fu,suna daban kuwa Shi Zhou.Mutumi ne da aka haife shi a Taicang da ke cikin Jiangsu.Asalin aikinsa shawa wa kayayyaki fenti.Ya taba koyon yin zane daga mashahurin maizane Zhou Chen.Ya fi kwarewa wajen yin zanen tsaunuka da koguna da mutane har da kyawawan mata.

Zanen "wurin al'ajabi",zane ne mai launinkore-kore da aka yi surar muhalli dake da tazara mai yawan gaske daga wurin zama na mutane.Ga tsaunuka masu tsayi sun yi sama da kasa,gajimare na tashi,hazo na tafiya sannu a hankali,wani haikali ya buya a ciki,wani lokaci kuma ya bayyanu.Ga gada da ruwan rafi,ga itatuwa masu ban mamaki na tsaye cik,lalle wurin al'ajabi ne.Kan fasahar zane,maizane ya yi siffar kome filla filla.surar mutum muhimmin abu ne cikin zane,ya fitar da siffar mutum sarara da launi,ta haka ana iya ganin gwanintarsa wajen yin surar mutane da tsaunuka da kuma koguna.

Tang Yin da zanensa "dawo gida kan jaki"

Tang Yin a daular Ming (1470-1523AD),wani sunansa daban Bo Hu,wani sunan daban kuwa Liuru mai bin addinin Buddha.Mutum ne da aka haife shi a gundumar Wu (Suzhou ana kiranta a yau).Ya yi kwarewa wajen yin wakoki da zane.Lokacin da ya tsufa,ya fara bin addinin Buddha,ransa ya baci a kwana a tashi.

Zanen "dawo gida kan jaki",zane ne da aka yi kan silk maras launi sosai.A cikin zanen ya yi siffofin itatuwa masu ban mamaki da gidaje dake cikin tsauni.Ruwan rafi na kwarara cikin duwatsu,itatuwa masu launin kore na karkadawa cikin iska tamkar suna rawa.Wani mutum dake bisa jaki yana kan hanyarsa ta dawowa gida,yana nufin gidansa dake cikin tsauni.Ga ruwan rafi na malala a karkashin gada a wani mutum dake dauke da itacen wuta na tafiya bisa.Maizane ya kuma rubuta wata waka a gefen cewa "na koma gida ba tare da samun kome ba.na hau jaki ina nufin gidan dake cikin tsauni.Gajiya da kura sun kama ni.Na yi farin ciki da ganin matata.Wannan zane ya shaida halayyar Tang Yin wajen yin zane.(Ali)

>>[Mutum-mutumi a Tarihi]

Mutum-mutumin sojan daular Qing

Wannan hoton mutum-mutumin sojan daular Qing da aka tono daga rami lambatuWata hanyar zuwa kabari tana da kwana.

Masu binciken kayayyakin tarihi sun kasa bayyana dalilinta.Wasu sun ce Zhu Yuanzhang ya nuna hikimarsa wato ya yi kome ba kamar saura ba.Wasu sun ce an yi haka ne domin tsawaita hanya..

Mutum-mutumi ne mai buga ganga da rewa waka na daular Donghan

Wannan hoton mutum-mutumi ne mai buga ganga da rewa waka na daular Donghan da aka tono a Chengdu da ke Sichuan.

Ma'aikatar Sichuan binciken kayayyakin tarihi na wurin ta bi hanyar zamani ciki har da amfani da satellite,aka samu bayanai sama da dubu ashiri,daga bisani aka gane inda dakin dake karkashin kasa na kabarin Xiao yake.Masana masu binciken kabarin nan sun tabbatar da cewa dakin dake karkashin kasa yana kasa da mita fiye da goma,yana cikin hali mai kyau,ba wanda ya yi satar kayayyakin dake cikinsa.

Damisoshi masu launin azurfa

Damisoshi masu launin azurfa na lokacin baya baya da kasashe masu yaki da juna ke ciki,an tone su ne daga Shenmu dake Shaanxi.

Gunki mai nuna tausayin dake da hannaye dub

Hoton Avalokitesvava, gunki mai nuna tausayin dake da hannaye dubu na daular Ming a haikali na Shuanglin a wurin Pingyao dake a Shanxi.

Bayan da aka yi bincike,nasana sun kuma gano cewa a kan gangaren da kabarin ya ke shimfidu da akwai abubuwan da mutanen suka yi har sun kai kashi sama da sittin cikin dari na gangare kamar manyan duwatsun da aka jejjera a bisa kabarin,bayan da aka yi bincike,an ce da hannaye ne masu gina kabarin suka kawo.

Dokin karfe dake tafiya bisa alallaka a guje

Dokin karfe dake tafiya bisa alallaka a guje da aka tono daga kabari na daular Donghan a Gansu

Ding da aka tono a karkarar birnin Beijing daya daga cikin kabarai 13 na sarakunan daular Ming ne,mafarin hanyar zuwa kabarin yana hagu da kabarin,ya sha banban sosai da kabarin Xiao.Bayan da aka yi bincike.

Nasana sun kuma gano cewa a kan gangaren da kabarin ya ke shimfidu da akwai abubuwan da mutanen suka yi har sun kai kashi sama da sittin cikin dari na gangare kamar manyan duwatsun da aka jejjera a bisa kabarin,bayan da aka yi bincike,an ce da hannaye ne masu gina kabarin suka kawo,suna da amfani sosai wajen kare kabarin daga ruwa da masu sata.Abin mamaki a nan shi ne duwatsun dabbobi da aka kafa a gaban kabarin Xiao duwatsu ne da ake kira "fossile" a turance masu dadadden tarihi na shekaru miliyan dari uku.

Wani injinya mai ilmin ma'adinai ya gano haka,daga baya sakamakon nan ya samu amincewa daga masana da yawa.

Kwanon yumbu mai launi

Kwanon yumbu mai launi dake da zanen raye raye na gargajiya.Wannan hoto ne na wani kwanon yumbu da aka tono a shekara ta 1973 a kauyen Sunjiazhai na gundumar Datong ta lardin Qinghai na kasar Sin.A ta cikin kwanon akwai hotuna har kashi uku na mutane dake raye raye.Yau da shekarun kimanin 5000 ke nan.

>>[Binciken Kayayyakin Tarihi]

Hanyar silik a zamanin da na kasar Sin

"Hanyar silik",tsohuwar hanyar cinikayya ce da kasar Sin ta bude kafin shekaru fiye da dubu biyu, ta shahara a duniya,gada ce da ta hada kasar Sin da kasashen Turai da Asiya da kuma Afrika,ta taka rawar gani wajen musayar kayayyaki da al'adu tsakanin gabas da yamma.

"Hanyar silik",tsohuwar hanyar cinikayya ce da ta taso daga kasar Sin ta zarce Asiya ta tsakiya zuwa Asiya ta kudu da ta yamma da kuma Turai da Afrika ta arewa a zamanin da.Ana kiran hanyar nan "hanyar silik' saboda an yi jigilar kayayyakin siliki masu yawan gaske daga kasar Sin zuwa kasashen yamma.Sakamakon binciken kayayyakin tarihi ya yi nuni da cewa an sami hanyar silik ne a daular Han ta kasar Sin a karni na daya na BC,ta "hanyar silik"ta kudu ana iya kai Afghanistan da Uzbek da Iran har da birnin Alexamder dake a kasar Massar a yanzu,wata hanyar daban ta zarce kasar Pakistan da Kabul na Afghanistan har ta kai hancin tekun Farisa,idan an nufin kudu daga birnin Kabul ana iya kai Karachi na Pakistan a yanzu,an iya kai kasar Farisa da Roma da sauran kasashen duniya ta jiragen ruwa a teku.

Daga karni na biyu na BC zuwa karni na biyu na AD,da akwai dauloli guda hudu da suka shimfidu dab da "hanyar silik" daga yamma zuwa gabas,su ne kasar Rome a Turai da kasar Parthia a Asiya ta yamma (kasar mai bin tsarin bayi na zamanin da na Farisa),da kasar Kushan a Asiya ta tsakiya (wata daula da take mallakar Asiya ta tsakiya da arewancin Indiya) da daular Han ta kasar Sin a Asiya ta gabas.Samun "hanyar silik" ya kawo dama ga al'adu na wadannan dauloli da suka iya yin mu'amala da bawa juna tasiri kai tsaye,daga bisani duk al'adu na samun cigaba ba shi kadai kawai ba a duniya.

Ta "hanyar silk"—hanyoyi tamkar gizagizo ,an sha mu'amala tsakanin Gabas da Yamma.Cikin takardun zamanin da na kasar Sin sunayen shuke shuke da aka rubuta da kalmar "Hu" tana nufin yawancinsu an samo su ne daga kasashen yamma,kamar walnut da pepper da turnip a turance.Daga karni na bakwai zuwa karni na tara na bayyanuwar Innabi Isa da kasar Sin ke cikin daular Tang,"hanyar silk" ta fi samun budin yalwa.Mu'amala tsakanin kasar Sin da kasashen yamma ta samu cigaban da ba a taba ganinsa ba a da.Tsuntsaye da dabbobi masu ban al'ajabi da lu'u-lu'u da abubuwa masu kamshi da kayan gilas da kudaden zinariya dana Azurfa na kasashen yamma da kide kide da rye raye da abinci da tufaffi daga kasashen Asiya ta yamma da ta tsakiya sun kwararo zuwa kasar Sin.A sa'I daya kuma kayayyakin da fasahohin da aka samu a kasar Sin sun malala zuwa kasashen yamma ta hanyar silk kamar su silk da aikin gona da kiwon tsuntsaye masu samar da silk da fasahar yin takarda da dabi,da kayan fenti da fadi-ka mutu da albarushi da compass,sun ba da babban taimako ga al'adun duniya.

Lokacin da aka yi musayar kayayyaki ta "hanyar silk",aka kuma yi mu'amala a fanning al'adu a tsakaninsu.Addinin Buddha daya daga cikin manyan manyan addinai uku na duniya ya shigo kasar Sin a karshen daular Xihan(206-220BC).A cikin ramin ibada da aka haka a karni na uku AD a Kezhir na jihar Xinjiang da akwai zanen dake bisa jikin bango mai fadin muraba'in mita dubu goma ya shaida yadda Addinin Buddha ya shigo kasar Sin daga Indiya a zamanin da.Bisa kimantarwa da aka yi,an ce Addinin Buddha ya isa Kezhir na jihar Xinjiang daga kasar Indiya ta "hanyar silk",daga Kezhir ya isa Dunhuang,sa'an nan ya shiga cikin kasar Sin.Ramukan ibada na Addinin Buddha da aka bari dab da "hanyar silk",mashahura cikinsu akwai ramukan ibada na Mogao dake Dunhuang,da ramukan ibada na Longmen a Luoyang,yawacinsu suna da haliyyar Gabas da ta yamma a fanning fasaha,shaida ce da ta bayyana mu'amala da aka yi tsakanin Sin da kasashen yamma a fannin al'adu,ga shi a yau sun zama kayayyakin tarihi na al'adu na duniya.

Bayan karni na tara AD,halin da nahiyoyin Turai da Asiya ke ciki wajen siyasa da tattalin arziki ya yi manyan sauye sauye,musamman bayan fasahar tafiye tafiyen jirgin ruwa a tekuna ta samu cigaba,jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa a tekuna ta taka rawar gani a cikin cinikayya,hanyar nan ta gargajiya da aka bi a kasa ta yi tabarbarewa.Kawo zuwa karni 10 AD lokacin da kasar Sin ke cikin daular Song,ba safai a kan dauki "hanyar silk" tamkar hanyar cinikayya ba.

Duk da haka,wannan tsohuwar "hanyar silk" tana da tsawo sosai kuma tana da dadadden tarihi,ta taka muhimmiyar rawa wajen samun wayin kai na duniya.A cikin shekarun baya,kungiyar UNESCO ta majalisar dinkin duniya ta kaddamar da shirin nazarin hanyar silk,ta dauki "hanyar silk" tamkar "hanyar tauna miyau" domin sa kaimi ga tattaunawa da mu'amala da ake yi tsakanin Gabas da Yamma.

Ramukan ibada dake cikin tsaunin maiji da na Longmen a Luoyang

Ramukan ibada da ke cikin tsaunin Maiji na da tsayin mita sama da 150,mai tazara kilomita 45 daga kudu maso gabacin birnin Tianshui na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin.Bisa takardar tarihi da aka rubuta,a lokacin karshe na daular Qing( wajen karni na uku BC) ne aka fara haka ramukan ibada a tsaunin Maiji an yi ta sassaka hotunan Buddha a gangare mai tsayin mita 30 da mita 70 a tsaunin nan.

(Hoto:Ramukan ibada dake cikin tsaunin maiji da na Longmen)

(Hoto:Ramukan ibada dake cikin tsaunin maiji da na Luoyang)

Wadannan ramukan ibada dake cikin tsaunin sun jeru layi bisa layi daya a kan daya,suna da kyaun gani sosai.Da akwai mutum-mutumin tabo 194 da mutum mutumin duwatsu sama da dubu bakwai da zanen dake bisa bango mai fadin muraba'in mita 1300 a ramukan da aka haka a dauloli na Beiwei da Xiwei da Beizhou da Sui da Tang da dauldoli biyar da Song da Yuan da Ming da Qing.Mutum mutumi sama dubbai tamkar ainihin mutane dake cikin ramukan ibada suna da ban sha'awa.Wasu gumakan Buddha ne dake cikin halin nitsuwa,wasu kuwa mabiyan addinin Buddha ne na karantun littattafai masu tsarki,wasu suna hira,wasu kuma suna dariya,wasu kuwa suna jinjina hannayensu,wasu kuma yara ne masu nuna biyayya da ban sha'awa.Da akwai Buddha Amituo mai tsayin mita 16 da mutum-mutumin da aka sassaka mai tsayin centimeter sama da goma,dukkansu sun yi kama da abubuwan dake akwai.Duk wadannan mutum mutumin da aka sassaka sun shaida haliyyar mutane da zamansu dake akwai,sun bayar da muhimman shaidoji ga nazarin tarihin addinin Buddha da tarihi da nazarin kayayyakin tarihi da dabi'un al'umma.Ramukan ibada dake cikin tsaunin Maiji suna cikin kyakkyawan hali sabo da suna cikin dazuzzukan dake cikin tsauni,sun kauce wa yake yake da sata.

Ramukan ibada na Longmen na lardin Henan sun shimfidu a gabbobi biyu na Kogin Yihe mai tazarar kilomita 13 daga kudu na birnin Luoyang na lardin nan,wuri ne mai kyaun gani dake da dakunan ibada da dama,wuri ne da masu yawon shakatawa da masu tsara wakoki suka so tun fil azal.An fara haka ramukan ibada na Longmen ne yayin da sarkin Xiaowen na daular Beiwei ya tsungunar da hedkwatar kasa a birnin Luoyang (wajen shekara ta 493 AD).Bayan da aka yi ta ginawa cikin shekaru sama da dari hudu.ramukan ibada dake cikin tsauni sun yi kama da shekar kudajen zuma.Da akwai ramukan ibada fiye da 2300,da mutum mutumin sama da dubu dari da rubutun kan duwatsu sama da 3600 da hasumiyar Buddha guda 40.A cikin zanen dake jikin bango,da akwai mala'iku na tafiya cikin 'yanci bisa gjimare,wasu suna rawa dauke da 'ya'yan itatuwa a hannayensu,wasu suna waka tare da kayan kide kide,wasu suna fesa ruwan sama kamar furanni,suna burge mutane sosai.

Mutum mutumi masu launi iri iri da da masu fasahar a zamanin da suka kirkiro sun kasance muhimmin kayayyaki ne na nazarin tarihi da fasahohi na zamannin da na kasar Sin.Ramin Guyang daga cikin ramukan ibada na Longmen an fara haka shi ne yayin da sarkin Xiaowen na daular Beiwei ya tsungunar da hedkwatar kasa a birnin Luoyang (wajen shekara ta 494 AD),ramin ne da aka haka tun tuni dake da abubuwa masu yawan gaske.Mutum mutumin dake cikin rami suna da kyaun gani,zane zanen dake ciki ma nada launi iri iri.Mutum mutumin suna cikin halin nitsuwa sun yi kama da mutanen da ke zama,kayayyakin tarihi ne masu daraja wajen nazarin fasahar ramukan ibada na daular Beiwei.Rubutun da ke cikin ramin da surarsu abubuwa ne masu dajara wajen nazarin rubutun kasar Sin.Wani rami mai suna Binyang,rami ne da aka fara haka shi a shekara ta 500 AD.aka kammala shi a shekara ta 523 AD,an shafe shekaru 24 ana yinsa.A cikin ramin akwai mutum mutumin Sakyamuni mai kafa addinin Buddha da mabyansa da Pusa dake sa kaya mai kyaun gani da fuskokinsu a rame suke,dukkansu sun shaida fashar daular Beiwei wajen sassaka mutum mutumin.

Kabarin Waziri Zen Houyi da Kararrawa

Bisa abin da aka rubuta cikin littattafan zamanin da,an ce masu mulki na zamanin da sun dora muhimmanci kan kide kide a kasar Sin,a ganinsu wakoki su ne suke kara wa mutane himma,ladabi shi ne dokokin biyayya ga mutane,kide kide masu dadin ji a wata kasa,alama ce da ta shaida wadatuwar kasa.Da haka ana iya banbanta mai arziki da na talauci ta hanyar kide kide.A shekara ta 1978,aka gano manyan kararrawan tagulla daga wani kabari na zamanin da a birnin Suizhou dake tsakiyar kasar Sin,kararrawan tagulla da aka gano sun jawo hankulan mutanen duniya,dalili kuwa hi ne kayayyakin da aka gano sun tabbatar da abin da aka rubuta cikin littattafan zamanin da,sun kasance sabbin shaidu ga magada da su kara fahimtarsu kan al'adu a zamantakewar al'umma na zamanin da a kasar Sin.

A watan Fabrairu na shekara ta 1978 a wurin da ake ginawa gidaje a Leigudun da ke kewayen birnin Suizhou na lardin Hubei,kwaram aka gano wani filin kasa da launin bakin bikili da ya banbanta da na sauran filayen kasa.A cikin wuri mai launin ruwan kasa aka gano alamun ayyukan dan Adam,wannan ya jawo hankalin ma'aikatar binciken kayan tarihi.Bayan da aka tono,aka gano wani kabari na zamanin da mai tsawon mita 21 daga gabas zuwa yamma mai fadin mita 16 daga kudu zuwa arewa.Da aka bude dakin kabari,aka iske guntqyen dutse manyan guda 47 da ke bisa akwatin da aka sa mamaci a ciki.Bayan da aka kawar da guntayen dutse,ba kayayyakin lu'u lu'u aka iske ba,ruwa ne mai zurfin mita uku. Sai aka ja ruwan waje da famfo.Da ruwan ya janye,sai a ga kayayyakin tarihi sun fito fili.Bayan da aka yi ta tonewa,an samu kayayyakin tarihi dubu 15 a cikin kabarin nan,daga cikinsu akwai kayan tagulla na nuna ladabi,da kayan kide kide,da makamai da kekuna da dawakan karfe da kyan zinariya da kayan lu'u lu'u da kayan fenti da kuma kayan gora.Surar kayayyakin tana da ban al'ajabi,sifoffinsu ma kamar abubuwan da ke akwai a zama,zane zanen kan kayan suna da kyaun gani,abubuwa ne masu daraja sosai.Daga cikin wadannan kayayyakin tarihi,abun da ya fi jawo hankulan mutane shi ne kararrawan tagulla guda 65.

Wadannan kararrawan da aka gano,kayan kida ne da suka fi yawa da aka gano kawo zuwa yanzu,fasahar kera su da kuma girmansu da sifoffinsu suna matsayin gaba.An kasa su gidaje takwas bisa sifoffinsu da sautinsu.Mafi tsayi shi ne centimeter 153.4,mafi karami centimeter 20.4 kawai,nauyinsu gaba daya ya kai kilogramme 2500.Kararrawa suna rataye ne a katako mai benaye uku,A jikin kararrawa da akwai rubutun kalmomi da yawansu ya zarce 2800.Bayan da aka yi jarrabawa,kararrawan na iya sama da kide kide masu dadin ji iri iri.

Bayan da aka yi nazarin littattafan tarihi,masu binciken kayayyakin tarihi sun tabbatar da cewa kabarin nan kabari ne na wazirin Zen Houyi a lokacin da kasashe masu yaki da juna ke ciki.Bisa binciken da aka yi kan kayayyakin tarihin da aka gano daga kabari ta hanyar zamani,an binne marigayi Zen Houyi ne a shekara ta dari hudu BC.

Kabarin Zen Houyi yana karkashin ruwa a kasa,daga baya ruwan ya cinye kabarin,shi ya sa kayayyakin da aka sa a cikin kabarin a ruwa suke,kayayyakin da ke ciki ba su lalace ba kuma ba wanda ya saci kayan saboda ruwa.

Bayan da aka tono kabarin Zen Houyi,gwamnatin wuri ta kafa wani dakin musamman na nuna kayayyakin da aka tono daga kabari,aka yi kwaikwayon "wurin kabarin Zen Houyi" da kafa dakin nuna kararrawa,an kuma shirya kungiyar makida dake amfani da irin wadannan kararrawa ta yadda mutane na zamanin yau na iya saurari kide kide na zamanin can da.

Kangon Yin da rubutun kan katantanwa

Kasar Sin tana cikin halin wayin kai na tsawon shekaru dubbai,shi ya sa da akwai kayayyakin tarihi masu yawan gaske a karkashin kasa.Tun bayan da fasahar zamani ta binciken kayayyakin tarihi ta shigo kasar Sin daga kasashen yamma a karni na 20,aka gano wurare da kayayyaki da yawa na tarihi a kasar Sin.

Kango mai fadin muraba'in kilomita 24 da aka gano a birnin Anyang na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin,kango ne na Yin da ya shahara a duniya.Bisa abin da aka rubuta cikin tarihi,an ce a karni na 14 BC,Sarki Pangen na daular Shang ya kaurar da hedkwatar kasa daga Qufu na Shandong zuwa wannan wuri,daga nan cikin shekaru kimanin dari uku na baya,wurin nan cibiya ce ta siyasa da al'adu da kuma tattalin arziki ta daular Shang.A shekara ta 1046 BC,sarkin Wuwang na daular Zhou ya lashe sarkin karshe na daular Shang sarkin Zhou,daga nan daular Shang ta hallaka,wurin nan ya zama kango.Ana kiransa Kangan Yin saboda daular Shang tana da wata sunan daban Yin.

(Hoto: Kangon Yin)

Abubuwan da aka gano a Kangan Yin,abubuwa ne mafi muhimmancin da aka gano a karni na 20 a kasar Sin.A shekara ta 1928,karo na farko ne da aka gano abubuwan tarihi masu yawan gaske ciki har da rubutun kan katantanwa da kayan tagulla.Daga cikinsu rubutun kan katantanwa da aka gano,muhimmin batun duniya ne wajen binciken abubuwan tarihi.

(Hoto :Rubutun kan katantanwa)

Rubutun katantanwa rubutu ne na zamanin da da aka yi bisa jikin kunkuru da kasusuwan dabbobi.A daular Shang kafin ya yi kome Sarki ya kan kada kuri'a.katantanwa kayan wasa ne da sarki ke amfani da su wajen kada kuri'a.

Kafin a yi amfani da su,kamata ya yi a goge katantanwa da kasussuka,an cire jinni da nama dake cikinsu,sa'an nan aka sassaka a jikin katantanwa da kasussuka.Bokaye ko masu shirya wasan kada kuri'a su kan rubuta sunayensu da ranar yin wasa da kuma tambayoyin da suke neman amsa a bisa.daga baya a kan gasa su da wuta, a kan samu alamu a jikin kasussuwa sabo da zafin wuta.Daga wadannan alamu aka sami sakamakon kada kuri'a.Bayan da aka dudduba sakamakon kada kuri'a,aka tanadi wadannan kasusuwan cikin dakin ajiye kayayyain gwamnati.

Kawo yanzu an tono katantanwa da kasussuwa sama da dubu 160 a kangan Yin.Wasunsu da akwai rubutu cikakku wasu babu.Bisa kididdigar da aka yi,an ce da akwai kalmomi kimanin dubu hudu a jikin wadannan katantanwa da kasussuka,daga cikinsu masana ilmin kayayyakin tarihi suka yi nazarin kalmomi kimanin fiye da dubu uku,masana sun iya yin bayanai kan kalmomi sama da dubu.sauran kuwa ba a iya gane su ba tukuna ko kuwa ra'ayoyin masana sun banbanta sosai kan su.Dayake an gane ma'anar kalmomi sama da dubu,ana iya gane halin da daular Shang ke ciki wajen siyasa da tattalin arziki da kuma al'adu na wancan zamanin da.

Littafin musamman da aka rubuta kan nazarin rubutun kan kasussuwa littafi ne mai suna "Tieyun canggui" da mallam Liu E ya rubuta an buga shi a shekara ta 1913.Littafin da mashahurin masanin tarihi kuma da adabi Guo Moruo ya rubuta kan nazarin rubutun bisa kasussuwa an buga shi ne a shekara ta 1929,wani muhimmin littafi ne.Masana masu kwarjini wajen nazarin rubutun kasussuwa a kasar Sin a yanzu sun hada ne da shehun mallami Qiu Xigui dake aiki a jami'ar Beijing da shehun mallami Li Xueqing dake aiki a cibiyar nazarin tarihin kasar Sin.

Ban da rubutun kasussuwa na daular Shang da aka gano a kangan Yin,an kuma gano rubutun kasussuka na daular Xizhou da ya fi dadewa shekarun baya,babu kalmomi da yawa a bisa,saboda ba su da muhimmanci a wannan daula.A cikin shekaru fiye da 70 da suka gabata,an gano wuraren gidajen sarakuna sama da 50 da kabaransu 12 da sauran kabarai dubbai,da ramukan addu'a kimanin dubu da wuraren ayyukan hannu fiye da 30 da sauran kayayyaki na tagulla da lu'u lu'u da tangaram da kasussuwa da dama,ta haka ana iya ganin halin da kasar Sin ke ciki tun fil azal.

Binciken kayayyakin tarihi a kabarin sarkin daular Xixia

Binciken kayayyakin tarihi a kabarin sarkin daular Xixia a jihar kabilar Hui mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta Ningxia da ke arewa maso yammacin kasar Sin wani muhimmin bincike ne da aka yi kan batutuwa dari na tarihi a karni na 20 a kasar Sin,yana da muhimmancin gaske cikin tarihin nazarin kayayyakin tarihi na kanana kabilu a kasar Sin.

Kafin shekaru 770 da suka wuce da akwai dauloli uku a kasar Sin.Daya daga cikinsu kabilar Han ke mulki ana kiranta daular Song a tsakiyar kasar Sin a yanzu,dayan kuwa daular Liao da kabilar Nuzhen ke mallaka a arewa maso gabashin kasar Sin,wata daban ita ce daular Xixia da kabilar Dangxiang ke mallaka a arewa maso yammacin kasar Sin.

Xixia wata mulukiyar kasaa ce mai yanci,tana da nata harshe da rubutu.Abin bakin ciki shi ne a shekara ta 1227,rundunar sojan sarki Chengjisihan ta Mongoliya ta hallaka daular Xixia,ta yi wa mutanen Dangxiang kisan kyashi,shi ya sa littattafan daular Xixia sun bace,kawo yanzu ba a san halin da wannan daular ke ciki ba.

A farkon shekaru 70 na karnin da ya gabata aka gano wurin kabarin sarkin daular Xixia,daga baya cikin shekaru 30,masana ilmin kayayyakin tarihi na kasar Sin sun yi ta yin bincike da nazari kan kabarin sarkin daular Xixia,daga baya aka gano shirye-shiryen kabarai na daular Xixia.

Kaburburan sarakunan daular Xixia suna nan ne a hamada mai fadin muraba'in kilomita hamsin,da akwai filayen musamman tara da aka kebe domin kaburburan sarakunan kasa da sauran kaburbura na manyan jami'ai da na masu arziki,wuri ne mafi fadi a kasar Sin da aka tanadi kaburburan sarakunan kasa,fadinsa ya kai na kaburbura 13 na sarakunan kasa na daular Ming dake a birnin Beijing.A kowane filin kabarin sarkin kasa da akwai dakuna masu kyaun gani.

Filin kabari na uku fili ne mafi fadi daga cikin filaye tara da aka kebe domin sarakunan kasa.Masana ilmin binciken tarihi sun tabbatar da cewa kabari ne na Li Yuanhao,sarki na farko da ya kafa daular Xixia.Daga nan aka mayar da hankali kan binciken filin kabari na uku.

Hasumiya da ke cikin filayen kaburburan an dauke su tamkar "kabarin kasar Massar a gabas",hasumiya ta kan tsaya a kuriyar filin ta arewa maso yamma.tana sashen baya na kabari,hasumiya ce mai kusurwoyi takwas mai benaye da dama,da kasa aka gina ta,mafi fadinta ya kai mita 34,daga gindinta akwai benaye bakwai ko biyar.Hasumiya gine gine na musamman da aka gano filayen kaburburan daular Xixia ba a taba ganin irinsu ba a sauran wuraren kaburburan kasar Sin,sun shaida irin halayyar musamman na masu arziki na daular Xixia wajen binne mamaci.

A ran 30 ga watan Afrilu na shekara ta 2000 ne,aka gano wani abu mai fuskar mutum kums mai jikin tsuntsu a kuriyar arewa maso gabashin filin kabari na uku yayin da ake bincike.Masana sun tabbatar da cewa "mutumin tsuntsu"ne da aka rubuta a cikin littafin addinin Buddha.wani tsuntsu ne a duwatsun Himalaya,tsuntsu ne a duniyar matattu a cikin addinin Buddha,abin ado ne a jikin gine gine na addinin Buddha.

Kawo yanzu an tono kayayyakin gine gine dubu 140 da abubuwan ado metan a filayen kaburburan sarakunan daular Xixia.A ganin masana,kaburburan sarakunan daular Xixia suna da halayen musamman na sarakunan kabilar Han a tarihi na kasar Sin,sa'I daya kuma suna da tasiri sosai daga gine gine na addinin Buddha,sun hada al'adun kabilar Han da na addinin Buddha da na kabilar Dangxiang gu daya,sun zama wani salon musamman a cikin gine ginen dake cikin filayen kaburburan kasar Sin,suna da muhimmanci a tarihi.

Kayayyakin tarihi da yawa da aka gano a kaburburan daular Xixia suna tattare da al'adu da abubuwa masu daraja na wannan daula,sim shaida halayen musamman na tarihi da na al'adu na daular Xixia,sun kasance babban ma'ajin kayayyakin tarihi na al'adu na daular Xixia a tarihin kasar Sin.

Binciken kayayyakin tarihi a haikalin Famen a lardin Shaanxi na kasar Sin

Haikalin Famen a gundumar Fufeng ta lardin Shaanxi na kasar Sin,haikali ne da ya fi shahara saboda an tanadi hakorin Sakyamuni wanda shi ne ya kafa addinin Buddha a duniya.A watan Afrilu na shekara ta 1987 ne aka gano wani dakin dake karkashin kasa ba zata yayin da masana binciken kayayyakin tarihi ke cikin shirin kafa sabon haikali,abubuwa masu daraja na tarihi da aka ajiye a dakin dake karkashin kasa sun girgiza duniya,muhimman abubuwa ne da aka gano bayan da aka gano ramukan binne mutum mutumin sojoji da dawaki na daular Qing a lardin Shaaxi.

Haikalin Famen yana cikin gundumar Fufeng mai tazarar kilomita 120 daga yammacin birnin Xi'an,an fara gina shi ne a kimanin shekara ta 499 AD da kasar Sin ke cikin daular Beiwei.Lokacin budin yalwa na haikalin Famen shi ne karni na bakwai AD da kasar Sin take cikin daular Tang.Gwamnatin daular Tang ta kashe mankuda kudade da amfani da leburori masu yawa wajen fadada haikalin,daga baya aka sami wani haikali mafi girma a yankin hedkwatar kasa da farfajiya guda 24 da masu zaman zuhudu sama da dubu biyar a cikinsu.

Bisa abin da aka rubuta cikin littattfai masu daraja na addinin Buddha,an ce sarki Ayu na kasar Tianzhu (Indiya) ya barbaza hakora da kasusuwan Sakyamuni da ya kirkiro addinin Buddha duk domin yadada addinin Buddha aka gina hasumiyoyi dubu 84 a duniya,daga cikinsu goma sha tara suna cikin kasar Sin,haikalin Famen yana daya daga cikinsu.

Haikalin Famen ya shahara saboda a karkashin hasumiya dake cikin fajiyarsa akwai kasusuwan Sakyamuni,mutane su kan taru daga kowane lungun kasa domin nuna girmamawa.Bisa abin da aka rubuta a cikin littattafan tarihi,an ce da akwai sarakuna guda takwas na daular Tang sun sha yin maraba da zuwan kasusuwan Sakyamuni a gidan sarauta domin nuna girmamawa,sun kuma bayar da kyaututtuka na abubuwa masu daraja da yawa,aka ajiye su a cikin dakin dake karkashin hasumiya.Ba a sake ganin hali mai armashi a haikalin Famen ba saboda yake yake da girgizar kasa da sauransu.

A shekara ta 1981,Pagoda mai tarihin shekaru darurruwa ya wargaza saboda ruwan sama.A shekara ta 1987,gwamnatin lardin Shaaxi ta shirya wata kungiyar binciken kayayyakin tarihi zuwa haikalin Famen,ta haka kuwa aka bude dakin daular Tang dake karkashin kasa na tsawon shekaru 1113.

Dakin dake karkashin kasa a Famen tsawonsa ya kai mita 21.4,fadinsa muraba'in mita 31.48 ya hada da daki na gaba da tsakiya da na baya da hanyoyi.An tanadi kayayyakin tarihi masu daraja da yawa a ciki,wasu kasusuwan Sakyamuni ne,wasu kuwa kayayyaki ne na zinariya da azurfa da lu'u lu'u da tangaram da silk,yawansu ya kai wajen dari tara.Musamman kasussuwan Sakyamuni da aka gano,muhimmin abu ne da aka gano bayan da aka gano mutum mutumin sojoji da dawaki na daular Qing,kuma babban batu ne na duniyar mabiyan addinin Buddha na gida da na waje da kuma tarihin al'adu na duniya.

Ban da kasusuwa masu daraja da aka gano,an kuma gano kayan siliki a dakin dake karkashin kasa na Famen,wuri ne da aka gano silk mafi girma da yawa da daraja na daular Tang bayan ramin ajiye littattafan addini a Dunhuang na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin,sai a ce shi ne wurin ma'ajin kayan silk na daular Tang a kasar Sin.Bisa abin da aka rubuta a cikin takardun tarihi,an ce fasahar yin kayan silki da aka tanada a dakin karkashin kasa a Famen ta fi nagarta,zaren zinariyar da aka yi amfani da shi wajen dinke tufafi bai kai girman gashin mutum ba.A akwaitin ajiye kayan silk da ke cikin dakin karkashin kasa,tsayinsa bai kai centimeter 23,kayan silk da aka ajiye a ciki sun kai 780.

An gano kayayyakin zinariya da azurfa da na liuli masu launin walkiya darurruwa a cikin dakin dake karkashin kasa na Famen,daga cikinsu kayayyaki 16 sun fi burge masana nazarin kayan tangaram na kasar Sin saboda launinsa.Wannan launi ne na sirri da aka yi amfani da shi a fadar sarakuna na daular Tang,fasahar yinsa ta bace,an tabo shi a cikin littafin tarihin kasar Sin,ba wanda ya ga shi a baya.Bisa abin da aka rubuta a cikin tarihi,an ce kwano mai launin nan tamkar kwanon dake dauke da ruwa a ciki yana walkiya babu kura ko kadan.

Gwamnatin wurin ta kafa wani dakin ajiye kayayyaki masu daraja da aka gano a dakin dake karkashin kasa a Famen domin kare su da kuma gwada su ga maziyararta.Masanan kare kayayyakin tarihi na kasar Sin sun hada kansu da takwarorinsu na kasar Jamus sun yi wa kayan siliki da aka tono daga dakin dake karkashin kasa kariya ta hanyar zamani na kimiyya.A shekara ta 2002 aka kai kasusuwan Sakyamuni mai kafa addinin Buddha zuwa yankin Taiwan na kasar Sin domin nuna girmamawa,a cikin wata daya da 'yan kai,mutane kimanin miliyan hudu sun kai ziyarar ban girma ga kasusuwan Sakyamuni mai kafa addinin Buddha.

Binciken kayayyakin tarihi a Shanxingdui

Kasar Sin kasa ce mafi fadi a duniya.A zamanin da da akwai kananan kasashe da dama na kabilu da aka kasance a wannan kasa.Lardin Sichuan na yanzu wuri ne da kasar Shu ta zamanin da ke kasancewa.Kayayyakin tarihi da aka gano a Shanxingdui a shekaru saba'in na karnin da ya gabata sun girgiza duniya.

Wurin tarihi na Shanxingdui yana cikin yankin da birnin Guanghan ke mallaka a lardin Sichuan,yana da tarihi na tsakanin shekaru dubu biyar da dubu uku.A yanayin bazara na shekara ta 1929,wani manomin dake aiki a gonarsa ya gano wani lu'u lu'u mai kyaun gani wanda ya ke da halayyar kasar Shu a zamanin da,shi ya sa ya jawo hankulan mutane,daga baya an gano kayayyakin tarihi na tarihin shekaru dubu uku.A shekara ta 1986 ne masana binciken kayayyakin tarihi suka tono manyan ramuka guda biyu da aka yi amfani da su wajen nuna girmamawa ga matattu,an gano kayayyakin tarihi masu daraja da ba a taba ganin irinsu ba sama da dubu,wannan ya girgiza duniya,aka kuma tono abubuwan tarihi masu daraja daga nan,tambayoyin tarihi ma na biyo.

Wani abin ban mamaki daga cikin kayayyakin tarihi da aka gano a Shanxingdui shi ne abubuwan rufe fuska na tagulla da dama da aka samu.Kafin wannan an gano kyakkyawan kayan tagulla da yawa a yankin Henan dake tsakiyar kasar Sin ciki har da tukwane da kwano,duk da haka babu abin rufe fuska na tagulla.Abubuwan rufe fuskokin daaka gano a Shanxingdui,kusan dukkansu na da babbar gira da ido da hanci da baki,kusan babu mukamuki,wasu suna murmushi,wasu na fushi ba fushi sosai ba.Bayan da aka dudduba wadannan abubuwan sosai aka gano wani karami rami a kunne.Fuskokinsu sun sha banban da na mutane na zamanin nan.Mene ne suke wakilta? Har yanzu masana ba su sami amsa ba bayan da suka yi tunani mai zurfi.

Wani mutum-mutumi dogo da siriri da aka gano a Shanxingdui,fuskarsa ta yi kama abin rufe fuska,yana saye da babbar riga,babu takalma,yana tsayawa kan wani dandali.Tsawonsa ya kai centimeters 170,mutum-mutumin ne mafi tsawo na tagulla da aka gano a duniya.Hannunsa daya na sama,dayan kuwa na kasa,kamar yana rike da wani abu.Da aka tono shi,ba kome a hannayensa.Masana sun yi kimanta cewa idan hannunsa na rike da wani abu,mutum-mutumin zai iya fadi.Masana sun ce shi boko ne da ya sha banban da sauran mutane,ya kan fito a bikin ta'azziya.

Ban da abubuwan rufe fuskoki da mutum-mutumin da aka gano,an kuma gana sandar zinariya da itace tagulla da hauren giwa.Tsawon sandar zinariya ya kai mita 1.42,akwai zane zane a jikinsa,a cikin zane zanen akwai sifoffin tsuntsaye biyu da kifaye biyu,bisa kan kifaye da wuyan tsuntsaye da akwai hoton kibiya da hoton mutum mai dariya.Itacen tagulla ya ba mu mamaki.Tsayinsa ya kai mita hudu,yana da rassa tara,bisa kowane reshe akwai wani tsuntsu da ya tsaya cik.Bisa nazarin da aka yi,an ce wannan tsuntsu ba irin tsuntsu da mu kan gani ba ne yau da kullum wani tsuntsu ne na mala'ika da yake wakiltar rana.

Bayan da masana suka yi nazari suka gano ba ma kawai akwai alamun al'adun kasar Shu ta zamanin da ba har ma da akwai alamun al'adu na Asiya ta yamma da sauran nahihoyi daga cikin kayayyakin tagulla da aka gano a Shanxingdui,musamman mutum-mutumin tagulla da sandar zinariya da sauran abubuwa dukkansu sun yi kama da kayan al'adu na Maya da Massar wadanda suka fi shahara a duniya.wadannan kayayyakin tagulla da aka gano a Shanxingdui sun sha banban da irinsu da aka gano a tsakiyar kasar Sin.Daga hauren giwa saba'in da aka gano,an ce akwai ciniki tsakanin kasar Shu da sauran kasashen kewayenta da kuma kasashen dake nesa da ita.Daga siffar finjalin giya da aka gano ta yi kama da na kasashen Turai a wancan lokaci,kayan tagulla na Shanxingdui za su yiwu su samu tasiri daga Asiya ta yamma da na Gabas na kusa da Turai.Kayayyakin tarihi da aka gano a Shanxingdui sun cika gibin dake akwai a fannonin binciken kayayyakin tarihi da ilmin aesthetics da tarihi na kasar Sin.

Binciken kabarin kakanin-kakanin sarkunan daular Ming

Daga cikin kaburburan sarakunan kasar Sin a zamanin can da,kaburburan sarakunan daular Ming (Daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644 AD) sun fi zama cikakku.Daga cikinsu kabarin kakanin-kakanin sarakuna na daular Ming ya fi kasaita,kabari na farko ne da sarki na farko na daular Ming Zhu Yuanzhang ya kafa domin kakanin-kakaninsa.Zhu Yuanzhang yana kan kujerar sarki daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1398,sarki ne mai ban mamaki a tarihin kasar Sin.An haife shi a gidan matalaucin manomi.ya taba zama a wani haikali domin samun zama.Daga baya ya shiga boren manoma mai adawa da daular Yuan (Daga shekara ta 1271 zuwa shekara ta 1368 AD),saboda bajinta da dabarun yake da su a cikin yake yake ya zama jagorar 'yan bore manoma daga wani manomi.A shekara ta 1368,Zhu Yuanzhang ya nada kansa sarki kuma ya hada kasar Sin baki daya.

Bayan da ya zama sarki,Zhu Yuanzhang ya gina kabarin da aka binne tufaffi da huluna na kakanin-kakaninsa domin tunawa da su,gawar kakansa ma na cikin wannan kabari.

Kabarin kakanin-kakanin sarakunan daular Ming yana cikin tsohon garin Sizhou dake cikin gundumar Xuyi a gabacin kasar Sin.yana gabar gabas na tafkin Hongze,daya daga cikin manyan tafkoki marasa ruwan gishiri a kasar Sin.An shafe shekaru 28 wajen gina kabarin .Bisa abin da aka rubuta cikin tarihi,an ce da akwai ganuwa guda uku dake kewayen kabarin da gadaje masu launin zinariya uku manyan dakuna iri iri sama da dubu,lalle sun fi kasaita da girma.Har wa yau dai wata hanya mai tsawon mita 250 dake tsakiyar filin kabarin ta shimfidu daga kudu zuwa arewa,wato daga kofar filin kabari zuwa kofar kabarin—inda aka binne kakan sarkin Zhu Yuanzhang.an kafa duwatsun dabbobi 42 a gefuna biyu na wannan hanya.Kowanensu yana da nauyi sosai da girma.

(Hoto: Kabarin kakanin-kakanin sarkunan daular Ming)

Tatsuniya wajen gano kabarin nan ta ce a shekara ta 1680,kabarin kakanin-kakanin sarakunan daular Ming ya nutsa cikin ruwa saboda wata ambaliya,daga nan kabarin ya kasance "kabarin da ke karkashin ruwa." Har zuwa shekara ta 1963,aka yi fari mai tsanani a wurin ruwan tafkin Hongze na ja da baya,kabarin kakanin-kakanin sarakunan daular Ming ya bullo,ana iya ganin wasu duwatsun dabbobi da mutum-mutumin waziri da janar-janar da fadawa.kowanensu tsayinsa ya wuce mita uku da nauyin TON goma.Dakunan da ke bisa kabarin sun rushe.Bayan da masana suka yi bincike,an ce kayayyakin da aka binne cikin kabarin suna cikin hali mai kyau.

Har zuwa yanzu dakin dake cikin kabarin yana cikin kududdufi.Ana iya ganin kofar dutse na kabarin.Abin mamaki shi ne da wuya a janye ruwan dake cikin kududdufi gaba daya.A ganin masana,kududdufi ya katse iska da dakin kabari,shi ya sa kayayyakin daka binne ciki dakin kabarin suna cikin hali mai kyau.

Bayan da aka yi fari a yankin tafkin Hongze a shekara ta 1963,an kuma yi fari mai tsananni a shekara ta 1993 da shekara ta 2001,musamman farin da aka yi a shekara ta 2001,shi ya sa ganuwar waje mai tsawo mita 1178 dake kewayen kabarin kakanin-kakanin sarakunan daular Ming,sashe mafi tsayi da ya bayyanu saboda farin.Tsohon garin Sizhou da kabarin kakanin-kakanin sarakunan daular Ming ke zaune,wuri mai wadata ne a zamanin da.Da aka yi fari a shekara ta 1963tsohuwar ganuwa da gindin wasu gine ginen sun fito fili.Daga nan ana iya ganin girmansa da wadatuwarsa. Ambaliyar ruwa ba ta cinye garin nan ba sai tabo ne ya rufe shi daga baya.Da haka wasu masana suna masu ra'ayin cewa idan tsohon garin Sizhou ya bullo,da sauki za a iya mayar da shi.An binne garin Pompei na kasar Italiya ne saboda amon wutar dutse,daga baya aka tono shi har ya girgiza duniya.A ganin masana,kamar Pompei yake tsohon garin Sizhou, "garin Pompei ne na kasar Sin".

Binciken Kabarin sarkin Xiao na daular Ming

Kabarin Xiao,kabari ne na Zhu Yuanzhang shi kansa wanda ya kafa daular Ming (Daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644 AD),kabari ne da ya fi kasaita daga cikin kaburburan sarakuna na duniya.

Zhu Yuanzhang (yana kan kujerar mulki daga shekara ta 1368 zuwa 1398 AD),sarki ne mai ban mamaki a tarihin kasar Sin.An haife shi ne a wani gidan matalaucin manomi.Ya taba yin zaman zuhudu wato gudun duniya a haikali domin samun zama.Daga baya ya shiga boren manoma mai yin adawa da daular Yuan(Daga shekara ta 1271 zuwa shekara ta 1368),har ya zama jagorar masu bore daga wani manomi saboda bajinta da dabaru da ya nuna a cikin yake yake.A shekara ta 1368,ya zama sarki,kuma ya hada kasar Sin baki daya.

Lokacin da yake kan kujerar mulki,Zhu Yuanzhang ya fara gina kabarinsa,ya shafe shekaru 25 wajen gina shi,ya kammala aikin gina kabarinsa ne yayin da dansa ya hau kujerar mulkin kasa,kabarin Xiao yana karkarar birnin Nanjing saboda ya kafa hedkwatar kasa a Nanjing (daga baya dansa ya kaurar da hedkwatar kasa daga birnin Nanjin zuwa birnin Beijing).Kabarin nan na daular Ming daya kawai yana birnin Nanjing,sauran kabaran sarakuna 15 suna karkarar birnin Beijing.Bisa abin da aka rubuta,an ce tsawon ganuwar dake kewayen kabarin Xiao ya kai kilomita 22.5,watau ya kai kashi biyu cikin kashi uku na ganuwar birnin Nanjing a wannan lokaci.Bayan shekaru dari shida,dukkan dakunan da ke filin kabarin Xiao sun rushe saboda yanayi da yake yake,daga abubuwan da aka bari a wurin,ana iya gane shirye-shiryen da aka tsara wajen gina kabarin nan.Kabarin nan ya yi kama da sauran kaburbura na daular Ming bisa shirye-shirye da fasali,ya fi su girma,lalle kaburburan sauran sarakunan daular Ming suna bin sawunsa.Shirye-shiryen kabarin Xiao ya sha banban da na sarakuna na sauran dauloli a tarihin kasar Sin.Wata hanyar zuwa kabari tana da kwana.Masu binciken kayayyakin tarihi sun kasa bayyana dalilinta.Wasu sun ce Zhu Yuanzhang ya nuna hikimarsa wato ya yi kome ba kamar saura ba.Wasu sun ce an yi haka ne domin tsawaita hanya.

Hanyar zuwa kabarin Xiao ta fara ne daga Sifangting inda aka kafa wani dakin dake da wani dutsen tunawa a ciki.Rufin dakin nan ya rushe,bangunan suna nan.A jikin dutsen aka sassaka kalamomin da dan Zhu Yuanzhang ya rubuta wadanda suka bayyana babban taimakon da ya bayar,yawan kalamomin sun kai 2746.A gefuna biyu na hanyar an kafa duwatsun zaki da rakuma da giwaye da dawaki 12 da kuma mutum-mutumin wazirai da fadawa 8,suna da girma sosai,duwatsun sassaka ne masu daraja na daular Ming.

Wurin da ya gagara fahimta a kabarin Xiao na daular Ming shi ne dakin dake karkashin kasa inda aka ajiye gawawakin sarkin Zhu Yuanzhag da matansa biyu.Wata ganuwa mai tsawon mita fiye da 1100 tana kewayan kabarin,da'irar da ya kai mita dari hudu.wani daki mai daraja yana tsayawa bisa kabarin,tsayinsa ya kai mita 129 daga leburin teku.Har yanzu ba a san inda dakin dake karkashin kasa yake ba,akwai ra'ayoyi daban daban kan batun nan.Wata tatsuniya ta ce yayin da aka binne gawar Zhu Yuanzhang,da akwai kungiyoyi 13 suka fito daga kofofi 13 na ganuwar birnin,siffarsu kusan daya ne domin kada a gane wace kungiyar ke dauke da ajiye gawarsa.Wasu sun ce ba a binne gawarsa a karkarar Nanjing ba,an binne shi ne a karkarar birnin Beijing batun nan ya zama wata tambaya da ba a san amsa ba.Tun daga shekara ta 1997,ma'aikatar binciken kayayyakin tarihi na wurin ta bi hanyar zamani ciki har da amfani da satellite,aka samu bayanai sama da dubu ashiri,daga bisani aka gane inda dakin dake karkashin kasa na kabarin Xiao yake.Masana masu binciken kabarin nan sun tabbatar da cewa dakin dake karkashin kasa yana kasa da mita fiye da goma,yana cikin hali mai kyau,ba wanda ya yi satar kayayyakin dake cikinsa.

(Hoto: Kabarin sarkin Xiao na daular Ming)

(Hoto: Mutum-mutumin da ke Kabarin sarkin Xiao na daular Ming)

Kabarin Xiao na daular Ming ya sha banban da na sauran dauloli a fannoni da yawa.An gano hanyar zuwa kabari tana da kwana kuma tana waje da tsakiya bayan da aka yi bincike.Me ya sa haka.Babu wanda ya san dalili.Duk da haka fasalin gine ginen filin kabarin ya kawo tasiri ga wuraren kabaran sarakunan daga baya.Alal misali kabarin Ding da aka tono a karkarar birnin Beijing daya daga cikin kabarai 13 na sarakunan daular Ming ne,mafarin hanyar zuwa kabarin yana hagu da kabarin,ya sha banban sosai da kabarin Xiao.Bayan da aka yi bincike,nasana sun kuma gano cewa a kan gangaren da kabarin ya ke shimfidu da akwai abubuwan da mutanen suka yi har sun kai kashi sama da sittin cikin dari na gangare kamar manyan duwatsun da aka jejjera a bisa kabarin,bayan da aka yi bincike,an ce da hannaye ne masu gina kabarin suka kawo,suna da amfani sosai wajen kare kabarin daga ruwa da masu sata.Abin mamaki a nan shi ne duwatsun dabbobi da aka kafa a gaban kabarin Xiao duwatsu ne da ake kira "fossile" a turance masu dadadden tarihi na shekaru miliyan dari uku.wani injinya mai ilmin ma'adinai ya gano haka,daga baya sakamakon nan ya samu amincewa daga masana da yawa.Wannan injiniya ya iske abubuwan da aka samu a teku a jikin duwatsun dabbobi tare da madubi mai kara girman abu.Shi ya sa duwatsun dabbobin da aka kafa gaban kabarin Xiao suna da daraja a tarihi da fasaha har da kimiyya.

A watan Yuni na shekara ta 2005,an yi taro dangane da wuraren tarihi na halittu da al'adu na duniya a birnin Suzhou na kasar Sin inda za a tattauna ko a mai da kabarin Xiao na daular Ming wurin tarihi na al'adun duniya.Batun nan zai jawo hankulan mutane a lokacin nan.

Binciken kabaran sarakuna 13 na daular Ming

Samun kaburburan sarakuna 13 na daular Ming ya shafi wani juyin mulki.Zhu Yuanzheng shi ne sarki na farko da ya kafa daular Ming,ya tsungunar da hedkwatar kasa a Nanjing a kudu maso gabacin kasar Sin.Bayan rasuwarsa aka mika kujerar mulkin kasa zuwa ga jikarsa,Zhu Li,da na hudu na Zhu Yuanzhang ya ta da yakin basasa domin neman kwace kujerar mulki,daga baya burinsa ya cika.Bayan da aka murkushe Nanjing,ba a san jikar Zhu Yuanzhang ba har yanzu dai tambaya ce da babu amsa a cikin tarihin kasar Sin.Bayan da Zhu Li ya hau kujerar mulki ya kaurar da hedkwatar kasa daga Nanjing zuwa Beijing domin samun tsaro.A duk lokacin da Zhu Li ke kan kujerar mulki,ya tura mutanensa don su zabi wurin da za a tona kabarinsa.Bayan da aka yi tattaunawa sosai sai aka zabi wani wuri mai kyaun gani da saukin kariya a arewa maso yammacin birnin Beijing da ya zama kabarinsa aka nada masa sunan Kabarin Chang.A cikin shekaru sama da metan daga shekara ta 1409 AD da aka fara gina kabari har zuwa shekara ta 1644 AD da aka hallaka daular Ming,aka binne gawawakin sarakuna 13 a nan aka samu kabaran sarakuna 13 na daular Ming.

Fasalin kabaran sarakuna 13 ya yi daidai da na kabarin Xiao na daular Ming.Da akwai wata hanyar dake tsakiya yankin kabarin domin nuna girman sarkin kasa.Wata kofa da ke gaban kabarin wata babbar kofa ce ta duwatsu mai tarihin shekaru fiye da 450.A jikin duwatsu akwai zane zane.Daga nan babu nisa sai ka gamu da wata kofar kabaran wata kofar Dagun,kofa ce da dukkan sarakuna suka ketare idan sun kai ziyarar ban girma ga kakanin-kakaninsu.Daga nan wata ganuwa mai tsawon kilomita 40 da ta kewaya kabaran,akwai kofofi goma a jikin ganuwar da sojoji ke gadi domin kare kaburbura.A wurin kaburburan akwai hakimai masu sa ido da manoma masu noman kayan lambu da kuma dogarai masu kare kaburburan.

(Hoto: Hanyar kabaran sarakuna 13 na daular Ming )

Sarakuna su kan kirkiro tatsuniyoyi da dama domin kare kaburburansu cikin dogon lokaci haka kuma sun buya kabaransu sosai.shi ya sa inda dakin dake karkashin kasa na kabarin ya ke,ya zama sirri .Kabarin Ding da aka tono shi a watan Mayu a shekara ta 1955.kabarin ne da ba a san inda dakin dake karkashin kasa na kabarin ya ke ba.Da aka tono,an iske dakin nan yana da sassa biyar watau sashe na gaba da tsakiya da baya da na hagu da dama,da duwatsu ne aka gina shi. A sashen tsakiya akwai akwatunan ajiye gawawwaki,wanda ya fi girma a tsakiya,akwatin ne da aka ajiye gawar sarki Zhu Yujun,sauran kuwa inda aka ajiye gawawwakin matansa biyu.Kewayensu da akwai akwatunan da ke dauke da lu'u lu'u da kayan tangaram.Daga baya,aka tono abubuwan tarihi masu daraja sama da dubu uku.Daga cikinsu akwai kayan silki masu launi da tufafi da kayan ado na zinariya da sauran kayan zinariya da lu'u lu'u da tangaram.dukkansu kayayyakin fasaha ne daular Ming.

(Hoto: Kayayyakin kabaran sarakuna 13 na daular Ming )

Kabari na daular Han a Mancheng da rigar lu'u lu'u

A lokacin daular Han ta yamma (Daga shekra ta 206 BC zuwa shekara ta 8 AD) a tarihin kasar Sin,ana tsammanin cewa lu'u lu'u na iya kare gawar mutum daga rubewa,shi ya sa sarakuna da masu arziki su kan sa rigar lu'u lu'u bayan mutuwarsu.Rigar lu'u lu'u ana dinke lu'u lu'u da zaren zinariya.A shekara ta 1968 a karo na farko ne masana ilmin kayayyakin tarhi suka gano wata rigar lu'u lu'u mai daraja a gundumar Mancheng na lardin Hebei na kasar Sin.

Kabarin daular Han na Mancheng yana gundumar Mancheng na lardin Hebei mai tazara fiye da kilomita metan daga birnin Beijing.Kabari ne na sarki Liu Sheng da matarsa Dou Wan na kasar Zhongshan,daya daga cikin kanana kasashe na daular Han ta yamma.Bisa abin da aka rubuta a cikin tarihi,an ce an nada Liu Sheng sarkin kasar Zhongshan ne a shekara ta 154 BC,yana kan kujerar mulki har tsawon shekaru 42,shi sarki ne na farko na kasar Zhongshan.

An gina kabarin Liu Sheng a cikin wani tsauni,kabarinsa na da ramuka daban daban.akwai rami na barci da rami na zama da rami na kide kide da sauransu,sai ka ce wata kyakkyawar fada ce da ke cikin tsauni.

Daga fasalin kabarin,ana iya gane cewa an sa hankali sosai wajen tsara fasalin kabarin Liu Sheng wanda ya fi kasaita,aiki ne mai wuya.Ko ma a zamanin yau da ke da hanyoyi masu sauki wajen aiki,in ana so a gina irin wannan kabarin a cikin tsauni,a kalla dai sai an shafe shekara daya da mutane sama da dari suna aiki.

An gano kayayyakin tarihi masu yawa a cikin kabarin Liu Sheng dukkansu an jejjera su cikin tsari.Kaya mafi yawa daga cikinsu kayan tangaram,sa'an nan kayan tagulla,kayan karfemda kayan zinariya da azurfa,wanda ya fi shahara shi ne rigar lu'u lu'u.

"Rigar lu'u lu'u" an dinke ta ne da kananan guntayen lu'u lu'u masu siffofi iri iri wadanda kowanensu na da karamin rami a jiki an hada su tare da zaren zinariya.Rigar nan ta kasu kashi biyar,akwai kashi na kai da na jikin sama da na wando da na hannu da na kafa.tsawonsa ya kai wajen mita biyu,yawan lu'u lu'u ya kai 2498,nauyin zaren zinariya ya kai gramme 1100.A jikin rigar lu'u lu'u akwai abin rufe ido da abin rufe hanci da kunne da kuma baki har ma da abin rufe azzakari da dubura,dukkansu an yi su da lu'u lu'u.

Bisa nazarin da masana suka yi,an ce dinke rigar lu'u lu'u ba aiki mai sauki ba ne,da farko sai a yanke manyan duwatse masu daraja,sa'an nan a mai da su zama kanana guntayen lu'u lu'u masu siffofi iri iri da jiki ke bukata,a haka rami a kowanesu,sa'an nan a hada su tare.Diameter na ramin kowane lu'u lu'u millimeter daya kawai,lalle da wuyan dinke rigar nan mai ban mamaki a duniya.

Kamar yadda aka gano rigar lu'u lu'u a wurin Liu Sheng,haka aka gano wata daban a wurin matarsa Dou Wan.Wannan riga ta kuma kasu kashi biyar akwai kashi na kai da na jikin sama da wando da na hannu da kafa.girmarta ba ta kai ta Liu Sheng ba,cikakkun rigunan lu'u lu'u da aka gano a kabarin Liu Sheng da Dou Wan,rigunan lu'u lu'u ne da aka gano a karo na farko a cikin binciken kayan tarihi na kasar Sin,sun kara wa mutane fahimtar siffar rigar daular Han da fasalinta.

Banda rigar lu'u lu'u ,an kuma tono allurar zinariya da na azurfa da tasa mai zane da likitoci ke amfani da su,muhimman abubuwa ne a cikin tarihin amfani da fasahar allura wajen kiwon lafiya da likitanci na kasar Sin.An kuma gano wata butar tagulla da ke amfani da ita wajen gane lokaci,tana da dadadden tarihi,tana da daraja wajen nazari a cikin tarihin binciken ilmin samaniya na kasar Sin.Wani takobin da Liu Sheng ke amfani da shi,fasahar kera shi tana da wuya sosai a wancan zamani,ta shaida fasahar da kasar Sin ke da ita wajen narke karafa a wancan zamani.

A shekara ta 1988,gwamnatin kasar Sin ta mai da kabarin nan ya zama muhimmin wurin kare kayayyakin tarihi na kasar Sin saboda matukar darajarsa.

Binciken tarihin kasar Yelang a zamanin da

"Nuna girman kai na sarkin kasar Yelang" Karin magana ce da ya ke sanin kowa a kasar Sin,ya samo asali ne daga wata tatsuniya game da wata kasar Yelang dake kudu maso yamman kasar Sin kafin shekaru dubu ko fiye.Kasar Yelang ta taba wadata cikin shekaru sama da dari a tudun Guizhou,daga baya ta bace.A farkon karnin nan masana binciken kayan tarihi na kasar Sin sun tono sirrin kasar Yelang a zamanin da ta hanyar binciken garken kabarai a Hezhang dake a lardin Guizhou a yanzu.

A watan Satumba na shekara ta 2001,an gano kaburbura 108 na zamanin kasar Yelang a kauyen Kele na gundumar Hezhng na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin,an samo kayayyakin tarihi masu yawa a cikin wannan binciken da aka yi suna da muhimmiyar ma'ana wajen binciken al'adu da tarhi na kasar Yeland.Abin da aka gano a wannan bincike ya zama daya daga cikin muhimman batutuwa guda goma da aka gano cikin bincike a shekara ta 2001.Kasar Yelang a zamanin da kasa ce da kanana kabilu ke mulki ta yiwu ta kasance tsakanin karni na uku BC zuwa karni na farko AD.A karni na biyu BC,shahararren masanin tarihi na daular Xihan Si Maqian ya kai ziyara a kanana kasashe da kanana kabilu ke mulki tare da jakadan gidan sarauta na daular Han.A cikin littaffan da ya wallafa kan kanana kasashe dake kudu maso yamma,ya rubuta haka daga cikin kanana kasashe da ke kudu maso yamma,kasar Yelang ta fi girma,tana da kwararrun dakaru dubu dari,jiragen ruwa dake kai da kawo a cikin koguna tana da wadatu sosai.Yayin da sarkin kasar Yelang ke hira da jakadan gidan sarauta na daular Han,ya tambayi jakadan cewa "Kasar Han tana da girma ko kasar Yelang tana da girma?".A wannan lokacin kasar daular Han ta mallaki yawancin yankunan kasar Sin.kasar Yelang tana cikin wasu tsaunuka ne kawai,sarkin Yelang ya san bambancin dake tsakanin kasarsa da daular han ba shi ya sa ya saka tambayar nan ba.Daga nan wannan Karin magana ta samu domin siffanta mutanen dake nuna girman kai,kuma kamar abin dariya ne har zuwa yanzu,kuma shaida ce da ta bayyana kasancewar kasar Yelang a kasar Sin kafin shekaru dubu biyu.

Kasar Yelang tana da arzufattun al'adu masu ban mamaki.Bayan bacewar wannan kasa,ba wanda ya san tarihin kasar Yelang a tarihi ba saboda canje canjen da aka samu wajen yankunan mulki da kaurar kanana kabilu da karancin takardu,ta zama wata tambaya ce mai jawo hankula cikin tarihin kanana kabilu na kasar Sin a zamanin da.Yawancin yankunan kasar Yelang suna cikin lardin Guizhou na zamanin yau.Daga dandalin tattara dakaru da aka bar a gundumar Hezhang da kayayyakin gine gine da aka tono,ana iya tsammanin hali mai armashi da wannan kasar Yelang ke ciki.Binciken al'adun kasar Yelang a tarihi,muhimmin aiki ne na ma'aikatar binciken kayan tarihi ta gwamnatin Guizhou.An gano dabi'un binne gawawwaki na kasar Yelang da ya sha banban da na sauran kasashe a cikin binciken garken kaburburan a kauyen Kele a gundumar Hezhang ya kasance daya daga cikin manyan batutuwa guda goma da aka gano a fanning binciken kayayyakin tarihin kasar Sin a shekara ta 2001.

Kaburburan da aka tono a kauye Kele na gundumar Hezhang sun shimfidu a tattare,kowanensu ba shi da girma,tsawon wasunsu bai kai miata uku,fadinsu ba kai mita daya ba.Duk da haka hanyoyin da aka bi wajen binne gawawwaki sun sha banban.Daga cikinsu tukwanen tagulla kamar ganguna da aka tono.Kaya ne da aka kakaba kan mamaci ko kafafuwansa,wasu kuma an kakaba su a kafaffuwa tare da kwanon tagulla na wanke.Wata hanyar daban da aka bi wajen binne mamaci ita ce aka kakkaba wa mamaci kwanon tagulla na wanki bisa fuska ko keya,ko an dasa takobi kusa da kan mamaci.Ba a taba ganin irin hanyoyin binne mamata da aka bi a kasar Sin ba kafin wannan,hanya ce da kasar Yelang ke da ita kawai wajen binne mamatu.A ganin masana,wannan ya shaida mutanen Yelang sun mutumta kurwa da kayan tukwane da ganguna da kuma abubuwan wanki.A ganin wasu kwararru,a kara nazarin hanyar nan ta musamman wajen binne matattu da ra'ayoyinsu game da addini.

Kayan tagulla da aka tono daga kaburburan Kele ba ma kawai sun cika gibin da ke akwai a fanning al'adun tagulla a lardin Guzhou,hatta ma halayen musamman na kanana kabilu da suke da su suna da daraja sosai wajen bincike.Kamar su tukwanen tagulla kamar ganguna da takobin tagulla da makamancinsu dukkansu sun sha banban da irin kayan da aka gano a tsakiya da sauran yankunan kasar Sin.Kayan tagulla da aka tono suna da tsarin kayan tagulla na kasar Yelang.Kabaran da aka tono a kauyen Kele a gundumar Hezhang suna dauke da sawun kasar Yelang cikin tarihi ba a rubuce ba,wannan kasa da ta bace kafin shekaru dubu biyu ta fara bayyanu.A ganin wasu masana daga kabaran Kele ana iya samun amsar tambayar kasar Yelang a zamanin can da.

Tangaram da kasar Sin

Kalmar Turanci "China" tana da ma'anar "kasar Sin",kuma tana da ma'anar tangaram.Tun tuni ake kiran kasar Sin "kasar Tangaram",Wace nasaba dake tsakanin kasar Sin da tangaram?

Takardun da aka rubuta wajen binciken kayayyakin tarihi sun tabbatar da cewa tangaram yana da dadadden tarihi,an samunsa ne daga kayan tukwane.kayan tangaram da aka gano a Longshan na gundumar Xia ta lardin Shanxi na kasar Sin yana da tarihi na tsawon shekaru kimanin 4200.

Kayan tangaram na gaskiya ya bullo ne a daular Donghan (daga shekara ta 23 zuwa shekara ta 220 AD).An fara yin kayan tangaram ne a lardin Zhejiang dake kudancin kasar Sin.Daga baya fasahar yin tangaram ta shiga arewa daga kudu,ta kuma samu cigaba sosai.Muhimmin abu da aka samu cikin cigaban fasaha,shi ne fasahar yin kayan tangaram mai fari.Kafin wannan launin tangaram ba fari ba ne,mai launin toka-toka ne.Samun tangaram mai launin fari yana da muhimmin tasiri ga cigaban fasahar tangaram saboda ana iya shafa masa fenti mai launi iri iri.

Fasahar yin kayan tangaramta cigaba da ingantatuwa a dauloli na Tang da na Song (Daga karni na 10 zuwa karni na 13 AD).Tangaram mai launi iri iri na daular Tang,kayan fasaha ne da aka kirkiro a wannan zamani.muhimmin dalilin samun launi iri iri shi ne lokacin da ake tuya kayan tangaram a cikin dakin musamman da aka kebe,fentin da aka shafa wa tangaran ya canja.Da farko an yi zane zane irin na kasar Sin a jikinsa ko sassaka ko yi masa ado yadda ya ke so,sa'an nan an shafa masa fenti mai launin ja da kore da fari,aka jejjera su cikin dakin tuya mai zafi,daga baya kayana tangaram ya zama kayan tangaram mai launi iri iri.

A daular Ming (Daga shekara ta 1368 zuwa shekara ta 1644 AD) da daular Qing (Daga shekara ta 1644 zuwa shekara ta 1911),kasar Sin tana kan gaba wajen kera tangaram a duniya,yawan tangaram da ta kera ingancin kayan tangaram nata dukkansu sun kai matsayin koli.Birnin Jingdezhen dake kudancin kasa ya zama cibiyar kera tangaram a kasar Sin,tarihinsa na da shekaru daruruwa.Ga shi a yau kayan tangaram masu inganci sun fito ne daga wannan wuri.Tun daga karni na 8 AD kasar Sin ta fara fitar da kayan tangarama zuwa kasashen waje.Kafin wannan "hanyar silk" da ta shahara ta hada kasar Sin da kasashen waje wajen cinikayya da al'adu,ana kiran kasar Sin "kasar silk".Bayan karni na 8 AD,tare da karuwar kayan tangaram na kasar Sin da aka sayar da su a kasashen waje,sai kasar Sin ta fara samun sunan "kasar tangaram".

Muhimmiyar nahiya da kasar Sin ta fara fitar da tangaram zuwa waje ita ce Asiya.Bayan karni na 17 na AD,gidajen sarauta da na gwamnatocin kasashen Turai ta yamma sun fara tattara tangaram na kasar Sin.Bayan da kasar Portugal ta bude sabuwar hanya,tangaram ya zama kyauta mai daraja a kasashen Turai.A wannan lokacin fasahar Rococo ta gagara a kasashen Turai wadda ta hada fasahar Turai da ta kasar Sin gu daya,shi ya sa kayayyakin kasar Sin ciki har da tangaram sun kwarara zuwa kasashen Turai.Bisa kwarya kwaryar kididdiga da aka yi,an ce a karni na 17,kasar Sin ta fitar da kayan tangaram dubu metan a kowace shekara,a karni na 18,yawansu ya kai kimanin miliyan daya a shekara.Ana sayar da tangaram na kasar Sin a ko ina a duniya,tangaram ya zama kayan ciniki na duniya.Kalmar China ta bazu tare da kayan tangaram na kasar Sin da Britaniya da nahiyar Turai,daga baya kayan tangaram (China) ya zama sunan kasar Sin.Har zuwa yanzu ba a san ainihin lokacin da kasar Sin ta samu wannan suna na turanci ba,duk da haka babban cigaban da kasar Sin ta samu wajen yin kayan tangaram da barbazuwar kayan tangaram a duniya sun sa mutanen duniya suna son kayayyaki masu sigar musamman na kasar Sin da suka hada kasar Sin da kayan tangaram sosai da sosai.

Kabari na daular Han a Mawangdui dab da Changsha na lardin Hunan

Abin da aka tono daga kabarin daular Han a Mawangdui dab da Changsha dake kudancin kasar Sin a shekarun 1970 ya girgiza kasar Sin da duniya baki daya.Karo na farko a duniya da aka gano wata gawar mata cikin hali mai kyau.Yau shekaru sama da dubu biyu ke nan da aka ajiye gawar nan cikin kabarin,fuskarta kamar tana da rai,fatarta tana da laushi,lalle abu ne mai ban mamaki.A sa'I daya kuma an tono kayayyakin tarihi masu daraja iri iri daga cikin kabarin nan.

Wata tatsuniya da ta yadu a tsakanin jama'a dake zama a karkarar birnin Changsha na lardin Hunan da ke kudancin kassar Sin ta ce ana kira wannan wuri da sunan Mawangdui saboda an binne wani sarki mai suna Ma a nan.wata tatsuniya daban ta ce an binne mahaifiyar sarkin Changsha a zamanin da a nan,daga nan aka kirkiro da tatsuniyoyi iri iri.A shekara ta 1971 yayin da ake gina wani daki a karkashin kasa,aka haka kasa sosai sai aka ga wani tabo fari da taushi,aka cigaba da hakaawa,wata iska mai wari ta fito,da aka kyasta ashana,nan da nan iskar ta kams wuta kamar wani maciji da ya kama wuta,wani yana so ya kashe wuta da ruwa,iskar ta ja da ruwa baya,daga baya aka kashe wutar da buhun da ke dauke da sumunti.

Bayan da kwararru suka yi bincike,sai aka gano wani kabarin na zamanin da a karkashin kasa.Da aka tono,aka iske wani ramin da ke cike da tabo mai launin fari dake da tsayi fiye da mita daya,a karkashin tabo mai fari shi ne gawayi kimanin kilo dubu biyar da lorori guda hudu za su iya dauke su.Bayan da aka kawar da gwayi,sai ka ga tabarma gomamiya masu launin rawaya kamar sabbi,bayan mintuwa goma sai sun zama abin wofi mai launin baki.Akwai akwatuna guda hudu daya cikin daya,akwatin da ke waje mafi girma tsawonsa ya kai mita 7 fadinsa ya kai mita biyar da tsayinsa kusan mita uku.

Bayan da aka bude akwatin,sai aka ga gawar wata mata,surarta a bayyane,tana da gashi da tambarin yatsu da na kafa ana iya ganinsu,fatarta na da laushi da tankwara,gabbobinta na iya motsawa.Da aka yanke jikinta filla filla,kayan dake cikin jikinta suna cikin kyakkywan hali da cikin makogwaronta da tumbi da kuma hanunta da akwai kwayoyin kankana,wannan ya bayyana cewa matar nan ta mutu ne a yanayin da kankana ta nuna ta ci kwayoyin kankana.A cikin kabarin akwai tambarin Xin Zhui.Bayan da aka yi bincike,an ce kabarin nan kabari ne na matar wazirin kasar Changsha a farkon zamainin daular Xihan kafin karni na biyu AD,sunanta Xinzhui.

"Gawar matan da ba ta rube sosai ba cikin shekaru dubbai" ta girgiza duniya. Masana da masu yawon shakatawa da masu shirya sinima da kuma masu binciken ilmin kimiyya dukkansu sun taru a birnin Changsha.Bisa kididdigar da ma'aikatar da abin ya shafa ta yi,an ce cikin gajeren lokaci bayan da aka gano gawar jikin mata a Mawangdui,an sami karin mutane dubu hamsin nan take a birnin Changsha.Cikin shekaru biyu bayan da aka tono kabarin Xinzhui,an kuma tono manyan kabarai biyu na daular Han a kusa.Bisa binciken da aka yi,an ce daya kabarin namijin Xinzhui ne,sunansa Li Cang,wazirin kasar Changsha,wani kabarin daban na dansu ne.Ana kiran kaburburan nan uku "kaburburan daular Han a Mawangdui dab da birnin Changsha.Kayayyakin tarihin da aka tono daga kabaran sun yi yawan gaske,ciki har da tufaffi da abinci da magungunan sha da kayan fenti da mutum-mutumin katako da kayan kida da tangaram da zane zanen dake bisa silk da kuma rubutun dake bisa silk da jikin bamboo.Duk wadannan kayayyakin tarihi,kayayyaki ne na fasaha da ake iya amfani da su,suna da daraja sosai.An tono kayan saka 1400 daga kabaran,sai aka kira su siton ajiye kayan silk na daular Xihan (Daga shekara ta 206 BC zuwa shekara ta 25 AD) mai ban mamaki.Daga cikinsu akwai rigunan silk biyu,tsawonsa ya kai mita daya da 'yan kai,tsawon hannayensa ya kai wajen mita biyu,nauyinsa gramme 28 kawai.wata babbar riga,ana iya ajiye ta cikin tsakiyar taffin hannu,idan an sanya ta,sai ka ce yana sa rigar hayaki ne.Wannan ya shaida babban cigaban da kasar Sin ta samu a fanning fasahar saka.Kayan rubutun da aka tono daga kaburburan,littattafai ne dangane da ilmin sararin samaniya da yanayi kamar su "tsafi bisa taurari biyar" da "tsafi da alamun yanayi" da kuma likitanci da magungunan sha na gargajiya kamar su "dokokin bugawar jinni" da "hanyoyin da ake bi wajen kawar da cututtuka 52" na kasar Sin a wancan zamanin da.rubutu da yawa da aka tono sun canja ra'ayoyin dake akwai a kasar Sin.

Kayan tarihin da aka tono daga kaburburan Mawangdui sun haifar da tasiri mai zurfi ga masu binciken kayayyakin tarihi na kasar Sin.A ganin masana,abubuwa mafi daraja da aka gano a kabaran nan su ne gawar jikin mata a cikakkun kayayyaki da kuma rubutun dake bisa siliki da gora.Idan aka sami daya,muhimmin batu ne,ga shi a yau an gano uku,babu wani wuri daban da ya yi kama da Mawangdui kan kayayyakin tarihin da ya samar,sabili da haka,kayayyakin da aka tono daga kabaran daular Han a Mawangdui "wani batu ne mafi muhimmanci a fannin binciken kayayyakin tarihi na kasar Sin da duniya a karni na 20.

Ramukan Mogao a Dunhuang

Ramukan Mogao a Dunhuang dake arewa maso yammacin kasar Sin,wani babban sito ne na kayayyakin fasaha na kasar Sin,yana daya daga cikin manyan sito guda hudu na ramuka a kasar Sin,abubuwan da aka tanada a ciki suna da yawa,siton ya tattara duwatsun fasaha na sassaka na dauloli fiye da goma da mai tsawon shekaru kimanin dubu,wurin tarihi na addinin Buddha ne mafi girma a duniya dake cikin hali mai kyau.

A wani tudun dake karkarr birnin Dunhuang na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin ana kitansa "tudun karar rairayi".A jikin tudun na gabas an haka ramuka masu tarin yawa bisa benaye biyar mai tsawon kimanin kilomita biyu daga kudu zuwa arewa,wadannan ramuka sun kasance layi bisa layi masu kyaun gani,su ne ramukan Mogao na Dunhuang da ya shahara a duniya.

An fara haka ramuka ne a shekara ta 366 AD.Wata rana wani mai zaman zuhudu da ake kiransa Le Zun ya isa Dunhuang.Da ya ga haske na walkiya a tudun karar rairayi tamkar mabiyar addinin Buddha dubu dubbai sun bullo,yana tsammanin wurin wuri ne mai tsarki.Daga nan ya gayyaci wasu mutane da su haka rami na farko a jikin tudun.Bayan da aka yi ta gine gine cikin dauloli daban daban,yawan ramukan ya yi ta karuwa.A lokacin daular Tang na karni na bakwai AD,ramukan Mogao sun wuce dubu.shi ya sa ana kiran rmukan Mogao "ramuka dubu na addinin Buddha".

Ramukan Mogao wata fadar fasaha ce da ta hada fasahohin gine gine da zane zanen jikin bango da sassaka.Lokacin da mutane na dauloli daban daban suka haka ramuka,sun kuma sassaka mutum mutumin Buddha da yawa da yin zane zane kan jikin bango.Dayake aka samu sauye sauye cikin tarihi da kawo lahani,har wa yau dai da akwai ramuka wanen dari biyar da zane zanen bisa bango mai fadin muraba'in mita dubun hamsin da mutum mutumin sasska sama da dubu biyu a Mogao.Siffofinsu ya sha bamban,tufaffi da suka sa ba daya ba,hanyoyin gwadawa ma sun bambanta,sun shaida halayen musamman na dauloli.Zanen dake bisa jikin bango yana da kyaun gani,idan aka hada zane zanen dake cikin dukkan ramukan,tsawonsu zai iya kai kilomita wajen talatin.Ramukan Mogao su kasance wuri mai nisa daga cibiyar kasar Sin,suna cikin barci na shekaru daruruwa ba su jawo hankulan mutane ba.Duk da haka a farkon karni na 20,wani siton ajiye littattafai masu daraja da aka gano a wannan wurin ya girgiza duniya,wata masifa mai bacin rai ta hassarar kayayyakin tarihi masu yawa ta biyo baya a tarihin zamanin da na kusa na kasar Sin.

A shekara ta 1900 yayin da wani mai kula da ramukan Mogao ya ke sharar rairayi,sai ya gano wani dakin sirri ba zata.,daga baya ana kiran dakin sirri dakin ajiye littattafan addini.A cikin wannan rami mai tsawo da fadi mita uku aka tanadi littattafan addini,kayan silk da zane zane da hotunan mabiyan Buddha da sauran kayayyakin da ba a taba ganinsu ba,yawansu ya kai wajen dubu hamsin.Wadannan kayayyakin tarihi an kera su ne daga karni na hudu zuwa karni na goma sha daya AD,sun shafi kusan dukkan fannonin zamantakewar al'umma ciki har da tarihi da labaran kasa da siyasa da kabilu da soja da harsuna da fasahar adabi da addini da likitanci da magungunan sha na kasar Sin da kasashen Asiya ta tsakiya da ta kudu da na Turai ana kiransu cikakken kamus na zamanin da na tsakiya.

Bayan da aka gano ramin ajiye littattafan,an kai wasu kayayyakin tarihi waje da ramuka domin samun riba.Tare da shigowar wadannan kayayyakin tarihi cikin jama'a ne sai aka sami labarin rubutun hannu na zamanin da da aka boye cikin ramukan Mogao.Masu bincike na sauran kasashen duniya sun kwararo.A wancan zamani gwamnatin Qing ba ta da karfi,masu bincike na Rasha da Britaniya da Faransa da Japan da Amurka sun kwace littattafai dubu arba'in da zane zanen kan bango da kayan sassaka masu daraja da yawa daga Dunhuang bi da bi cikin shekarun da yawansu bai kai ashirin ba.Wannan babbar masifa ce ga ramukan Mogao da aka kawo musu.A halin yanzu a kasashen Britaniya da Faransa da Rasha da Indiya da Jamus da Denmark da Sweden da Korea ta kudu da Finland da Amurka aka tanadi kayayyakin tarihi na Dunhuang,yawansu ya kai kashi biyu cikin kashi uku na dukkan kayayyakin tarihin da aka tanada a ramin ajiye littatttafan.Bayan da aka gano ramin ajiye littattafan,wasu masana na kasar Sin sun fara nazarin takardun Dunhuang cikin mawuyacin hali.A shekara ta 1910,rukunin farko na littattafan da masanan Sin suka wallafa kan takardun Dunhuang ya fito fili,daga nan kungiyar masana nazarin takardun Dunhuang ta kafu.A cikin shekarun gomamiya da suka shige,masanan kasashen duniya masu sha'awar fasahar Dunhuang sun yi ta nazarin fasahar nan,a fannin nazarin takardun Dunhuang,masanan kasar Sin su ma sun sami sakamo mai babban tasiri.Ramukan Mogao na Dunhuang wurin al'adu ne mai daraja sosai na kasar Sin,tun tuni gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci wajen kare wurin nan.A shekara ta 1950,gwamnatin kasar Sin ta mai da ramukan Mogao cikin muhimman wuraren tarihi na farko da ya kamata a kare su.A shekara ta 1987,kungiyar UNESCO ta majalisar dinkin duniya ta sa sunan ramukan Mogao cikin jeren sunayen wuraren tarihi na al'adu na duniya.Ga shi a yau a gindin tudun Sanwei dake gaba da ramukan Mogao,an gina wata cibiyar nuna kayayyakin fasaha na Dunhuang,an yi kwakwayon wasu ramuka,ta haka aka kare kayayyakin tarihin dake cikin rmuka,an kara abubuwan kallo ga maziyararta.Masu yawon shakatawa na ketare sun yi sharhi kan ramukan Mogao cewa ramukan Mogao sun kasance "sito mafi girma na kayayyakin fasaha na addinin Buddha dake akwai a duniya."

Labari dangane da gano kekuna da dawaki na tagulla a kabarin sarki na farko na daular Qin

A shekara ta 1980 bayan shekaru shida da aka gano mutum-mutumin da dawaki na daular Qin,masana binciken kayayyakin tarihi na kasar Sun sun kuma gano kekuna da dawaki na tagulla a kabarin sarki na farko na daular Qin,abin da aka gano a wannan gami ya sake girgiza duniya.

Mista Yang Xude,masanin binciken kayayyakin tarihi shi ne mutumi na farko da ya gano wannan dukiya mafi daraja a kasar Sin.Yayin da ya huda kasa da inji a wuri mai tazara mita 20 daga kabarin sarkin farko na daular Qin,ya gano wani kwan zinariya kamar yatsa a cikin tabon da injin ya kawo sama daga kasa mai zurfin mita bakwai.Da ya ba wa jagorar wurin Chen Xuehua kwan yatsa da ya samo,Mista Chen Xuehua ya yi farin ciki,ya ce an samo kekuna da dawakin tagulla da ake nemansu ruwa a jallo tun tuni.

Bisa jagorancin kwararru ne,mahaka suka mai da hankalisu sosai wajen haka wurin da ke da kekuna da dawakin na tagulla a karkashin kasa .Bayan da suka yi ta haka wajen wata daya,aka gano kekunan biyu da dawakin takwas da matukan biyu na tagulla a karkashin kasa mai zurfin mita 7.8.

Bayan da aka samu kekuna da dawakinna tagulla,masana sun yi dogon tunani kan yadda za a fitar da su.Da farko sun haka ramuka masu zurfin mita 10 a kekuna da dawakin tagulla,an rufe su da manyan akwatuna guda hudu masu tsayin mita daya,sa'an nan a sa wani babban abu kamar shefur (wato spade a turance) a karkashinsu,daga baya wani babban inji mai daga kaya ya daga su gaba daya,an ajiye su a cikin lori da ya kai su cikin dakin nuna kayayyakin tarihi na daular Qin.

Bayan da aka gyara kekuna da dawakin tagulla cikin shekaru biyu da suka gabata a dakin nuna kayayyaki na daular Qin,an gwada su ga mutane.Fitowar kekuna da dawakin tagulla ta girgiza duniya.

Girman kekuna da dawakin na tagulla da aka gano ya kai kashi daya cikin kashi biyu na ainihinsu da ke akwai a doron kasa,fasalinsu da siffofinsu da fasahohin kera su dukkansu ba kamarsu a duniya..Fasahohin kerarsu,wasu har wa yau dai ana amfani da su,wasu har wa yau kuwa ba a san sanadinsu ba.

Yadda aka yi mutum-mutumin soja da dawaki a daular Qing

A shekara ta 1989 yayin da wata tawaga ta ofishin binciken kayayyakin tarihi na cibiyar nazarin ilmin kimiyya na zamantakewar al'umma ta kasar Sin ke huda kasa a wata gona ta kauyen Liucunbao a yankin Weiyang na birnin Xi'an na lardin Shaanxi,an gano ramuka 21 na daular Han ta yamma mai dadadden tarihi na shekaru 2100 da aka tono domin tuya manyan mutum-mutumin sojan da dawaki,an tono dubban makamantansu.Ramukan da aka gano, ramukan musamman ne da aka gina na tuya mutum-mutumin soja da dawaki domin sarakuna da gwamnatoci.

Da haka ana iya ganin cewa ba abin mamaki ba ne da aka samu mutum-mutumin sojan da dawaki masu yawa na daular Qing a zamanin yau.Mutum-mutumin da aka tono sun samar da hanyar yinsu.Da farko an yi samfurin mutum-mutumin,an sassaka masa ido da baki da kunnuwa da hanci da harshe a fuskar kafin a tuya shi,an kuma shafa farin tabo ga yawacinsu.Lokacin da ake tuya su,abin ban sha'awa shi ne yadda aka jejjera su cikin ramukan tuya,ba kamar yadda aka yi tsammani ba kafafuwansu ba a kasa suke ba,kawunansu ne a kasa, kafafuwan na sama.Hanyar da aka bi tana da ilmin kimiyya a ciki,dalili kuwa shi ne sashin jikunan mutum-mutumin na sama ya fi na kasa nauyi,da kawunansu a kasa,mutum-mutumin ya tsaya tam tam ba fadi da wargaje ba.Wannan ya ba da shaida cewa mutanen kasar Sin suna da ilmin kimiyya kan nauyin abu kafin shekaru sama da dubu biyu.Bayan da aka tono mutum-mutumin soja da dawaki na daular Qing,wasu mutane sun yi kwaikwayon dawaki,ba su san wannan hanya ta tsohon zamani da aka bi ba,sai su sa kafafuwan dawaki kasa,ba da jimawa ba dawakin sun wargaje sun sha kaye da yawa.A zamanin daular Qing, an bi wani tsarin sa sunayen magini a jikunan mutum-mutumin da suka gina,ya kamata magina suka sassaka sunayen a jikunan don gane adadin da suka gina da kuma ingancinsu,wannan shi ne dalilin sanya sunayen magina da aka bari a jikunan .A halin yanzu ana iya gane sunaye 85 ciki har da Gongbing da Gongjiang.

Yadda aka kera tukwanen tagulla mafi girma a duniya

A watan Maris na shekara ta 1939,an tono wata tukunyar tagulla mafi girima a duniya a wata gona dake arewacin kauyen Wuguan na birnin Anyang na lardin Henan dake tsakiyar kassar Sin,sunan tukwanen shi ne Simuwu,nauyinsa ya kai kilo 875,tsayinsa ya kai centimeter 133 da fadinsa centimeter 78.Mene ne amfanin wannan tukunyar tagulla mafi girma? Yaya aka kera ta ? Masana sun ce tukunyar Simuwu ce da aka yi amfani da ita wajen nuna ban girma ga mahaifiya da ta rasu.Bayan da aka yi nazarin tarihi,an tabbatar da cewa tukunyar tagulla Simuwu,tukunya ce da sarki Zegeng na daular Shang ya yi amfani da ita domin nuna ban girma ga mahaifiyarsa Biwu da ta rasu.A da masana suna masu ra'ayin cewa an kera wannan tukunya ce kashi kashi,watau an kera kunnuwa da jiki da kuma kafaffuwa,sa'an nan a hada su tare.Bayan da aka yi binciken filla filla baya bayan nan,an tabbatar cewa an kera ta ne gaba daya ta hanyar al'ada ta zubi.Kafin an kerata,ya kamata an yi samfurinta da tabo.Da aka samu samfuri,an zuba ruwan tagulla mai zafin gaske a ciki daga kafaffuwanta biyu,dayan kuma hanyar fitowar iska.Da aka gama wannan,sai an kara mata kunnuwa biyu ta hanyar nan,ta haka aka samu tukunyar tagulla ke nan.