logo

HAUSA

Babi02: Siyasa

0001-01-01 08:00:00 CRI

>>[Tsarin Siyasa]
Tsarin mulki
Jumhuriyar jama'ar kasar Sin kasar gurguzu ce mai mulkin shibtar demokradiya ta jama'a wadda ajin ma'aikata ke shugabanta, kuma kawancen ma'aikata da manoma ke tushensa.
Tsarin mulki
Tsarin mulki kuwa babbar doka ce ta kasa. Ya tanada muhimman abubuwa misali, babbar ka'idar tsarin zaman al'umma da tsarin kasa na wata kasa, babbar ka'idar shirin kungiya da aikace aikacen hukumomin kasa, da babban hakki da alhaki na 'yan kasa, ya kan tanada tutar kasa da taken kasa da tambarin kasa da hedkwatar kasa da sauran muhimmin tsari da mahukunta ke so, suna shafar fannoni daban daban na zaman kasa. Tsarin mulki yana da amfanin doka na koli, shi ne jigon aikin tsara sauran dokoki, bai kamata ba sauran dokoki su yi gaba da tsarin mulki.
"Tsarin tarayya na taron ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin" da aka bayar a gabannin kafuwar Jumhuriyar jama'ar kasar Sin, wani tsari ne na hadadden fagen demokradiyar jama'ar kasar Sin, kuma tsarin mulki ne na wucin gadi. An zartas da <> ne a cikakken zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma an bayar da wannan tsari a ran 29 ga watan Satumba, shekara ta 1949. Kafin bayar da "Tsarin mulki na Jumhuriyar Jama'ar kasar Sin" a shekara ta 1954, wannan tsari ya yi amfanin tsarin mulki na wucin gadi.
Tun bayan da aka kafa Jumhuriyar Jama'ar kasar Sin a ran 1 ga Oktoba, shekara ta 1949, aka tsara da bayar da tsarin mulkin Jumhuriyar Jama'ar kasar Sin guda 4 a shekara ta 1954, da shekara ta 1975, da shekara ta 1978, da shekara ta 1982.
An tsara tsarin mulki na 4 na kasar Sin, wato tsarin mulki na yanzu ne a ran 4 ga watan Disamba, shekara ta 1982, an zartas da bayar da wzannan tsarin mulki a gun cikakken zama na 5 na majalisa ta 5 ta wakilan jama'ar duk kasar Sin. Wannan tsarin mulki ya gaji da yalwata babbar ka'idar tsarin mulki na shekara ta 1954, ya takaita fasahohi na yalwata zaman gurguzu na kasar Sin, kuma ya tsamo fasahohin kasashen duniya, sabo da haka wata babbar doka ce mai sigar musamman ta kasar Sin kuma ke dace da bukatun raya zaman gurguzu na zamani na kasar Sin. A fili ne ya tanada tsarin siyasa da tsarin tattalin arziki da hakki da alhaki na 'yan kasa da kafuwar hukumonmin kasa da alhakinsu da babbar dawainiyar kasa ta nan gaba na Jumhuriyar jama'ar kasar Sin. Ya tanada cewa, dole ne jama'ar kabilun duk kasa da dukkan kungiyoyi su dauki tsarin mulki a kama da ka'idarsu ta aikace aikace, duk wata kungiya da duk wani mutum ba ya da ikon musamman na kauce wa tsarin mulki da doka.
Wannan tsarin mulki ya kasu gabatarwa, babban tsari, babban hakki da alhaki na 'yan kasa, hukumomin kasa, tutar kasa, tambarin kasa da hedkwatar kasa, yana da babi 4 da ayoyi 138. Tun bayan da aka bayar da wannan tsarin mulki, kasar Sin ta yi gyare gyare har sau 4 don kyautata shi.
Tsarin majalisar wakilan jama'a
Tsarin majalisar wakilan jama'a babban tsarin siyasa ne na kasar Sin, salon kungiyar mulki ne na mulkin shibtar demokradiyar jama'ar kasar Sin, kuma tsarin siyasa ne na kasar Sin. Ya yi banban da majalisa da ke karkashin tsarin mulki mai iko na kashi 3 na kasashen yammacin duniya, Tsarin mulki na kasar Sin ya tabbata cewa, majalisar wakilan jama'ar duk kasa hukuma ce mai ikon koli na kasa. 'Yan kasa da shekarunsu suka kai 18 duk suna da ikon zabe da zabe su da su zama wakilan majalisa. A majalisu na matakai daban daban na jama'ar kasar Sin, kai tsaye ne a ke zaben wakilai na matakan gundumomi da garuruwa, majalisu na sama da su ba kai tsaye a ke zabe ba. Majalisar wakilan jama'ar duk kasa tana kunshe da wakilan da aka zaba a larduna da jihohi masu ikon kai da birane masu matsayin larduna da rundunar soja. Tsawon lokaci da majalisun jama'a ke kan mukamansu shi ne shekaru 5, a kan yi cikakken zaman taron wakilai a ko wace shekara.
A gun taron da a kan yi a ko wace shekara na majalisun wakilai, sai wakilai su saurari rahoto kan aikin gwamnati da sauran muhimman rahotanni, wakilai za su duba wadannan rahotanni, kuma su tsai da kuduri. A lokacin da babban taron majalisu yana rufe, zaunannen kwamiti na majalisa wato zaunanniyar hukumar majalisar wakilan jama'a na matakai daban daban zai aiwatar da ikon da majalisar wakilai ta danka masa. Misali ikon zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar duk kasa shi ne bayyana tsarin mulki, da duba aiwatarwar tsarin mulki da kafa da gyara sauran dokokin da ke waje da dokokin da majalisar wakilan jama'ar duk kasa ta kafa, kuma zai dau nauyin yin rahoto ga majalisar wakilan jama'ar duk kasa da sauran ayyuka.
Babban iko na majalisar wakilan jama'ar duk kasa shi ne ikon kafa dokoki da ikon dubawa da tsai da muhimmin kuduri da ikon nadawa da tubewa. A kasar Sin tsara shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman al'umma na wani tsawon lokaci ya zama muhimmiyar manufa na yalwata zaman tarayyar kasar Sin, amma wadannan shiruruka ba za su samu amfanin doka ba, face sai majalisar wakilan jama'ar duk kasa ta zartas da su. Dokokin kasar Sin sun tanada cewa, manyan shugabannin kasar Sin su shugaban kasa da shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa dole ne majalisar wakilan jama'ar duk kasa ta zabe su. Majalisar wakilan jama'ar duk kasa kuma za ta nada firayim ministan majalisar gudanarwa da ministoci. Majalisar wakilan jama'ar duk kasa kuma tana da ikon gabatar da shirin tube shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa da shugaban kasa da firayim ministan majalisar gudanarwa da sauran shugabannin kasa bisa shirin da aka tsara.
Tsarin gama kan jam'iyyu da dama da ba da shawara kan harkokin siyasa
Tsarin gama kan jam'iyyu da dama da ba da shawara kan harkokin siyasa da ke karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wani babban tsarin siyasa ne na kasar Sin.
Kasar Sin wata kasa ce mai yawan jam'iyyun siyasa. Ban da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke kan karagar mulki kuma da sauran jam'iyyu 8 na demokradiya. Wadannan jam'iyyun demokradiya sun haifu ne tun kafin kafuwar Jumhuriyar jama"ar kasar Sin. Suna nuna goyon baya ga shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a wajen siyasa, wannan kuwa zabensu na tarihi a cikin gama kai da suka yi da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin cikin dogon lokaci da yin gwagwarmaya tare. Dole ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun demokradiya su yi aikace aikacensu bisa ka'idar tsarin mulki. Jam'iyyun demokradiya suna da 'yancin kai a wajen shirin kungiya, suna more 'yancin siyasa da 'yancin shirin kungiya da matsayin doka da tsarin mulki ya tanada. Babbar ka'idar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yin gama kai da jam'iyyun demokradiya ita ce, kasancewa cikin dogon lokaci, duba wa juna, nuna wa juna biyaya da more alfahari da kau da wahaloli tare.
Jam'iyyun demokradiya na kasdar Sin ba jam'iyyun adawa ba ne, amma jam'iyyu ne da ke halartar harkokin siyasa. Muhimman ayyuka na jam'iyyun demokradiya a wajen harkokin siyasa su ne: halarci shawarwarin da za a yi kan babbar manufar kasa da zaben shugabannin kasa, halarci ayyukan kula da harkokin kasa da hallarci aikin tsara ka'ida da manufa da dokoki na kasa.
A lokacin da kasar Sin za ta dauki muhimmin mataki ko tsai da kudurin da ke dangane da kadarar jama'a, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kan yi shawarwari da jam'iyyun demokradiya da mutanen da ba na wata jam'iyya ba don saurara ra'ayoyinsu da shawarwarinsu, sa'an nan ta tsai da kuduri. A cikin majalisar wakilan jama'ar duk kasa da zaunannen kwamitinta da zaunannun kwamitoci da majalisun wakilai na matakai daban daban, jam'iyyun demokradiya da mutanen da ba na wata jam'iyya ba duk suna da wakilansu don halartar harkokin siyasa da ba da shawara. Kuma su ba da amfani sosai a cikin kungiyar ba da shawara kan harkokin siyasa, kuma su gabatar da mutane 'yan jam'iyyar demokradiya da mutanen da ba na wata jam'iyya ba su kama mukaman shugabanni a gwamnatoci da ofisoshin shari'a na matakai daban daban.
Hanyoyin gama kan jam'iyyu da dama da ba da shawara kan harkokin siyasa su ne, da farko, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a. majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a muhimmin wuri ne da jam'iyyu daban daban da kungiyoyin jama'a daban daban da wakilan mutane na da'irori daban daban su yi taro don ba da shawara kan harkokin siysa. An biyiu, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kwamitocin jam'iyya na matakan wurare daban daban su yi taron tade tade da sanar wa juna muhimman al'amura da babbar manufar kasa da sunayen 'yan takaran shugabanni na kasa da na wuri wuri da sunayen wakilan majalisa da majalisar ba da shawara kan harkokin siiysa don saurara ra'ayoyinsu da shawarwarinsu. Na uku, 'yan jam'iyyun demokradiya wadanda su ne wakilan majalisa na matakai daban daban su halarci harkokin siyasa da ba da amfanin dubawa. Na hudu, a zabi 'yan jam'iyyar demokradiya da su kama mukami na shugabanni na gwamnatocin wuri na ma'aikatu da sassan da abin ya shafa. Na biyar gabatar da 'yan jam'iyyar demokradiya da su dace da sharuda da su kama mukami a ofishin bincike shari'a da kotu.
>>[Hukumomin Kasar Sin]
Majalisar wakilan jama'ar duk kasa
Tsarin majalisar wakilan jama'ar kasa babban tsarin siyasa ne na kasar Sin. Majalisar wakilan jama'ar duk kasa hukumar koli ce ta kasa, tana kunshe da wakilan da aka zaba a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane da jihohin musamman da rundunar soja, tana aiwatar da ikon kafa dokoki da tsai da kuduri ga manyan maganganun harkokin siyasar kasa.
Babban iko na majalisar wakilan jama'ar duk kasa shi ne gyara tsarin mulki da duba aikin aiwatar da tsarin mulki da kafa da gyara dokoki na harkokin jama'a da hukumomin kasa, da duba da zartas da shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da zaman al'umma da yadda aka aiwatar da su da ba da rahoto kan kasafin kasa da yadda aka aiwatar da shi, da yardar da tsarin larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane da tsai da tsarin jihohin musamman da tsai da maganar yaki da zaman lafiya; da zabar shugabannin hukumar ikon koli na kasa wato zabar manbobin zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar duk kasa da zabar shugaban kasa da mataimakinsa da tsai da firayim minista na majalisar gudanarwa da sauran manbobi, da zabar shugaban kwamitin soja na tsakiya da da sauran manbobi, zabar shugaban babban kotun jama'a da zabar shugaban ofishin bincike shari'a, majalisar wakilan jama'a tana da ikon tube wadannan mutane daga kan mukamansu.
Tsawon lokacin da majalisar wakilan jama'a ke kan mukaminsu shi ne shekaru 5, kuma ta yi taro a ko wace shekara. A lokacin da majalisar wakilan jama'a ta ke a rufe, zaunannen kwamiti zai aiwatar da ikon koli. Zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa yana kunshe da shugaban zaunannen kwamiti da mataimakinsa da babban sakatare da manbobinsa.
Dokokin kasar Sin suna kunshe da dokokin da majalisar wakilan duk kasa da zaunannen kwamitinta suka kafa, da dokokin da majalisar gudanarwa da ma'aikatunta suka kafa da dokoki na wuri wuri da na jihohin ikon kai na kananan kabilu da dokoki na jihohin musamman na tattalin arziki da jihohin musamman.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin
Tsarin ba da shawara kan harkokin siyasa na jama'ar kasar Sin wata kungiya ce ta kishin kasa da hada kai, kuma muhimmiyar hukuma ce ta yin shawarwarin siyasa da ke a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma wata muhimmiyar hanya ce ta yada demokradiyar gurguzu a cikin harkokin siyasa na kasar Sin. Hadin kai da demokradiya su ne manyan batutuwa biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa.
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin tana kunshe da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar sin da 'yan jam'iyyun demokradiya daban daban da mutanen da ba na wata jam'iyya ba, da wakilai na rukunonin jama'a da kananan kabilu da na da'irori daban daban, da wakilai na 'yan uwanmu na jihar musamman ta Hong Kong da Macao da Taiwan da Sinnawa 'yan kaka gida da mutanen da aka gayyace su musamman, tsawon lokacinsu kan mukami shi ne shekaru 5.
Babban aiki na kwamitin duk kasa da na wuri wuri na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin shi ne yin shawarwari kan harkokin siyasa da dubawa ta hanyar demokradiya da shiga harkokin siyasa.
Abin da a ke nufi da shawarwarin siyasa shi ne yin tattaunawa kafin kasa da wuraren kasar Sin suka tsai da manufa ga muhimman maganganu na siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman tarayya. Kwamitin duk kasa da na wuri wuri na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin za su iya shirya taruruka don yin shawarwari bisa shawarar jam'iyyar kwaminis ta kasar sin da zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'a da gwamnatin jama'a da jam'iyyun demokradiya da kungiyoyin jama'a, kuma za su iya ba da shawara ga wadannan hukumomi da su gabatar da muhimman maganganu don a yi shawarwari.
Dubawar demokradiya ita ce duba aiwatar da tsarin mulki da dokoki da mhimman manufofi da ka'idoji da aikin ma'aikatun gwamnati da ma'aikatansu, za ta iya duba su ta hanyar ba da shawara da yin suka.
Shiga harkokin siyasa shi ne bincike muhimman maganganun da ke cikin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma da maganganun da ke jawo hankulan jama'a don nuna ra'ayoyin jama'a da yin shawarwari. Su gabatar da ra'ayoyinsu da shawarwarinsu ga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ma'aikatun gwamnati ta hanyar ba da rahoton bincike da ba da shawara da shiruruka.
A watan Satumba na shekara ta 1949, cikakken zama na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin ta wakilci iko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ta wakilci burin jama'ar duk kasa, ta sanar da kafuwar Jumhuriyar Mutanen kasar Sin, ta ba da muhimmin amfani a cikin tarihi. Bayan da aka kira majalisar wakilan jama'ar duk kasa ta farko a shekara ta 1954, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'a ta daina wakiltar ikon majalisar wakilan jama'a, amma ta ci gaba da zama wata babbar kungiyar kasar Sin ta kishin kasa da hada kai, kuma ta yi ayyuka masu dimbin yawa a cikin harkokin kasa da zaman al'umma da harkokin sada zumunta da kasashen waje, ta ba da muhimmin taimako. Ya zuwa watan Maris, shekara ta 2004, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kafa hulda da hukumomi 170 na kasashe 101 na duniya da kungiyoyi 8 na kasashen duniya da jihohi, kuma ta yi cudanyar sada zumunta.
Majalisar Gudanarwa
Majalisar Gudanarwa
Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ita ce gwamnatin tsakiya ta jama'a, hukumar koli ce ta gudanarwa, ita ce ke aiwatar da dokokin da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da zaunannen kwamitinta suka kafa da kudurran da suka zartas, kuma za ta yi rahoto kan aiki ga majalisar wakilan jama'ar kasa da zaunannen kwamitinta. Majalisar gudanarwa tana da ikon tsai da matakai da dokokin gudanarwa da bayar da kuduri da umurni a cikin da'irar ikonta. Majalisar gudanarwa tana kunshe da firayim minista da mataimakinsa da manbobin majalisar gudanarwa da ministoci da darektocin kwamitoci da shugaban duba akonta da babban sakatare.
Firayim minista na yanzu shi ne Wen Jiabao
A halin yanzu majalisar gudanarwa tana kunshe da ma'aikatu 28, wato ma'aikatar harkokin waje da ma'aikatar tsaro da kwamitin raya kasa da gyare gyare da ma'aikatar ilmi da ma'aikatar kimiya da fasaha da kwamitin masana'antun kimiya da fasaha na tsaro da kwamitin harkokin kabilun kasa da ma'aikatar kiyaye zaman lafiya da ma'aikatar kiyaye kwanciyar hankali ta kasa da ma'aikatar dubawa da ma'aikatar harkokin jama'a da ma'aikatar shari'a da ma'aikatar kudi da ma'aikatar harkokin mutane da ma'aikatar tabbatar da aiki da zaman al'umma da ma'aikatar hanyar jirgin kasa da ma'aikatar sufuri da ma'aikatar albarkatan kasa da ma'aikatar gine gine da ma'aikatar sadarwa da ma'aikatar ruwa da ma'aikata ilmi da ma'aikatar noma da ma'aikatar ciniki da kwamitin yawan mutane da yin haifuwa bisa shiri da bankin jama'ar kasar Sin da ofishin duba akonta.
Ma'aikatar harkokin waje
Ma'aikatar harkokin waje wani ofis ne na aiwatar da manufar kasa ta harkokin waje wanda ke yin harkokin waje. Babban alhaki na ma'aikatar harkokin waje shi ne yin harkokin waje a madadin kasa da gwamnati, ciki har da bayar da manufa da kuduri na kasa a wajen harkokin waje da bayar da takardu da sanarwa na harkokin waje da yin shawarwari na harkokin waje da halarci taruruka da harkoki na MDD da gwamnatoci da kungiyoyin kasashen duniya da kafa ofisoshin jakadanci da kula da 'yan diflomasiya da ba da jagora da daidaita ofisoshin ma'aikatun da ke a kasashen waje da harkokin waje na larduna jihohi da birane da horar da ma'aikatan harkokin waje.
Ministan harkokin waje na kasar Sin na yanzu shi ne Li Zhaoxing。
Kwamitin raya kasa da gyare gyare
Babban aikinsa shi ne shirya da aiwatar da babban shirin yalwata tattalin arzikin kasa da zaman al'umma da shiri na matsakaicin zango da na shekara shekara, da bincike harkokin tattalin arziki na gida da waje da ci gabansa don kyasta makomar tattalinh arziki, da bincike bincike muhimman maganganu da ke shafar lafiyar tattalin arzikin kasa da gabatar da shawarwari ga manufar daidaitawa da daidaita bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da shirya manyan ayyuka da shirya jarin da kasa za ta zuba da ba da jagora ga aikin yin amfani da jarin kasashen waje, ba da jaroga da duba rancen kudi da ba da jagora ga aikin yin amfani da jarin jama'a a wajen zuba jari ga ayyuka, da bincike takiti da manufa na zuba jari a kasashen waje da shirya manyan ayyukan da kasa za ta zuba jari da manyan ayyuka na jarin waje da manyan ayyukan da za a yi a kasashen waje, shirya da tsai da dokoki game da tattalin arzikin kasa da bunkasuwar zaman tarayya, da kokokin bude kofa ga kasashen waje da shiga aikin shirya dokokin da abin ya shafa.
Darektan kwamitin raya kasa da gyare gyare na yanzu shi ne Ma Kai
Ma'aikatar ciniki
A watan Maris na shekara ta 2003 ne aka kafa ma'aikatar nan Babban aiki na wannan ma'aikata shi ne tsara babban shiri da ka'ida da manufa na cinikin gida da waje da ci gaban gama kan tattalin arziki na kasashen duniya da dokokin gama kan tattalin arziki na kasashen duniya da zuba jarin baki, da tsara shirin yalwata cinikin cikin gida da bincike da gabatar da ra'ayin gyara tsarin cudanya, da tallafi kasuwoyi na birane da kauyuka, da bincike da tsara dokokin kasuwa da odar cudanya da karya kane kane da kangewar wurare da kafa hadadden tsarin kasuwa na bude kofa da gasa da oda, duba da bincike bukatun hajoji a kasuwa da shirya aikin daidaita muhimman hajoji da muhimman kayayyakin aikin kawo albarka, bincike da tsara dabarun sarrafa hajojin shigi da fici da shirya sunayensu, shirya yawan kayayyakin shigi da fici da bayara da takardun izni, shirya da aikata manufar tender ga hajojin shigi da fici da daidaita aikin kin kayayyaki masu dimbin yawa da za a sayar wa kasar Sin da sauran ayyukan da ke jibintar da cinikin waje da kafa tsarin daidaici na cinikin waje da shirya sauran ayyukan da ba da jagora ga masu sayar da kayayyaki ga kasashen waje.
Kwamitin soja na tsakiya
Kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne hukumar koli ta shugabancin soja da ke a karkashin shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Kwamitin nan yana kunshe da shugaba da mataimakin shugaba da manbobi. Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ne ke tsai da kwamitin soja na tsakiya wanda ke aiwatar da tsarin azzimar shugaba. Babban aikinsa shi ne shugabantar kungiyoyin masu damara na duk kasa.
Kwamitin soja na tsakiya na Jumhuriyar mutanen kasar Sin shi ne hukumar shugabancin soja ta kasa, ya shugabanci kungiyoyin masu damara na duk kasa. Kwamitin soja na tsakiya yana kunshe da shugaba da mataimakan shugaba da manbobi. Kwamitin soja na tsakiya yana aiwatar da tsarin azzimar shugaba. Majalisar wakilan jama'ara duk kasa ne ke zabar shugaba, zai dauki nauyi ga majalisar wakilan jama'ara duk kasa da zaunannen kwamitinta. Tsawon lokacin da kwamitin soja na tsakiya ke kan mukaminsa shi ne shekaru 5, amma ba a kayyade yawan tsawon lokaci ba.
Kungiyoyin masu damara na kasar Sin suna kunshe da rundunar sojan suncin jama'ar kasar Sin da rundunar 'yan sanda masu damara da sojoji farara hula. Rundunar sojan suncin jama'ar kasar Sin ita ce sojojin kullum na kasdar Sin, rundunar 'yan sanda masu damara tana kan aikin kiyaye zaman lafiya da kasa ta shirya mata da kiyaye zaman lafiyar zaman tarayya. Sojoji farar hula su ne jama'a masu damara da ba su bar gurbin aiki ba.
Shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kwamitin soja na tsakiya na Jumhuriyar mutanen kasar Sin shi ne Xi Jinping.
Kotun jama'a
Kotun jama'a hukuma ce ta yanke hukunci ta kasa. Kasa ta kafa kotun koli, larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da birane sun kafa babban kotu, wurare sun kafa kotunan wuri wuri. Kotun koli na jama'a shi ne hukumar yanke hukunci na koli na kasa, yana da ikon kai na yanke hukunci, kuma yana duba aiki na kotunan wuri wuri. Kotun koli na jama'a ya yi rahoto kan aiki ga majalisar wakilan jama'ar kasa da zaunannen kwamitinta. Majalisar wakilan jama'a ce ke nada shugaban kotun koli da mataimakinsa da kwamitin shari'a na kotun koli na jama'a.
Alhakin kotun koli na jama'a shi ne yanke hukunci ga wadanda ba su yarda da hukuncin da aka yanke a kotunan wuri wuri da tabbatar da hukuncin kisa. Bayan da ya bincike maganganun da aka yanke a kotunan wuri wuri, yana da ikon gyara su, kuma yana da ikon bayyana maganganun shari'a.
Shugaban kotun koli na jama'a shi ne Xiao Yang.
Ofishin bincike shari'a
Ofishin bincike shari'a hukuma ce ta dubawar dokoki. Ofishin bincike shari'a ya kammala aikinsa ne ta hanyar aiwatar da ikon duba shari'a. yana da ikon duba shari'a ga maganganun manyan laifufuka na cin amanar kasa da jawo wa kasa baraka, yana da ikon duba maganganun da ma'aikatun kiyaye zaman lafiya ke bincike, yana da ikon tsai da kudurin ko za a kama wadanda a ke tohumarsu, ko ba za a kai musu kara ba, kuma yana da ikon duba ma'aikatun kiyaye zaman lafiya da kotun jama'a da gidan yari da kurkuku ko suna yin harkokinsu bisa doka.
Ofishin bincike shari'a yana da ikon kai na bincike shari'a bisa dokoki, ba ruwansa da katsarandan na gwamnatoci da kungiyoyin zaman tarayya da sauran mutane, duk 'yan kasa suna da daidaici a gaban dokoki. Kasa ta kafa ofisoshin bincike shari'a na matakai 4 wato na wuri wuri da na tsakiya da na koli. Ofishin bincike shari'a na koli yana wakiltar kasa don aiwatar da ikon bincike shari'a cikin 'yancin kai, ya dau nauyi kai tsaye ga zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ar kasa, babbar dawainiyarsa ita ce shugabantar ofisoshin bincike shari'a na matakai daban daban don aiwatar da ikonsu na bincike shari'a don tabbatar da hadadden aikin aiwatar da dokoki bisa hanyar gaskiya.
Shugaban ofishin bincike shari'a na koli na yanzu shi ne Jia Chunwang.
>>[ Jam'iyyun kasar Sin ]
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kungiyar maduganci ce ta ajin ma'aikata, a sa'I daya kuma kungiyar maduganci ce ta jama'ar kasar Sin da al'ummar kasar Sin, cibiyar shugabanci ce ta sha'anin gurguzu mai surar musamman na kasar Sin. Tana wakiltar bukatun yalwatuwar karfin aikin kawo albarka na ci gaba, tana wakiltar manufar ci gaba ta al'adu mai ci gaba na kasar Sin, kuma tana wakiltar babbar moriyar yawancin mutanen kasar Sin.
Babban buri da makasudin karshe na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ne tabbatar da kwaminisanci. Catar jam'iyya ta tanada cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dauki Maksanci Leninanci da Mao Tsedong Tunani da hasashen Deng Xiaoping da muhimmin tunatin wakilci a fannoni 3 a kama da jagorar aikinta.
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafu ne a watan Yuli na shekara ta 1921. daga shekara ta 1921 zuwa shekara ta 1949, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shugabanci jama'ar kasar Sin don yin gwagwarmaya cikin mawuyaccen hali, ta ka da mulkin daulantaka da gargajiya da mahukuntan jarin hujja, kuma ta kafa Jumhuriyar mutanen kasar Sin. Bayan kafuwar kasa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta shugabanci jama'ar kabilun duk kasa don kiyaye 'yancin kai da kwanciyar hankali na kasa, ta yi nasarar juya zaman tarayyar kasar Sin daga sabuwar demokradiya zuwa gurguzu, kuma ta raya zaman gurguzu bisa shiri da babban mataki, ta sa kasar Sin ta samu matukar ci gaba da ba a taba gani a cikin tarihi ba a wajen tattalin arziki da al'adu.
Bayan da aka yi wa mahasusin kayayyakin aikin kawo albarka gyare gyare ta hanyar gurguzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi kuskure a wajen shugabantar aikin raya zaman gurguzu domin ba ta da isassun fasahohi. Daga shekara ta 1966 zuwa shekara ta 1976, kuma ta yi kuskuren ta da babban turun al'adu na dogon lokaci kuma daga duk fannoni.
A watan Oktoba na shekara ta 1976 an sa aya ga babban turun al'adu, kasar Sin ta shiga cikin wani sabon tsawon lokacin ci gaba. Bayan da aka yi cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an yi babban juyi mai ma'anar tarihi tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin. Tun daga shekara ta 1979, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fara aiwatar da manufar gyare gyare da bude kofa da Deng Xiaoping ya gabatar. Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar bude kofa da gyare gyare, kasar Sin ta samu babbar nasara a wajen tattalin arzikin kasa da ci gaban zaman al'umma, kasa ta yi manyan sauye sauye, shi ne lokacin da ya fi kyau tun bayan kafuwar kasa. Kuma lokaci ne da jama'a sun fi samun fa'ida.
Jam'iyyyar kwaminis ta kasar Sin tana nufin nuna himma a wajen yalwata dangantaka da kasashen waje don yin kokarin neman samun wani muhallin kasashen duniya sabo da bude kofa da gyare gyare da raya kasa ta zamani. A cikin harkokin kasashen duniya jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta tsaya kan manufar harkokin waje ta zaman lafiya cikin 'yancin kai da mallakar kai da kiyaye mallakar kai da mulkin kai. Ta yi adawa da darikar daular tasku da siyasar nuna karfi, kiyaye zaman lafiyar duniya da sa kaimi ga ci gaban 'yan Adam. Bisa tushen ka'idoji biyar na girmama wa juna mallakar kai da cikakken yankin kasa da rashin kai wa juna hari da rashin yin katsarandan a cikin harkokin gida da zaman daidaici da moriyar juna da yin zaman tare cikin lumana ne ta yalwata dangantaka da kasashen duniya. Bisa ka'idoji 4 na 'yancin kai da mallakar kai da cikakken daidaici da girmama wa juna da rashin yin katsarandan a cikin harkokin gida ne jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafa dangantakar aminci da jam'iyyun siyasa na kasashen duniya. A halin yanzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da dangantakar aminci da jam'iyyu fiye da 300 na kasashe fiye da 120.
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wata hadaddiyar jam'iyya ce da ta kafu bisa tsarinta da catarta kuma bisa ka'idar tsarin tattarawar demokradiya. "Catar Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin" ta tanada cewa, duk ma'aikata da manoma da sojoji da 'yan ilmi da sauran masu ci gaba na zaman al'umma wadanda suka kai shekaru 18 ga haifuwa, muddin sun amince da tsari da catar jam'iyya, kuma suna son shiga cikin aikin wata kungiyar jam'iyya tare da himma, kuma su aiwatar da kuduri na jam'iyya da biya kudin jam'iyya za su iya gabatar da rokonsu na neman shiga cikin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Kungiyioyin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin su ne babban taro na wakilan duk jam'iyya, kwamitin tsakiya, ofishin siyasa, zaunannen kwamiti na ofishin siyasa, sakatariya kwamitin tsakiya, kwamitin soja na tsakiya da kwamitin duba da'a na tsakiya. Ana kira babban taron wakilan duk kasa na jam'iyya a ko wane shekaru 5. A yayin da babban taron wakilan duk kasa ya ke a rufe, kwamitin tsakiya shi ne hukumar shugabancin koli ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da manbobinta kusan miliyan 70, babban sakatare na jam'iyya shi ne Xi Jinping.
Jam'iyyun demokrafiya na kasar Sin
A kasar Sin ban da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma akwai jam'iyyun siyasa 8 da a ke kira jam'iyyun demokradiya. Su ne, kwamitin turu na jam'iyyar Kwomingtang ta kasar Sin, kawancen demokradiya na kasar sin, kungiyar raya kasa ta demokradiya ta kasar Sin, kungiyar sa kaimi ga demokradiya ta kasar Sin, jam'iyyar demokradiya ta manoma da ma'aikata, jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin, kungiyar Jiusan, da kawancen ikon kai na demokradiya na Taiwan. Yawancinsu sun kafu ne a yayin da a ke yin yaki da maharan Japan da yakin neman suncin duk kasa. Jam'iyyun demokradiya suna nuna goyon baya ga shugabancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wannan dai zaba ce ta tarihi a cikin gama kai da su ke yi da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da yin gwagwarmaya tare cikin dogon lokaci. Jam'iyyun demokradiya suna more 'yancin siyasa da 'yancin kungiya da matsayin daidaici na dokoki da tsarin mulki ya tanada. Babbar ka'idar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yin gama kai da jam'iyyun demokradiya ita ce, zama cikin dogon lokaci, duba wa juna da nuna wa juna biyaya da yin arziki tare.
Jam'iyyun demokradiya ba jam'iyyun adawa ba ne, suna halartar harkokin siyasa. A halin yanzu, a cikin zaunannun kwamitoci na majalisun wakilan jama'a na matakai daban daban na kasar Sin da kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da ma'aikatun gwamnati da ma'aikatun tattalin arziki da al'adu da ilmi da kimiya da fasaha duk akwai 'yan jam'iyyun demokradiya da ke kan mukami. Misdali shugabanni na kwamitocin tsakiya na jam'iyyun demokradiya 8 suna kan mukamin mataimakan shugaban zaunannen kwamiti na majalisar wakilan jama'ara kasa da mataimakin shugaba na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa. A sa'I daya kuma jam'iyyun demokradiya suna yalwata manbobinsu, suna da kungiyoyinsu a larduna, jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da manyan birane da sauran birane na wurare daban daban.
Kwamitin turu na jam'iyyar Kwamingdang ta kasar Sin
Kwamitin turu na jam'iyyar Kwamingdan ta kasar Sin ya kafu ne a ran 1 ga watan Janairu na shekara ta 1948, rukunin demokradiya na jam'iyyar Kwamingdang ta kasar Sin da sauran 'yan kishin kasa ne suka kafa, hasali ma kawancen siyasa ne wanda ke yin kokarin raya zaman gurguzu mai surar musamman da hada kasar mahaifa. Tana da manbobi dubu 65, shugabar kwamitin tsakiya ita ce He Luli.
Kawancen demokradiyar kasar Sin
Kawancen demokradiyar kasar Sin ya kafu ne a watan Maris na shekara ta 1941, a wancan lokaci ana kira shi kawancen rukunonin siyasa na demokradiya na kasar Sin, a shekara ta 1944 ne an gyara sunansa da ya zama kawancen demokradiya na kasar Sin. Shi kawancen siyasa ne da ke kunshe da 'yan ilmi masu aikin koyarwa da ma'aikatan gurguzu da 'yan kishin kasa da ke nuna goyon baya ga siyasar gurguzu, jam'iyyar siyasa ce da ke bauta wa zaman gurguzu. Kawancen nan yana da manbobi dubu 156. Shugaban kwamitin tsakiya na yanzu shi ne Ding Shisun.
Kungiyar raya kasa ta demokradiya ta kasar Sin
Kungiyar raya kasa ta demokradiya ta kasar Sin ta kafu ne a watan Disamba na shekara ta 1945. Kungiyar nan musamman tana kunshe da masu masana'antu na al'ummar kasar Sin da 'yan ilmi da ke da hulda da su. Tana da manbobi dubu 85. Shugaban kwamitin tsakiya na yanzu shi ne Cheng Siwei.
Kungiyar sa kaimi ga demokradiyar kasar Sin
Kungiyar sa kaimi ga demokradiyar kasar Sin ta kafu ne a watan Disamba na shekara ta 1945. manbobinta musamman tana kunshe da 'yan ilmi da ke yin aikin koyarwa da al'adu da dabi da kimiya da sauran aiki. Tana da manbobi dubu 81. shugaban kwamitin tsakiya na yanzu shi ne Xu Jialu.
Jam'iyyar demokradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin
Jam'iyyar demokradiya ta manoma da ma'aikata ta kasar Sin ta kafu ne a watan Agusta na shekara ta 1930. Jam'iyyar nan kawancen siyasa ne musaman da ke kunshe da 'yan ilmi na likitanci da magungunan sha da kimiya da fasaha da ilmi da ma'aikatan gurguzu da 'yan kishin kasa masu nuna goyon baya ga gurguzu. Tana da manbobi fiye da dubu 80. shugaban kwamitin tsakiya na yanzu shi ne Jiang Zhenghua.
Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin
Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin ta kafu ne a watan Oktoba na shekara ta 1925. jam'iyyar nan musamman tana kunshe da Sinnawa 'yanb kaka gida da danginsu. Tana da manbobi dubu 29. Shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar nan shi ne Luo Haocai.
Kungiyar ilmi ta Jiusan
Kungiyar nan ta kafu ne a watan Mayu na shekara ta 1946. Kungiyar nan musamman tana kunshe da 'yan ilmi na kimiya da fasaha da ba da ilmi da likitanci. Tana da manbobi fiye da dubu 80. Shugaban kwamitin tsakiya na yanzu shi ne Han Qide.
Kawancen ikon kai na demokradiya na Taiwan
Kawancen ikon kai na demokradiya na Taiwan ya kafu ne a watan Nowamba na shekara ta 1947. Mutanen Taiwan da ke zaune a nan babban yanki ne suka kafa shi. Kawancen siyasa ne da ke kunshe da ma'aikatan gurguzu da 'yan kishin kasa masu nuna goyon baya ga gurguzu. Yana da manbobi dubu daya da 800. Shugaban kwamitin tsakiya na kawancen nan shi ne Zhang Kehui.
>>[Membobin zaunannen kwamiti na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na J.K.S na yanzu]