Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2018-07-02 13:32:15    
Bolton: Amurka za ta gabatar wa Koriya ta Arewa tsarin kawar da makaman kare dangi

cri
Mashawarci ga gwamnatin Amurka game da tsaro John Bolton, ya ce gwamnatin shugaba Trump na shirin gabatarwa Koriya ta arewa wani shiri mai kunshe da matakan da take fatan Koriyar ta arewa za ta aiwatar, domin cimma nasarar kawo karshen makaman kare dangi a zirin Koriya.

Bolton wanda ke zantawa da kafar talabijin ta CBS, ya ce Amurka ta tsara shirin da zai dace da burin da aka sanya gaba, kuma a cewar sa, nan gaba kadan sakataren wajen Amurkan Mike Pompeo, zai zanta da mahukuntan Koriya ta arewan game da wannan lamari.

Mr. Bolton wanda a baya ya taba zamowa wakilin Amurka a MDD, ya ce kunshin shirin na kasarsa wanda kwararru suka tsara shi, ya fayyace dukkanin matakan da suka dace a bi, wajen kwance damarar nukiliyar koriya ta arewa, tare da lalata makaman ta masu linzami cikin shekara guda, muddin kasar ta ba da hadin kai. (Saminu Hassan)