Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-01-25 15:25:53    
Za a kira taron sake farfado da kasar Haiti bayan girgizar kasa

cri
Kasar Haiti da ke abkuwar girgizar kasa mai tsanani tana jawo hankalin mutanen duniya sosai, yanzu, ayyukan ba da ceton agaji da gamayyar kasa da kasa suka yi sun sami sakamakon farko, sa'anan kuma halin da birnin Port Au Prince , hedkwatar kasar ke ciki ya sami kyautatuwa daga rikicin da ta faru a farkon girgizar kasa zuwa lokacin samun odar . A ran 23 ga wannan wata, shugaban kasar Haiti ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kafa rundunar sojojin da suke sanya huluna masu launin ja don kula da harkokin jinkai da kuma ba da taimako ga gwamnatin kasar Haiti wajen rarraba kayayyakin jinkai. A ranar 24 ga wannan wata, ministan harkokin waje na kasar Canada ya shelanta cewa, za a kira taron sake farfado da kasar Haiti a ranar 25 ga wannan wata a birnin Montreal na kasar Canada.

Kwanan baya, gwamnatin kasar Haiti ta sanar da cewa, an kawo karshen ayyukan yin cigiya bayan girgizar kasa. Babban aikin da za a yi shi ne zaunar da wadanda suka rasa gidajensu. A ranar 22 ga wannan wata, mutanen Haiti da yawansu ya kai darurukan dubu sun tashi daga birnin Port Au Prince zuwa sauran wurare don neman samun gidajensu na wucin gadi, kuma odar birnin Port AU Prince yana nan yana farfadowa. Gwamnatin kasar ita ma ta bayar da lambobin waryar tarho da adireshin internet don ba da taimako ga mutanen Haiti da ke zama a kasashen ketare wajen samun labarin dangoginsu. Gwamnatin kuma za ta dauki matakai don ba da taimako ga wadanda suke shan wahalhalun bala'in da suka samu kudi da kayayyakin da dangoginsu suka aika musu daga kasashen ketare, wasu kungiyoyi ma sun tafi kauyukan kasar Haiti don ba da taimako ga mutanen wurin, amma wadanda ba su tashi daga birnin Port Au Prince har wa yau dai suna kasancewa cikin mawuyacin hali na yin fama da karancin abinci da magungunan sha da sauransu.

A ranar 23 ga wannan wata, shugaban kasar Haiti ya kirayi Majalisar Dinkin duniya da ta kafa wata runduna sojojin da ke sanyan huluna masu launin ja don kula da harkokin jinkai. Shugaban kasar Rene Garcia Preval

Ya bayyana cewa, yanzu gwamnatin Haiti ba ta da karfin rarraba kayayyakin jinkai, shi ya sa tana dogara da taimako daga Majalisar Dinkin duniya don maye gurbin gwamnatin Haiti wajen ayyukan ba da ceton bala'in.

Amma, wasu ra'ayoyin jama'a suna ganin cewa, matakin da gwamnatin Haiti ta dauka ya nufin zaunar da karfufukan kasashen waje a kasar cikin dogon lokaci, ya kamata gwamnatin Haiti ta aiwatar da matakin a tsanake. Wasu kasashe sun bayyana a fili cewa, mai yiyuwa ne matakin zai mayar da kasar Haiti za ta zama wani sansanin soja na kasar Amurka daban a kasashen ketare.

A ranar 24 ga wannan wata, ministan harkokin waje na kasar Canada ya shelanta cewa, taron da za a yi a ranar 25 ga wannan wata kan batun farfado da kasar Haiti bayan girgizar kasa zai mai da hankali ga kimanta hasarar da aka samu sakamakon girgizar kasa a kasar Haiti da kuma tabbatar da ayyukan ba da taimakon jinkai da ayyukan sake farfado da kasar Haiti da kuma yin share fage da sake kiran babban taron kasa da kasa kan batun kasar Haiti.

Jaridar "The Washington Post" ta gabatar da wata shawara cewa, ya kamata a kafa wani asusun farfado da kasar Haiti don kula da taimakon agaji da kasashe da kungiyoyi daban daban na duniya suka samar da shi don ba da hidima ga ayyukan farfado da kasar Haiti da ba da tabbaci ga kasar wajen samar mata da kudaden sake farfado da ita.

An bayar da cewa, yawan mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasa a kasar ya riga ya wuce dubu 110 tare da mutanen da yawansu ya kai dubu 610 da suka rasa gidajensu.(Halima)