Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2010-01-16 18:07:28    
Kasar Sin ta samu babbar moriya wajen aikin tsare ruwa na Sanxia bisa kogin Yangtse a shekarar 2009

cri
Shekarar 2009 wata shekara ce da kasar Sin ta soma zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin ruwa wato babban aikin tsare ruwa na Sanxia bisa kogin Yangtze, kuma an samu moriya wajen fama da ambaliyar ruwa da bada wutar lantarki da zirga-zirgar jiragen ruwa da sauran fannoni.

A lokacin ambaliyar ruwa na shekarar 2009, an yi cikon ruwa da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekaru 5 da suka wuce a kogin Yangtze, kogi mafi girma na kasar Sin, yawan ruwan da aka adana cikin matarin ruwa na Sanxia ya kai kubik mita biliyan 4.27, hakan ya sassata matsin lambar da aka yi wa mutanen da ke bakin kogin wajen fama da ambaliyar ruwa.

Ban da wannan kuma babban aikin tsare ruwa na Sanxia ya kyautata halayen zirga-zirgar jiraren ruwa sosai. Yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a shekarar 2009 ta hanyar mashigin ruwa ta Sanxia ya kai ton miliyan 74.26, wato ya karu da kashi 8.5 cikin 100 bisa na shekarar 2008. (Umaru)