Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-12-28 10:16:24    
Kasashen Afrika sun ci nasarar babban zabe cikin lami lafiya a shekarar da muke ciki

cri
Shekarar 2009 shekara ce da aka yi babban zabe a nahiyar Afrika. A cikin duk tsawon shekarar, da akwai kasashe 13 da suka yi babban zabe, a cikin watan Oktoba da watan Nuwamba kawai, an samu sabbin gwamnatoci na kasashe 6. A shekarar 2009, an aiwatar da ayyukan share fage da kada kuri'un zabe yadda ya kamata ba tare da abkuwar hargitsi mai tsanani tamkar yadda kasar Kenya da Madagascar da Zimbabuwei da sauran kasashe suka yi ba a yayin da aka yi babban zabe, wannan ya canja tunani da aka yi wa mutane game da samun rikice-rikice a yayin da ake gudanar da babban zabe a kasashen Afrika.

Kodayake bambancin halin da ke kasancewa a tsakanin kasashe daban daban da suke yin babban zabe a shekarar, kuma na da bambancin dalilan da aka samu nasarar cin zabe, amma ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, dalilan da aka sami lafa a shekarar da kasashen Afrika suke yin babban zabe na da fannoni uku:

Na farko, jam'iyyu da 'yan takarar zabe wadanda suka ci nasarar zabe sun fi samun fiffiko a yayin da ake yin zabe , kuma abokan gabansu ba su iya kawo kalubale gare su ba, shi ya sa ba a sami babbar gardama domin sakamakon zabe ba.

Bari mu gabatar da misali game da kasar Afrika ta kudu , kungiyar ANC da ke cin nasarar zabe ta ba da babban karfin tasiri a ko'ina a kasar Afrika ta kudu, musamman ma ta sami goyon baya daga mutane bakake da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari bisa na yawan mutanen kasar. Amma jam'iyyar dimokuradiya wato babbar jam'iyyar hamayya ta kasar ba ta da karfi sosai ba, kuma wata babbar jam'iyya daban ita ma ba ta da karfin yin kalubale ga jam'iyyar ANC ba.

Na biyu, jam'iyyu da wadanda suka ci zabe dukkansu suna aiwatar da manufofin raya kasa ta hanyar yunkurin bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a, saboda haka, sun sami goyon baya daga magoyan bayansu, wato daga yawancin fararen hula.

Na uku, jam'iyyu da wadanda suka suka ci zabe sun sami babban goyon baya daga kasashen yamma.

A shekarar da muke ciki, koda yake an yi babban zabe a kasashen Afrika yadda ya kamata, amma sabon mulki zai gamu da kalubale iri iri da yawa.

Bari mu dauki misali game da kasar Botswana, saboda kasar ta dogara da sana'ar li'u-lu'u, shi ya sa ta gamu da mugun tasiri a yayin da ake abkuwar ricikin kudi a duniya, shi ya sa sabuwar gwamnatin ta gamu da kalubale a sakamakon samun karin marasa aikin yi da kara bambancin da ke tsakanin masu hannu da shuni da masu fama da talauci. Sabuwar gwamnati ta gabatar da ra'ayin kubutar da kanta daga dogarawar da ta yi da lu'u- lu'u a yayin da take shiga takarar zabe, da kuma sa kaimi ga raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban, amma, yadda za ta sami manufofi da matakai masu amfani , ana bukatar lokacin gwaji.

A shekarar 1994, kasar Afrika ta Kudu ta kawar da tsarin nuna bambancin kabila, sa'anan kuma, kungiyar ANC ta yi nasarar cin zabe a karo hudu a jere, amma a wannan karo, kungiyar ba ta sami kuri'u kashi biyu cikin kashi uku ba.

Babban dalilin da ya sa kungiyar ANC ta rage karfin tasirinta shi ne, a cikin kungiyar, ya kasance da sabane-sabane da yawa, a gaban shugaba mai ci Zuma , babban kalubale da yake fuskata shi ne yadda zai hada kai da mambobin kungiyar.

Kasashen Afrika sun ci nasarar babban zabe a shekarar 2009, wannan ya ba da misali ga kasashen da zai yi babban zabe a shekara mai zuwa, kuma zai ba da babban taimako ga cin daidaito manufar babban nahiyar Afrika don ta zama Afrika mai jituwa.(Halima)