Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-30 11:24:27    
Kungiyar WHO ta gabatar da sabuwar shawarar shawo kan ciwon sida da yin rigakafi da shi

cri
A ran 30 ga wannan wata, kungiyar WHO ta gabatar da sabuwar shawarar shawo kan ciwon sida da yin rigakafinsa, kuma a karo na farko ne ta gabatar da shawarar yin amfani da magungunan shawo kan kwayoyin yadada cututukan sida a lokacin da jariri ke shan nono daga mahaifiyarsa don shawo kan cutar sida da mahaifiya da jariri suka riga suka kamu da su, duk domin yin rigakafin yadada cutar a tsakanin mahaifiya da jariri.

A wannan rana, kungiyar WHO ta bayar da sanarwa, inda ta bayyana cewa, a yayin da ranar yaki da ciwon sida ta duniya ke kusantowa ba da dadewa ba, kungiyar ta gabatar da shawarar warkar da mutane balagai da samari da yara wadanda suka kamu da kwayoyin yadada cututukan sida tun da wuri ta yadda masu kamuwa da ciwon sida za su iya samun magunguna cikin sauri da kuma tsawaita lokutan yin amfani da magungunan shawo kan cututukan sida da suke yaduwa a tsakanin mahaifiya da jariri . Game da shawarar yin amfani da magungunan shawo kan cututukan sida don yaki da cututukan sida masu yaduwa a tsakanin mahaifiya da jariri, a karo na farko ne kungiyar ta gabatar da ita a cikin shawarwarin da abin ya shafa.

A cikin sanarwar, mataimakin babban direktan kungiyar WHO mai kula da harkokin cutar sida da cutar fuka da cutar zazzafin cizon sauro Hiroki Nakatani ya bayyana cewa, an gabatar da wadannan sabbin shawarwari ne bisa sabbin abubuwan kimiyya, in za a yi amfani da su a ko'ina, to za a iya tsawaita rayukkan mutanen da suke zama a yankunan da suka samu wadanda suka kamu da cutar da yawa da kuma kara inganta lafiyarsu.

Kungiyar WHO ta bayyana cewa, a shekarar 2006, kungiyar ta riga ta bayar da shawarwari kan lamarin, inda ta soma aiwatar da tsari game da rage lokutan warkar da cutar sida, a wancan lokaci, masu  cutar sun riga sun bayyana alamar kamuwar da cutar.

A fannin yin amfani da fasahar shawo kan kwayoyin yadada cututukan sida a tsakanin mahaifiya da jariri, kungiyar WHO ita ma ta gyara shawarar da aka bayar a shekarar 2006, wato an yi amfani da magunguna daga makwanni 28 da aka samu ciki zuwa ranar nakuda, yanzu fa ana yin amfani da magunguna daga makwanni 14 da aka samu ciki zuwa ranar karshen da jaririn ke shan nono daga mahaifiyarsa . kungiyar ta bayyana cewa, a wani fanni, mahaifiya tana iya yadada cutar sida ga jariri a lokacin da jaririn ke shan nono daga mahaifiyarsa, a wani fanni daban, in an ciyar da jariri ba tare da shan nonon mahaifiyarsa ba, to mai yiyuwa ne yaririn zai rasa abubuwan kara kuzari ga jikinsa da kuma gamuwa da hadarin kamuwa da sauran cututuka masu yaduwa, wani sabon gwajin da aka yi ya bayyana cewa, in an yi amfani da magungunan shawo kan cututukan sida masu yaduwa lokacin da mahaifiya ta ba da nono ga jariri, to za a iya rage yawan wadanda suke kamuwa da cutar da kashi 5 cikin dari, wato za a rage yawan yara da za su mutu a sakamakon cutar sida.

Sa'anan kuma, kungiyar ta samar wa kasashe daban daban shawarar da su daina yin amfani da magani mai suna Stavudine a kai a kai, saboda maganin na haddasa matsaloli ga wadanda suka sha.

A sa'I daya kuma, kungiyar WHO ta bayyana cewa, sabuwar shawarar da ta gabatar ta sami wasu kalubale, maganin da ake yin amfani da shi na kara karuwa, wannan ya bayyana cewa, wadanda suka yi amfani da maganin su ma suna ta kara karuwa, wani babban kalubale gare mu shi ne, yaya za a shawo kan mutane don su je asibiti don ganin likita kafin su nuna  alamar kamuwa da ciwon.(Halima)