A ran 9 ga watan, an rufe taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, inda aka zartas da "Sanarwar Sharm el Sheikh ta dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka" da "Shirin Daukar Matakai na Sharm el Sheikh a tsakanin shekara ta 2010 da ta 2012". Bayan taron, Mr. Yang Jiechi, ministan harkokin wajen kasar Sin da Mr. Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin da kuma Mr. Ahmed Aboul Gheit, ministan harkokin wajen kasar Masar sun shirya wani taron manema labaru kan hadin gwiwa, inda suka sanar da ci gaban da aka samu a gun taron da matakan da za a dauka domin tabbatar da samun irin wadannan ci gaba.
A gun taron manema labaru da aka shirya, da farko dai, Mr. Ahmed Aboul Gheit, ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewa, nasarar da aka samu a gun wannan taro ta alamanta cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna da fatan kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Takardun da aka zartas da su a gun taron sun shafi batutuwa iri iri da ke jawo hankalin kasashen Afirka. Mr. Gheit ya ce, "A gun taron, an zartas da muhimman takardu biyu, wato 'Sanarwar Sharm el Sheikh ta dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka' da 'Shirin daukar matakai na Sharm el Sheikh a tsakanin shekara ta 2010 da ta 2012' . A cikin sanarwar, kasar Sin ta bayyana fatanta na kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka, a waje daya, kasashen Afirka sun kuma bayyana cewa za su ci gaba da kara hada gwiwa tsakaninsu da kasar Sin a fannoni daban daban. 'Shirin daukar matakai na Sharm el Sheikh a tsakanin shekara ta 2010 da ta 2012' shi ma yana kunshe da abubuwa da yawa, da suke shafar harkokin siyasa, tattalin arziki, zaman al'umma, aikin gona, tabbatar da samar da isashen abinci mai inganci da zuba jari ga juna da na bankuna da ayyukan yau da kullum da dai makamatansu."
Game da batun dumamar yanayin duniya da ke jawo hankalin kasashe daban daban, musamman kasashen Afirka da tattalin arzikinsu bai samu ci gaba ba, an fi mai da hankali a gun wannan taro. Mr. Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya jaddada cewa, "Yanzu, dumamar yanayin duniya ya riga ya zama abin gaskiya. Galibin kasashen duniya suna ganin cewa, an samu sauyawar yanayin duniya ne sakamakon abubuwan dumamar yanayin duniya da wasu kasashe suka fitar tun shekaru 100 da suka gabata. Sakamakon haka, Jama'ar kasar Sin da na kasashen Afirka dukkansu kasashe ne da ke fama da illar da aka yi musu sakamakon dumamar yanayin duniya."
A game da batun Sudan da ke jawo hankalin kasashen Afirka, Mr. Yang Jiechi ya bayyana cewa, matsayin da kasar Sin ke dauka yana daidai da na kungiyar tarayyar kasashen Afirka da na kawancen kasashen Larabawa. Mr. Yang ya ce, "Kasar Sin zaunanniyar mamba ce a kwamitin sulhu na M.D.D. Mu kan mai da hankali da kuma tsayawa tsayin daka kan matsayin sauke nauyin da ke kanmu wajen kiyaye moriyar kasashe masu tasowa da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba a shiyya-shiyya da kuma a duk duniya. Mun girmama 'yantattar kasa da cikakken yanki da ikon mulkin kasa na kasar Sudan, ba za mu tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sudan ba. A waje daya, za mu ci gaba da samar da taimako ba tare da son kai ba ga dukkan jama'ar Sudan, ko suna zaune a kudu, ko a arewa ko a yankin Darfur na kasar." (Sanusi Chen)
|