Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 16:05:13    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi daga Beijing domin kai ziyara a Malaysiya da Singapore da kuma halartar taron koli na kungiyar APEC

cri

A ran 10 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya tashi daga birnin Beijing, domin fara ziyarar kwanaki 6 a kasashen Malaysiya da Singapore, da kuma halartar kwarya-kwaryar taron shugabanni a karo na 17 na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta kasashen Asiya da tekun Pacific wato APEC, wanda za a shirya a kasar Singapore.

Da aka tabo magana kan ma'anar ziyarar Hu a kasashen Malaysiya da Singapore, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin minista Hu Zhengyue ya ce,

'Wannan ya zama karo na farko ne Hu Jintao ya kai ziyarar aiki a kasashen Malaysiya da Singapore a matsayin shugaban kasar Sin, haka kuma wannan ta zama ziyarar da wani shugaban kasar Sin ya sake kai wa kasashen biyu bayan shekaru 15 da suka gabata, sabo da haka wannan ziyara tana da muhimmiyar ma'ana matuka wajen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da wadannan kasashen biyu da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN da suke ciki.'

Daga ran 14 zuwa 15 ga wata, za a shirya kwarya-kwaryar taron shugabanni a karo na 17 na kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta kasashen Asiya da tekun Pacific wato APEC a kasar Singapore. Gamayyar kasa da kasa na mai da hankali sosai kan sakamakon da za a samu daga wannan taro a karkashin rikicin kudi na duniya.

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin minista He Yafei ya bayyana cewa,

'Na farko, kasar Sin tana fatan za a gabatar da shirin hadin gwiwa wajen tinkarar rikicin kudi na duniya, da maido da bunkasuwar tattalin arziki. Na biyu, kasar Sin tana fatan za a bayyana ra'ayi a fili wajen yaki da yin kariyar cinikayya da zuba jari, da nuna goyon baya ga shawarwari a karo na Doha. Na uku, kasar Sin tana son kara gaggauta dunkulewar shiyyarmu wuri daya a fannin tattalin arziki. Na hudu, kasar Sin tana fatan za a ci gaba da yin gyare gyare kan tsarin kungiyar APEC, domin kara samun karfin takara.'

Malamin cibiyar nazarin dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa ta jami'ar Beijing minista Zhu Feng yana ganin cewa, matakan diplomasiyya da shugaban kasar Sin ya dauka a cikin shekarar bana sun bayyana cewa, kasar Sin ta shiga cikin hadin gwiwa a tsakanin shiyya shiyya da kasashen duniya cikin yakini, musamman ma a karkashin rikicin kudi na duniya, wadannan matakai sun bayyana siffar kasar Sin a matsayin wata babbar kasa da ke sauke kokarin sauke nauyi da ke kanta. Ya ce,

'Jawaban da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi sun burge dukkan kasashen duniya, ciki har da jawaban da ya yi a babban taron MDD sau da dama, da taron koli na rukunin G20 sau biyu. Shugaba Hu Jintao ya kan mai da hankali sosai kan tattalin arziki yayin da yake ziyara a kasashen waje, wannan ya kara daga matsayin kasar Sin a duk duniya, da kuma bayyana cewa, kasar Sin tana sauke nauyi da ke kanta.'(Danladi)