Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-10 10:34:58    
A gaskiya dai ziyarar Wen Jiabao a kasar Masar ta sa kaimi ga kara bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Masar da Larabawa da Afrika

cri
A ranar 9 ga wannan wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gama ziyararsa ta aiki a kasar Masar da kuma bayan halartarsa a taron ministoci na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, sai ya komo birnin Beijing. Kafin komowarsa, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi wanda ke rufa masa baya a gun ziyarar ya karbi ziyarar da manema labaru suka yi masa, inda ya bayyana sakamakon da aka samu a gun ziyarar. A ganinsa, ziyarar Wen Jiabao a kasar Masar ziyara ce ta sa kaimi ga yin tattaunawa kan wayewar kai , kuma ziyara ce ta kara raya hadin gwiwar sada zumunta a hakika, a gaskiya dai ziyarar ta sa kaimi ga kara raya dangantakar zumunci da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A cikin kwanaki biyu da yake zama a kasar Masar, Wen Jiabao ya kai da kawowa tsakanin birnin Alkahira da birnin Sharm El Sheikh, shirye-shiryen ziyara na da yawan gaske, yawan ayyukan da ya yi har ya kai 36. daga cikinsu, abu mafi jawo hankalin mutane shi ne halartarsa a bikin bude taron ministoci na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tare da shugaban kasar Masar Muhammed Hosni Mubarak da sauran shugabanni 20 na kasashen Afrika. A ganin Yang Jiechi, bisa halin da ake ciki na fama da rikicin kudi a duk duniya, firayim ministan kasar Sin ya kai ziyara a kasar Masar, wannan abu na da ma'ana mai muhimmanci sosai, ya bayyana cewa, mu ma muna mai da hankali sosai ga taron, duk saboda a cikin al'amuran kasashen duniya, a wani fanni, ya kamata a shawo kai kan rikicin kudi na kasa da kasa, a wani fanni daban kuma, ya kamata a warware matsalar sauye-sauyen yanayi. Kasashen Afrika su da kansu suna fuskantar matsaloli da yawa, kuma ana fatattake su a wasu fannoni , saboda haka, suna fama da wahalhalu da yawa, a daidai wannan lokaci, firayim ministan kasar Sin ya tafi Afrika, a gaskiya dai wannan ya sa ran alheri ga kasashen Afrika da jama'arsu.

Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar da sabbin matakai na sa kaimi ga raya hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma ya sanar da shawararsa ta kafa huldar abokantaka ta maganin sauye-sauyen yanayi a tsakanin Sin da Afrika, kuma kasar Sin za ta samar da rancen kudi da yawansa ya kai kudin Amurka dala biliyan 10 ga kasashen Afrika bisa gatanci, har ma ta samar wa kasashen Afrika da suke fama da talauci sosai gatanci na rashin buga haraji ko kadan ga kashi 95 cikin dari na kayayyakin da suka fitar, Mr Yang ya ci gaba da cewa, a ganina, halayen musamman na sabbin matakai 8 sun hada da mai da hankali ga gina manyan ayyuka, sa'anan kuma a mai da hankali ga zaman rayuwar jama'a da kiyaye muhalli da kara daga karfinsu na raya su da kansu. Na tabbatar da cewa, a cikin shekaru uku masu zuwa,hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zai kara habakawa.

Kasar Masar kasar farko ce da ta kulla huldar diplomasiya da kasar Sin a cikin kasashen Larabawa, muhimmin aikin da Wen Jiabao ya yi a gun ziyarar shi ne kara sa kaimi ga raya hadin gwiwar sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, Wen Jiabao ya kuma gana da babban sakatare na kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Amr Mahmoud Moussa, kuma ya bayar da muhimmin jawabi, Yan Jechi ya kuma bayyana cewa, a cikin laccar da Wen Jiabao ya yi, ya karfafa cewa, ya kamata a girmama ire-iren wayewar kai. (Halima)