Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 18:33:58    
Sin da Afirka sun samu sabon mafari na yin hadin gwiwa

cri
A yayin bikin bude taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar, Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya sanar da sabbin matakai 8 na yin hadin gwiwa da Afirka da Sin za ta dauka a shekaru 3 masu zuwa, wadanda suka shafi yanayi da makamashi da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da dai sauransu. Wadannan hakikanin matakai sun kara kyautata dangantakar abokantaka da yin hadin gwiwa ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare, sun kuma sanya Sin da Afirka su shiga sabon mataki bisa halin da suke ciki, bayan da suka kaddamar da hadin gwiwarsu yau da shekaru 50 ko fiye da suka wuce.

A sakamakon rikicin kudi da ke caza kan al'ummar kasa da kasa sosai a halin yanzu, Sin da Afirka dukkansu na fuskantar tsananin kalubaloli. Duk da haka, kasar Sin na ci gaba da daukar matakai 8 da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gabatar dangane da yin hadin gwiwa da Afirka a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka yau da shekaru 3 da suka wuce. Ta cika alkawarinta a tsanake na tabbatar da yawan kayayyakin da ake samarwa da guraban aikin yi da yawan jarin da ake zubawa. Za ta samu nasarar gudanar da dukkan matakai 8 a karshen wannan shekara. Game da wannan, Rupiah Banda, shugaban kasar Zambia ya nuna babban yabo da cewa, shaidu sun nuna cewa, kasar Sin aminiya ce!

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne in an kwatanta da matakai 8 da aka kaddamar da su yau da shekaru 3 da suka wuce, sabbin matakai 8 da Mr. Wen ya sanar da su sun hada da sabbin abubuwa. Da farko, Sin da Afirka sun kara fadada fannonin yin hadin gwiwa. Baya ga harkokin tattalin arziki da suka dade suna hada kansu a kai, Sin da Afirka za su yi hadin gwiwa a fannonin sauyawar yanayi da raya kimiyya da fasaha da yin mu'amala a tsakanin mutane. Wannan ya nuna cewa, Sin da Afirka sun habaka hadin gwiwarsu bisa halin da ake ciki, sun kara kyautata dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. Kazalika kuma, sabbin matakai 8 sun nuna cewa, Sin ta kara sa muhimmanci kan raya kwarewar jama'ar Afirka ta raya kasa da kansu da kuma samun dawamammen bunkasuwarsu. Sin za ta kaddamar da shirin abokai ta fuskar kimiyya da fasaha domin inganta hazakar Afirka na biyan bashi, za ta kuma kara raya albarkatun kwadago da yin hadin gwiwa da Afirka a harkokin ba da ilmi da kuma kara yin mu'amala a tsakanin jama'arsu. Nufin Sin na daukar wadannan sabbin matakai 8 shi ne taimakawa Afirka ta sami karin kwarewa ta a fannin bunkasuwa da gina kanta, ta haka Afirka za ta iya samun bunkasuwa mai dorewa da kanta sannu a hankali, a maimakon dogaro da samun taimakon kasashen waje kawai.

Tarihi da shaidun gaskiya sun nuna cewa, Sin da Afirka aminai ne, kuma abokai, haka kuma, su 'yan uwa ne sosai. A cikin shekaru 3 ko fiye bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, Sin da Afirka suna ta yin kokari domin kyautata dangantakar abokantaka ta sabon salo, wato yin zaman daidai wa daida da nuna amincewa da juna ta fuskar siyasa, da yin hadin gwiwa domin samun nasara tare ta fuskar tattalin arziki, da kuma yin mu'amala da yin koyi da juna ta fuskar al'adu. Kokarinsu ya zurfafa zumuncinsu tare da sa kaimi kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Yawan mutanen Sin da na Afirka ya wuce sulusin jimillar mutanen duniya gaba daya. Inganta hadin gwiwa a tsakaninsu ya ba su taimako sosai tare da ba da taimako wajen hada kan kasashe masu tasowa, da kuma kafa sabon tsarin zama mai adalci a harkokin siyasa da tattalin arziki na duniya.

Akwai dalilin da ya sa a gaskata cewa, taron Sharm el Sheikh zai kasance sabon mafari a tarihin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Sa'an nan kuma, tabbas ne sabbin matakai 8 da kasar Sin ta gabatar za su sa kaimi ga Sin da Afirka da su shiga sabon mataki na yin hadin gwiwa.(Tasallah)