Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-09 16:25:21    
Sabbin matakan da Sin za ta dauka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika za su kara mai da hankali kan sha'anin kyautata zaman rayuwar al'umma

cri
A ranar 8 ga wata, an yi taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Sharm El Sheikh da ke bakin teku a kasar Masar. Firaministan Sin Wen Jiabao ya halarci wannan taro, kuma a cikin jawabin da ya yi a gun bikin kaddamar da taron, ya gabatar da sabbin matsakan da Sin za ta dauka wajen ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. A gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, firaministan Sin ya bayyana cewa, sabbin matakan da gwamnatin Sin za ta dauka wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika za su kara kyautata zaman rayuwar al'umma.

Yayin da manema labaru suke zantawa da firaministan Wen kan bambancin matakan da gwamnatin Sin ta gabatar wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar da kasashen Afrika a wannan gami da matakan da ta gabatar a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Mr. Wen ya bayyana cewa,"Idan aka kwatanta bambancin matakan da Sin ta gabatar, ana ganin dukkansu domin kara kwarewar kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa. Sabbin matakan da Sin za ta dauka za su kara kyautata zaman rayuwar al'umma, kuma za su mai da hankali wajen aikin gona da manyan ayyuka da inganta aikin kiyaye muhalli da karfafa sha'anin kiwon lafiya da ilmi da dai sauran ayyukan da ke shafar zaman rayuwar jama'a."

Firaministan Wen ya musanta zargin da aka yi wa kasar Sin, wai ta kwace albarkatun ma'adinai da gurbata muhalli da gudanar da matakan mulkin mallaka na sabon nau'i a nahiyar Afrika.Mr. Wen ya bayyana cewa,"Idan aka tabo maganar kwace albarkatun ma'adinai da gudanar da matakan mulkin mallaka na sabon nau'i a nahiyar Afrika, na riga na ji wadannan maganganu, amma idan aka fahimci tarihin kasar Sin, ana iya gane cewa, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, ba wai tana tasowa daga yanzu ba ne, kuma kafin rabin karnin da ya wuce, Sin ta fara kulla dangantakar tsakaninta da kasashen Afrika, a halin da ake ciki yanzu, Sin ta ba da gudummawa ga kasashen Afrika. Misali, bayan shekarar 2006 ya zuwa yanzu, yawan cinikin da kasar Sin take zuba a kasashen Afrika ya riga ta karu daga dalar Amurka biliyan 50 zuwa biliyan 100. kana a sha'anin makamashi, yawan man fetur da Sin ta shigo da shi daga kasashen Afrika, ya kai kimanin kashi 13 cikin kashi 100 daga cikin dukkan man fetur da kasashen Afrika suka fitar, kuma yawan jarin da Sin take zubawa kan sha'anin man fetur da iskar gas ya kai kimanin kashi 1 cikin kashi 16 a cikin dukkan jarin da aka zuba a kasashen Afrika.

Ina dalilin da ya sa ake zargin kasar Sin kawai, ko wannan ra'ayin kasashen Afrika ne ko kuma ra'ayin kasashen yammancin duniya ne?

Firaministan Wen ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba da gudummawa ga kasashen Afrika ba tare da gindaya sharuddan siyasa ba, kuma Sin ba ta kutsa kai cikin harkokin gida na kasashen Afrika ba, kuma kasar Sin tana ganin cewa, makomar ko wace kasa na dogara ga al'ummar kasar. Mr. Wen ya bayyana cewa,"Yayin da mutane da dama ke ba da shawarwari ga kasashen Afrika wajen samun bunkasuwa, sun gabatar da tafarkin Washington ko kuma tafarkin Beijing, a ganina, dole ne kasashen Afrika su bi hanyoyin samun bunkasuwa na kansu da suka dace da halin da kasashensu ke ciki, wadannan hanyoyi, hanyoyin samun bunkasuwa ne na kasashen Afrika.

A sa'i daya kuma, Firaminista Wen ya yi kira ga kasashen duniya da su kara hadin gwiwa tsakaninsu, domin sa kaimi ga shirin samun bunkasuwa da aka tsara a shekarar 2000.(Bako)