|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-09 15:47:19
|
|
Firayin ministan kasar Sin ya gabatar da sabbin matakai game da hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika a gun taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin bangarorin biyu
cri
A ranar 8 ga wata a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, an yi taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. A yayin bikin bude taron, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya gabatar da sabbin matakai guda takwas na inganta hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika, ciki har da yunkurin kafa dangantakar abokantaka don fuskantar sauyin yanayi tsakanin Sin da kasashen Afrika, da ci gaba da yafe basussukan dake kan wasu kasashen Afrika, da kuma shirin rage harajin kwastan na kayayyakin da kasashen Afrika suke fitarwa, da dai sauransu.
Yanzu, an samu shekaru 9 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. Taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar da aka yi a birnin Sharm El Sheikh ya jawo hankalin shugabannin kasashen Afrika sosai. Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao, da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak, da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU Jean Ping, da kuma shugabanni daga kasashen Afrika fiye da goma sun halarci bikin bude taron.
A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya yi bayyani kan muhimman abubuwan dake tattare da taron, inda ya ce,
'Yau muna yin taro a birnin Sharm El Sheikh, kamata ya yi mu yi amfani da wannan dama mai kyau don nanata babbar manufa game da hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika, a waje guda kuma, za mu dudduba sakamakon da muka samu bayan taron koli na Beijing. A shekaru uku da suka wuce, mun samu nasarori da yawa, ana iya kimanta cewa, nan gaba kasar Sin za ta kara zuba jari a kasashen Afrika, kuma za a kara samun hadin kai tsakanin bangarorin biyu.'
A gun wannan taron ministoci, abin da ya fi jawo hankali shi ne, irin sabbin matakan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar don inganta hadin kai tsakaninta da kasashen Afrika. A yayin bikin bude taron, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya sanar da sabbin matakai guda takwas a fannonin tattalin arziki da ciniki, da ayyukan gona, da kimiyya da fahasa, da ba da ilmi, da likitanci da kiwon lafiya, da dai sauransu.
Ko da yake kasar Sin na fuskantar kalubale ta fuskar bunkasuwar tattalin arziki sakamakon matsalar kudi da ake ci a yanzu, amma ta tsaida kudurin ci gaba da yafe basussukan dake kan kasashen Afrika, kazalika kuma, za ta kara rage harajin kwastan kan irin kayayyakin da kasashen Afrika ke fitarwa. Mr. Wen Jiabao ya bayyana a gun taron cewa,
'Za mu taimakawa kasashen Afrika ta fuskar kara musu karfi na tattara kudi. Za mu ba da rancen kudi mai sauki na dalar Amurka biliyan 10 ga kasashenAfrika. Ga irin kasashen Afrika da suka karbi basussuka da yawa, da wadanda suke mafiya talauci, wadanda suka kulla huldar diplomasiya da kasar Sin, gwamnatin kasar Sin za ta rage basussuka game da samun rancen kudi maras ruwa da kamata ya yi gwamnatocin kasashen su biya sabo da wa'adinsu ya cika a karshen shekara ta 2009.'
A waje guda kuma, Mr. Wen Jiabao ya ba da shawarar kafa dagantakar abokantaka don fuskantar sauyin yanayi tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Bayan haka kuma, Mr. Wen Jiabao ya yi kira ga kasashen duniya da su nuna hakikanin goyon baya ga samun bunkasuwar kasashen Afrika. Ya jaddada da cewa, kasar Sin na bayar da taimako ga kasashen Afrika ba tare da saka sharudan siyasa ba.
'Ko da yaushe gwamnati da jama'ar kasar Sin na nuna girmamawa ga ikon kasashen Afrika wajen zaben tsarin mulkinsu na kansu. Sun yi imani cewa, kasashen Afrika nada karfin iya warware matsalolin da suke fuskanta da kansu.'(Bilkisu)
|
|
|