A ran 8 ga wata, a birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar, an bude taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.
Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao da shugaban kasar Masar Hosny Moubarak da shugabannin sauran kasashen Afirka da kuma Jean Ping, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka sun halarci bikin bude taron. Jami'ai kusan 100 na matakin ministoci masu kula da harkokin diplomasiyya da cinikayya da masana'antu da bunkasuwar tattalin arziki daga kasar Sin da kuma kasashen Afirka 49 sun halarci taron. Firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya yi jawabi a gun bikin domin ci gaba da gabatar da sabbin matakai 8 wajen hadin kan Sin da Afirka.
An mayar da "inganta dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare domin neman samun dauwamammen ci gaba" a matsayin babban taken taron. Kuma muhimmin aiki na taron shi ne kimantawa matakan da aka dauka bayan taron koli na Beijing, da kuma tsara shirin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a cikin shekaru uku masu zuwa.(Kande Gao)
|