Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 21:34:43    
Mahmoud Abbas ya sanar a hukunce cewa ba zai nemi yin tazarce ba

cri
A ran 5 ga wata, shugaban hukumar ikon al'ummar kasar Palestinu Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, ba zai shiga zaben shugaban hukumar ikon al'umma da na kwamitin tsara dokoki na kasar Palestinu ba, wadanda za a yi watan Janairu na badi. Kuma ya jaddada cewa, ba za a canza lokacin babban zaben ba na ranar 24 ga watan Janairu na shekarar 2010.

A wannan rana a birnin Ramallah, Mahmoud Abbas ya ba da jawabi ta telibijin cewa, ya riga ya sanar da kungiyar PLO da kwamitin tsakiya na kungiyar Fatah da cewa, ba zai zama dan takarar neman ci gaba da zama shugaban hukumar ikon al'ummar Palestinu ba.

A cikin jawabinsa kuma, ya nanata cewa, kamata ya yi a sarrafa rikicin dake tsakanin Palestinu da Isra'illa bisa kuduri da shirin taswira na MDD da kuma shawarar shimfida zaman lafiya da kasashen Larabawa suka bayar. Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, gwamnatin Isra'illa ta yi biris da bukatun neman zaman lafiya, tana ci gaba da kafa matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordon da kudus ta gabas, wanda ya kawo babban cikas ga shawariwari tsakanin Palestinu da Isra'illa.

Bayan jawabinsa, kwamitin tsakiya na kungiyar Fatah ya fito da sanarwa nan take, inda ya nanata matsayin Mahmoud Abbas na dan takara daya tak na kungiyar Fatah a babban zaben da za a yi a shekarar 2010.(Fatima)