Suna na Su Jianhua na kasar Sin shi ne Sayed- el-tilib, yana son al'adun kasar Sin tuna yana karamin yaro. A cikin shekaru da dama da yake karatu a kasar Sin, ya sami abokai da yawa na kasar Sin, kuma ya fahimtar cewa, ya kamata kasashen Afirka su kara yin hadin gwiwa da kasar Sin. Bayan ya gama karatu daga jami'a, a shekarar 1980 ya kafa wani kwamitin sa kaimi ga cinikin da ke tsakanin kasar Sin, da kasashen Larabawa, da kasashen Afirka, ya zama babban sakatare na wannan kwamiti. Yana son wannan kwamiti zai hada kwararren masanin ilmin kimiyya da fasahohi masu inganci na kasar Sin da albarkatun kasashen Afirka tare, da kuma jawo jari daga kasashen Larabawa.
Tun daga shekaru 80 na karni na 20, Su Jianhua ya sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kamfannonin kasar Sin da kasashen Afirka. Ya ce, "Tun shekarar 1984, a ko wace shekara, muna jawo kamfanonin kasar Sin da su shiga bikin nune-nunen kayayyakin duniya da aka yi a Hartoum na kasar Sudan, kuma muna hada kai da kamfanonin kasar Sin domin shigar da kayayyakin kasar Sin cikin bakukuwan nune-nunen kayayyaki a yankin gabas ta tsakiya a kasashen Afirka. Mun ci nasarori a kasashen Sudan, da Dubai, da Saudi Arabiya. Yanzu muna shirya kafa unguwar kasar Sin a kasar Sudan da wasu kasashe na yammacin Afirka domin bunkasa ciniki da ke tsakaninsu."
Ban da haka kuma, Su Jianhua yana kokarin sa kaimi ga musayar al'adu da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Ya ce, "Muna kokarin sa kaimi ga dalibai mafi yawa da su je kasar Sin karatu, tare da jawo daliban kasar Sin da su je Afirka karatu. Muna yin kokari sosai, misalin yanzu an kafa kos na Sinanci a jami'ar Hartoum. Kuma mun yi kira ga daliban kasashen Afirka da su zabi kasar Sin domin yin karatu. Yanzu, mun riga mun sami dalibai kimanin 100 zuwa kasar Sin koyon Sinanci, ko karatu ilmin likita na gargajiya na kasar Sin, da ilmin likita na zamani, da ilmin comtuer, da saurau fannoni"
1 2 3
|