Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 21:20:37    
An yi bikin gabatar da hotuna wadanda suka bayyana ci gaban da aka samu a aikin gaba dangane da taron koli na Beijing na dandalin hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika

cri

A ran 4 ga wata a ofishin jakadancin Sin dake birnin Lome a kasar Togo, an yi bikin gabatar da hotuna wadanda suka bayyana ci gaban da aka samu a aikin gaba dangane da taron koli na Beijing na dandalin hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika.

An yi wannan biki a shekaru 3 da suka wuce bayan da aka kammala taron koli na Beijing na dandalin hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. Bikin ya gabatar da hotuna har 80 wadanda suke bayyana ci gaban da aka samu ta fuskar aikin gaba dangane da taron kolin, musamman ma ci gaban da Sin da Togo suka samu a fannoni daban-daban saboda hada kai da suka yi, wadanda suke hada da ayyukan kafa cibiyar ba da abin koyi a fannin fasahar sha'anin noma, da kaddamar da ayyukan cibiyar yaki da cutar annoba da kammala aikin gina asibitin Lome, da kuma ayyukan da masu sa kai na kasar Sin suka yi a hukumomi daban-daban na Togo da dai sauransu.

Jakadan Sin dake Togo Yang Min ya yi jawabi a bikin budewa cewa, a cikin shekaru 3 da suka wuce, gwamnatin Sin ta tabbatar da matakai 8 da ta gabatar a taron kolin ta yadda za a kara kaimi ga karfafa dangantakar tattalin arziki da ciniki dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.(Amina)