Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 21:00:13    
Za a gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Bayan gudanar da taron koli na birnin Beijing, shugabannin Sin da Afirka su kan kai wa juna ziyara. A cikin shekaru 3 da suka gabata, shugabannin Sin sun kai ziyara a kasashen Afirka har sau 9. A sa'i daya, bangarorin biyu sun ba da muhimmanci sosai kan tabbatar da sakamakon taron, a yunkurin ci gaba da sa kaimi ga hadin gwiwar sada zumunta tsakanin Sin da kasashen Afirka bisa dandalin tattaunawar.

A gun taron koli na birnin Beijing, a madadin gwamnatin kasar Sin shugaba Hu Jintao ya sanar da matakan hada gwiwa 8 tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bisa kokarin bangarorin biyu, yanzu an yi kusan tabbatar da daukacin matakan.

Ko da yake kasar Sin ta yi nisa da nahiyar Afirka, amma dangantakar abokantaka tsakanin jama'arsu tana kasancewa cikin dogon lokaci. Ba shakka, taron ministoci a karo na 4 da za a yi na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka zai karfafa hadin gwiwa da zumunta dake tsakaninsu yadda ya kamata.(Fatima)


1 2 3