|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2009-11-04 22:15:44
|
WHO ta jaddada cewa, yin allurar rigakafi wata hanya ce da ta fi kyau wajen rigakafin cutar A(H1N1)
cri
A ranar 3 ga wata, kungiyar WHO ta sake nanata cewa, yin allurar rigakafi wata hanya ce da ta fi kyau wajen rigakafin cutar A(H1N1), musamman ma ga mata masu juna biyu, da yara, da mutanen da suke kamu da cutar da ta dade a jikinsu, da dai sauransu.
Kakakin kungiyar WHO Gregorie Hartle ya bayyana a wannan rana dacewa, kungiyar WHO ta nuna damuwa sosai ga yanayin da ake ciki na wasu mutane wadanda suke iya yin allurar rigakafin, da wadanda ke bukatar yin allura amma ba su amince da allular ba. Mr. Hartel ta ce, illar da a kan samu wajen yin allurar rigakafin ba ta da tsanani, kuma a cikin gajeren lokaci. Ya zuwa yanzu, ba a samu illa mai tsakani da aka yi hasashe ba. (Bilkisu)
|
|
|