Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 22:05:57    
Yankin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Zambia yana da kyakkyawar makoma a cewar ministan kasuwanci na kasar Zambia

cri

Bayan taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kasar Sin ta fara gina yankin yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki na farko a Afirka, wato yankin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Zambia wanda ya zama yankin tattalin arzikin da ke da amfani da dama na farko na kasar Zambia. A kwanakin baya, Mr. Felix Mutati ministan kasuwanci, da ciniki da masana'antu na kasar Zambia ya gana da manema labaru na dilancin watsa labaru na Xinhua, inda ya ce, yanzu ana ginawa wannan yanki bisa shiri yadda ya kamata, mutanen kasar Zambia suna nunawa kyakkyawar fata ga makomar wannan yanki.

Mr. Mutati ya ce, ko da yake wannan yankin raya tattalin arziki wani sabon abu ga kasar Zambia, amma ya gaskata cewa, ilmin da kasar Sin ta samu daga wajen gina yankin raya tattalin arziki zai ci nasara a kasar Zambia, kuma wannan yanki zai zama wani al'amari mai muhimmiyar ma'anar tarihi na amincewar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kasar Sin ta gina wannan yankin raya tattalin arziki domin shimfida alkawarin da ta yi cikin taron koli na Beijing, wato "kafa yankunan raya tattalin arziki guda 3 zuwa 5 a kasashen Afirka". A watan Fabrairu na shekarar 2007, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da tsohon shugaba Mwanawasa na kasar Zambia sun aza tubali na wannan yanki da kansu.

1 2 3