Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:22:22    
Sin ta horar da gwanaye ga kasashe 5 na Afirka wajen yin nazari kan tsire-tsire domin yin amfani da su a magungunan gargajiya

cri
A ran 2 ga wata a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, an kaddamar da kwas a matsayin koli na yin nazari da raya tsire-tsire a fannin magungunan gargajiya na Afirka da ma'aikatar ilmi ta Sin ta dau babban nauyin shirya kuma jami'ar likitanci da magunguna irin na gargajiya ta Tianjin ta Sin ta ba da taimakon shiryawa. Masana sama da 20 daga kasashe 5 na Afirka sun shiga kwas din.

Mataimakiyar shugaba ta jami'ar likita da magunguna irin na gargajiya ta Tianjin ta Sin Gao Xiumei ta bayyana cewa, makasudin gudanar da kwas din shi ne kara karfafa zumunta da hadin gwiwa iri na gargajiya tsakanin kasashe masu tasowa, da sa kaimi ga bunkasuwar aikin likita da magunguna iri na gargajiya a kasashe masu tasowa da nazari kan tsire-tsire a fannin magungunan gargajiya ta hanyar musanyar halin da ake ciki a Sin da hanyoyi da fasahohi na kasar a fannin sarrafawa da kuma yin nazari kan wadannan fannoni, a yunkurin kara ba da taimako ga sha'anin kiwon lafiya na bil'adam.

Gao Xiumei ta bayyana cewa, tun bayan shekarar 2001 zuwa yanzu, jami'ar ta riga ta jagoranci irin wannan kwas har sau 6. Kawo yanzu dai, mutane sama da 120 daga kasashe masu tasowa 23 sun shiga wannan kwas.(Fatima)