Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:20:06    
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya aika da sakon taya murna ga Hamid Karzai da ya sake zama shugaban kasar Afghanistan

cri

A ran 3 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya aika da sakon taya murna ga Hamid Karzai da ya sake zama shugaban kasar Afghanistan.

Sakon ya ce, a 'yan shekarun baya, bisa kokarin da bangarorin Sin da Afghanistan suka yi cikin hadin gwiwa, sun kafa dangantakar hadin kai a fannoni daban daban, da kuma sa kaimi ga samun bunkasuwar dangantakar a tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. Ko da yaushe gwamnatin kasar Sin taya tsayawa kan 'yancin kai da mulkin kan kasa da kokarin samun cikakken yankin kasa a kasar Afghanistan. Gwamnatin kasar Sin ta nuna goyon bayan ga tsarin zaman al'umma da hanyoyin da jama'ar kasar Afghanistan suke bi wajen samun bunkasuwa, da kuma kokarin da suke yi wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a kasar.

Sakon ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta yi imani cewa, bisa jagorancin Mr. Karzai, gwamnatin kasar Afghanistan da jama'arta za su samu sababbin nasarori a yunkurin sake gina kasa cikin lumana, da kuma ba da taimako ga aikin samun zaman lafiya da zaman karko, da bunkasuwa a shiyyarsu.(Danladi)