Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 21:36:54    
Dan takarar shugaban kasar Afghanistan Abdullah Abdullah ya janye jiki daga zagaye na biyu na babban zabe

cri

A ran 1 ga wata, Abdullah Abdullah, dan takarar shugaban kasar Afghanistan kuma tsohon ministan harkokin waje na kasar ya sanar da cewa, ya nuna fargabar cewa ba za a kwatanta adalci a cikin babban zaben ba, don haka ya tsai da kudurin janye jiki daga zagaye na biyu na zaben bayan da ya saurari ra'ayin jama'a. Wannan kuduri kuma ya sa Hamid Karzai, shugaban kasar na yanzu ya zama dan takara kacal a zagaye na biyu na zaben.

A ran nan, Mr. Abdullah ya bayyana a birnin Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, cewar an kasance da batun magudi a cikin zagaye na farko na babban zaben sakamakon sa hannu a ciki da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar ya yi, don haka ya gabatar da bukatu don tabbatar da samun adalci a cikin zagaye na biyu na zaben, amma an ki amincewa da bakatunsa. Sabo da haka, ba zai yiwu ba a gudanar da zaben a fili cikin adalci, kuma ba zai shiga zaben da za a yi a ran 7 ga wata ba. Haka kuma Mr. Abdullah ya ce, bai kamata ba 'yan kasar Afghanistan su amince da sakamakon zaben da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar ya bayar.

1 2 3