Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 21:40:21    
Iran ta mai da martani ga shirin yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya

cri

A ran 29 ga wata, kasar Iran ta mika wata takarda ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA domin mai da martini ga shirin yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya, amma ba a bayyana hakikanin abubuwan da aka rubuta cikin takarda ba. Babban jami'in hukumar IAEA Mohamed el Baradei ya ce, za a ci gaba da yin shawarwari tsakanin sassan da abin ya shafa kan tsarin yin gyare-gyaren makamashin nukiliya na kasar Iran da ake yi a kasashen waje, ana fatan za a cimma daidaito kan wannan matsala.

Bisa labarin da tashar Press TV ta kasar Iran ta bayar an ce, Ali Asghar Soltanieh, wakilin hukumar IAEA dake kasar ya bayyana cewa, Iran za ta nuna himma da kwazo wajen yin shawarwari a tsakaninta da sassan da abin ya shafa kan matsalar samar da makamashin nukiliya, amma labarin bai bayyana hakikanin abubuwan da aka rubuta a cikin takardar ba.

Bisa shirin yarjejeniyar da el Baradei ya bayar a wajen taron Viena da aka yi a makon jiya, an nemi Iran da ta yi jigilar sinadarin Uranium masu nauyin kilo 1,100 zuwa kasar Rasha kafin karshen wannan shekara don yi musu gyare-gyare, daga baya kuma za a jida zuwa kasar Faransa domin ci gaba da yin gyare-gyare. Yanzu kasashe 3 wato Amurka da Rasha da Faransa sun riga sun nuna goyon bayansu ga wannan shiri.

Kwanan baya, kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya yi taron tsokaci shirin yarjejeniyar da el Baradei ya gabatar. A wajen taron an tantance cewa idan an amince da shirin yarjejeniyar, za a iya samun abubuwa masu amfani da marasa amfani, wato da farko za a iya daidaita matsalar samar da abubuwan Konawa domin na'urar sarrafa makamashin nukiliya domin amfanin fararen hula na birnin Tehran. Na 2, za a iya sassauta takunkumin da ake kakaba wa Iran a yanzu, bugu da kari kuma za iya gaskantar da aikin tace sinadarin Uranium da Iran ke yi ta fuskar doka. Na 3, Bisa shirin yarjejeniyar an ce, Iran ta ba wa Rasha ikon kama gaba wajen samar mata da makamashin nukiliya, hakan yana da amfani ga daidaita matsalar samar da makamashin ga tashar ba da wutar lantarki da karfin nukiliya ta Bushire.

Kudurin da gwamnatin Iran ta tsayar kan matsalar makamashin nukiliya ya samu bambancin ra'ayoyi daga cikin kasar. A wurin taron kwamitin tsaron kasar Iran, da akwai wasu wakilai wadanda suka nuna damuwa ga kasashen yammacin duniya cewa, ko za su iya cika alkawarinsu na samar wa kasarsu da makamashin nukiliya, sabo da haka sun nemi da a gyara shirin yarjejeniyar Baradei sosai. Amma ran 29 ga wata, shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta hada gwiwa da kasashen yammacin duniya kan matsalar samar da makamashin nukiliya, kuma ya jaddada cewa Iran ba za ta yi rangwame ba a game da ikon mallakar makamashin nukiliya da ake so a haramta mata. Ya kuma sanar da cewa sakamakon da aka samu kwanan baya wajen shawarwarin da aka yi kan matsalar makamashin nukiliya ya zama babbar nasara ce ga kasar Iran a fannin harkokin waje.

Bisa labarin da kafofin yada labaru na kasar Iran suka bayar an ce, martanin da gwamnatin Iran ta mayar kan shirin yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya ya samu amincewa daga wajen shugaban koli na kasar Ayatollah Sayyed Ali Khamemei. Babban jami'in hukumar IAEA Mohamed el Baradei ya ce, za a ci gaba da yin shawarwari tsakanin sassan da abin ya shafa kan tsarin yin gyare-gyaren makamashin nukiliya na kasar Iran da ake yi a kasashen waje. (Umaru)