Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 18:43:04    
An samu sakamako mai kyau a yayin taro a karo na 20 na JCCT a tsakanin Sin da Amurka

cri
Ran 29 ga wata, a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, an yi taro a karo na 20 na JCCT a tsakanin kasar Sin da ta Amurka kan kasuwanci da ciniki.

A yayin bikin sa hannu na taron, bangarorin Sin da Amurka sun daddale "takardar bayani kan nufin sa kaimi ga zuba wa juna jari" da "shirin ayyuka na habaka yin hadin gwiwa a fannonin fasahar zamani da harkokin ciniki bisa manyan tsare-tsare" da sauran takardu 9 kan yin hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da ciniki. A yayin taron manema labaru da aka yi bayan rufe taron, Chen Deming, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, an cimma matsaya iri daya a fannoni da yawa a yayin taron. Inda ya ce,"Wang Qishan, mataimakin firayim ministan Sin da Gary Locke, ministan kasuwanci na Amurka da Ron Kirk, wakilin Amurka kan harkokin ciniki su ne suka shugabanci taron cikin hadin gwiwa. A sakamakon kokarin da bangarorin 2 suka yi, an samu cikakkiyar nasarar shirya taron, tare da samun ra'ayoyin bai daya sosai. An sami sakamako mai yakini."

Game da hakikanin sakamakon da aka samu a yayin taron, Mr. Chen ya bayyana cewa, Sin da Amurka dukkansu sun bayyana cewa, ya kamata a yi yaki da samar da kariya a harkokin ciniki da zuba jari tare, a bi ra'ayi daya da aka samu a yayin taron koli na G20. A ganinsu, kayyade sayen kayayyaki daga kasar Sin ba zai iya taimakawa Amurka ta rage gibin ciniki kan kasar Sin ba, sai dai Sin da Amurka suna kokarin raya ciniki a tsakaninsu cikin himma da zummar samun daidaito.

Dangane da batutuwan da kasar Sin ta jaddada da kuma mai da hankali a kai, kamar kin yarda da yin amfani da matakan ba da taimako ta fuskar ciniki fiye da kima, da sassauta irin kayyadewar da ke kan sayar da kaya zuwa Sin, da amincewa da matsayin Sin na tattalin arziki na kasuwanni, Mr. Chen ya ce, Amurka ta mayar da martani mai kyau kansu. Yana mai cewa,"Amurka na cewa, za ta inganta tuntuba da yin tattaunawa da Sin domin magance yin amfani da matakan ba da taimako ta fuskar ciniki fiye da kima. Sa'an nan kuma, Amurka za ta hada kai da Sin domin daidaita kulawar da Sin ke nunawa, a yayin da take yin gyare-gyare kan tsarin kayyade aikin fitar da kayayyaki. Haka kuma, Amurka ta amince da ci gaban da Sin take ta samu a fannin yin gyare-gyare kan kasuwanni, za ta yi taron kungiyoyin ayyuka kan matsayin tattalin arziki na kasuwanni cikin sauri, inda za a tattauna batun amincewa da matsayin Sin na tattalin arziki na kasuwanni."

Bana shekara ce ta cika shekaru 30 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka. A yayin bikin bude taron da aka yi a ran 29 ga wata da safe, Wang Qishan, mataimakin firayim ministan kasar Sin ya nuna cewa, yanzu Sin da Amurka suna kasancewa cikin sabon mafari a tarihi. Ya kamata taron JCCT a tsakanin Sin da Amurka ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa. Inda ya ce,"Shugaba Hu Jintao da Mr. Obama sun tabbatar da kafa kyakkyawar dangantakar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka a dukkan fannoni a karni na 21. Sun tabbatar da babbar manufa ta nan gaba da za a yi amfani da ita. Ya kamata taron JCCT ya ci gaba da taka rawa a wasu mabambantan fannonin."

Kazalika kuma, a yayin bikin bude taron, Gary Locke, ministan kasuwanci na Amurka ya darajta tsarin taron JCCT sosai, inda ya ce,"Taron JCCT a tsakanin Sin da Amurka kan samar da damar daidaita matsalolin da suke caza kan mutane sosai. Gwamnatin Amurka na son warware batutuwan da Sin ta gabatar, bisa ra'ayin yin hadin gwiwa. Saboda bangarorin 2 za su iya daidaita dukkan kalubalolin da suke fuskanta tare bisa nufin girmama juna da yin hadin gwiwa ba tare da boye kome ba."(Tasallah)