Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-30 15:52:13    
Gwamnatocin Sin da Mozambique za su ci gaba da yin kokari cikin hadin gwiwa, domin samar wa jama'a alheri

cri

A ran 28 ga wata, an kawo karshen babban zabe a kasar Mozambique da ke kudancin Afirka. A yayin da jakadan kasar Sin da ke kasar Mozambique Mr. Tian Guangfeng yake hira da wakilan gidan rediyon kasar Sin, ya bayyana cewa, tun lokacin da kasashen biyu suka kafa dangantakar diplomasiyya a shekarar 1975, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu na samun bunkasuwa a cikin sauri, bangarorin biyu sun kara amincewa da juna, da kuma taimakawa juna a harkokin duniya.

Game da babban zaben da aka kammala a kasar Mozambique, Mr. Tian ya ce,

'Mai yiyuwa ne sabuwar gwamnati ta mai da hankali a game da samun zaman karko da bunkasuwa, haka kuma za ta ci gaba da tafiyar da manufar samun abokai ba tare da samun abokan gaba' a fannin diplomasiyya ba. Ban da wannan kuma sabuwar gwamnatin Mozambique za ta bukaci taka wata muhimmiyar rawa a harkokin shiyyarta.

A tsakiyar karnin da ya gabata, gwamnatin sabuwar kasar Sin ta taimakawa jama'ar kasar Mozambique wajen samun 'yancin kai daga mulkin mallaka. Taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka, wanda aka shirya a shekarar 2006 ya raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka a wani sabon matsayi. Ya zuwa yanzu, shekaru uku da suka wuce, a matsyinta abokiya ga kasar Sin, Mozambique ta fahimci canje-canje da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka, yayin da gwamnatin kasar Sin take daukar matakai 8 wajen taimakawa kasashen Afirka. Mr. Tian ya ce,

'Hakikanan dalilan da ya sa shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya sanar da wadannan matakai 8 su ne, domin sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, da kara kwarewar kasashen Afirka domin su sami bunkasuwa da kansu, da taimakawa kasashen Afirka wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, da cimma burin samun ci gaba tare da cin moriyar juna da samun nasara tare. A halin yanzu, bangarorin biyu na Sin da Mozambique suna aiwatar da matakai 8 lami lafiya.'

A ran 8 ga watan Nuwamba, za a shirya taron ministoci karo na hudu a dandalin tattaunawa da hadin kai da ke tsakanin Sin da Afirka a birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar. Mr. Tian ya gaya mana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta sanar da wasu sababbin ayyuka ga kasashen Afirka a gun wannan taro. Ya ce,

'Dandalin tattaunawar da ke tsakanin Sin da Afirka ya zama wani abun misali ga kasashe masu tasowa da su kara hada kansu, haka kuma zai taimaka wajen kara matsayin kasashe masu tasowa da kuma karfafa tasiri da suke baiwa kasashen duniya. A ganina, gwamnatin kasar Sin za ta mai da hankali kan samun bunkasuwar dangantakar da ke tsakannin Sin da Afirka da kuma hadin kansu irin na cin moriyar juna a nan gaba. Sakamakon haka, gwamnatin kasar Sin za ta sanar da wasu sababbin matakai da za ta dauka domin kara hadin kai da ke tsakanin bangarorin biyu, haka kuma za ta dauki wadannan matakai ne tare da yin la'akari domin tinkarar rikicin kudi na duniya da cimma burin samun bunkasuwa na shekarar dubu biyu na MDD cikin hadin gwiwar Sin da Afirka.'(Danladi)