Kasar Sin da kasashen Afrika suna da zumanci na dogon lokaci, kuma ana ta kokarin bunkasa zumancin dake tsakaninsu har wa yau. Sin da kasashen Afrika kuma su kan fuskanci yanayi iri daya a tarihi, a cikin gwagwarmayar da suka yi domin neman samun yancin kai, bangarorin biyu su kan nuna wa juna juyayi da goyon baya, hakan ya sa sun kulla dangantakar sada zumanci mai kyau. A cikin rabin karnin da ya wuce, bangarorin biyu sun kara yin mu'amala ta fuskar siyasa da kai wa juna ziyara, ban da wannan kuma, sun yi kokarin bunkasa dangatakar cinikayya a tsakaninsu, da kuma hada kai a fannoni daban-daban, dadin dadawa, sun kara yin shawarwari da tattaunawa a cikin harkokin kasa da kasa. Kasar Sin ta ba da tallafi ga kasashen Afrika bisa gwargwadon karfinta, kuma kasashen Afrika su ma su kan nuna goyon baya mai karfi ga Sin.
A ran 12 ga watan Jarairu na shekarar 2006, gwamnatin Sin ta gabatar da takardar matakan da Sin ta dauka kan kasashen Afrika domin kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu, a cikin takardar kasar Sin ta yi kira da a kafa da raya sabuwar dangantakar sada zumanci bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu wadda ta bukaci bangarorin biyu su amince da juna a fannin siyasa, da yunkurin kawo moriyar juna a fannin tattalin arziki da kuma yin koyi da juna a fannin al'adu, bugu da kari, kasashen Afrika sun nuna maraba ga wannan takarda. Wannan shi ne karo na farko da gwamnatin Sin ta gabatar da takardar manufofin da Sin ta dauka kan kasashen Afrika da zummar sanar da burin daukar wadannan manufofi da matakan da za ta dauka, da kuma tsai da kudurin yadda za a hada kai a fannoni daban-daban nan gaba, gami da kara kaimi ga bunkasuwar dangantakar a tsakanin bangarorin biyu wadda take mai dorewa da kara hada kai domin kawo moriyar juna.
Takardar ta kunshi kalamomi kimanin 5,000, ban da farkon bayani, takardar ta kasu kashi 6 wato "Matsayi da amfanin kasashen Afrika" da "dangantakar Sin da kasashen Afrika" da "manufofin da Sin ta dauka kan kasashen Afrika" da "kara hada kai tsakanin Sin da kasashen Afrika a duk fannoni" da "dandalin hada kai na Sin da kasashen Afrika da ayyukan gabansa" da "dangantakar dake tsakanin Sin da hukumomin yankunan nahiyar Afrika".
Takardar ta nuna cewa, kara hada kai da kasashen Afrika muhimmin bangare ne na manufar diplomasiyya ta zaman lafiya cikin yanci da Sin ta dauka. Babban burin manufofin da Sin ta dauka kan kasashen Afrika su ne, girmama juna da kawo moriyar juna da taimakawa juna da kuma koyi da juna da samun bunkasuwa tare. Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar kara bunkasa dangantaka ta sada zumanci a tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma Sin ta kafa sabuwar dangantaka ta sada zumanci bisa manyan tsare-tsare bisa kokarin samar da moriyar jama'ar bangarorin biyu wadda ta bukaci bangarorin biyu su amince da juna ta fuskar siyasa da samu moriyar juna a fannin tattalin arziki da kuma yin koyi da juna ta fuskar al'adu.(amina)
|